lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul Karij-bahasi cikin wadatarwar tasbihatus Sugra kafa daya cikin halin larura

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi (h)

Lokaci: 8-9 na safiya

Fikhu (35) 16 ga watan Rabi'u Awwal shekara 1442 hijiri.

Maganarmu zata kasance cigaba kan abinda ya gabata cikin wadatarwar kafa guda daga tasbihatus sugra cikin halin larura da kuntatar lokaci, sabida haka karanta (subhnallahi) kafa guda yana isar masa da wadatar da shi kuma wannan shine abinda Mashur daga Malamai suka tafi akai, da farko dai an kafa dalili da ijma'I, sai dia cewa ijma'I ne madraki, sannan na biyu an kafa dalili da Sahihatu Mu'awiyatu Ibn Ammar da Mursalatu Saduk kamar yanda bayani ya gabata.

Amma mursalatu Saduk hakika ishkali ya gangara a kanta sakamakon raunin isnadi ta hanyar irsali, kuma bata samu kwaskwarima da Amalul Ashab sabida haka ba za a iya kafa dalili da ita ba.

Amma Sahihatu Mu'awiyatu ita babu wani ishkali kan ingancin isnadinta amma ta bangaren Dalala lallai duk da kasantuwar abinda aka ambata cikinta shine:

 (قلت له أدنى  ما يجزى  الله يعني من التسبيح في الركوع والسجود؟ قال: تسبيحة واحدة)

Na ce masa da menene yake isarwa wurin Allah daga tasbihi cikin ruku'u? yace tasbihi kafa daya.

Sabida haka wannan riwaya bata da dalala kan cewa muradi daga gareta shine tasbihtasu sugra, sai dia cewa idan an gwamata da abinda Mu'awiya da kansa ya rawaito daga Abu Abdullahi amincin Allah ya tabbata a gareshi

قال: قلت: أخف ما يكون من الحديث: 2) التسبيح في الصلاة؟ قال: ثلاث تسبيحات مرسّلاً، تقول: سبحان الله سبحان الله سبحان الله (الوسائل: باب 5 من أبواب الركوع)

Yace: nace mafi karanci abinda yake kasancewa daga tasbihi cikin sallah? Sai yace: tasbihi uku kace subhanallahi subhanallahi subhanallahi.

Abinda aka fahimta daga wannan hadisi abin nufi daga tasbihi kafa guda a halin larura shine (subhanallahi) bayan tafiya kan hadewar maraiwaci da abinda ya rawaita cikinsa.

Idan kuma an zabi akasin wannan fahimta da sallamawa idlakin da ya zo cikin Sahihatu Mu'awiyatu ta farko to lallai zai zamana an yi ikirari da cin karon idalkinta da wani idalaki da ya zo cikin Sahihatu Zurara abinda ta shiryar daga lazimci kasantuwarshi kafa daya shine tasbihatul Kubra kuma ta zo saki babu kaidi zata hado da har mara lafiya dama waninsa.

عن زرارة قال: ما يجزى من الكون في الركوع والسجود؟ فقال عليه السلام: ثلاث تسبيحات في ترسّل وواحدة تامة تجزى  (الوسائل باب 4 من أبواب الركوع الحديث 2)

An karbo daga Zurara yace: mene yake isarwa cikin ruku'u da sujjada? Sai amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: tasbihi uku suna isarwa kayi daya cikakkiya.

Gini kan cewa abin nufi daga daya cikakkiya shine tasbihatul Kubra.

A wannan lokaci hakan na lazimta yin kaidi da dabaibayi daga daya daga cikin idlakan guda biyu da daya daga cikinsu bawai dabaibaye idlakin Sahihatu Zurara da idlakin cikin Sahihatu Mu'awiyatu  da cewa yana isarwa da yin tasbihtul kubra kafa daya sai dai idan mara lafiya, yafi dacewa daga dabaibayin Sahihatu Sahihatu Zurara da ta Mu'awiyatu da take cewa mara lafiya tasbihi kafa daya ya wadatar masa itace tasbihil kubra, sannan dangantaka tsakanin idlakokin biyu da riwayoyin biyu dangantaka ce tsakanin umumu da kususu min wajhin  bayan samun cin karo da juna tsakanin idlakan biyu da faduwarsu sai mu koma zuwa ga idlakin da ya shiryar kan rashin wadatarwa tasbihi kafa daya daga tasbihatus sugra babu banbanci mara lafiya ne ko waninsa.

Wasu ba'ari daga malaman wannan zamanin sun tafi kan cewa zahiri shine ayyanuwar na farko ma'ana dabaibaye idlakin sahihatu Zurara da sahihatu Mu'awiyatu ma'ana dabaibaye idlakin farko da idlaki na biyu sai ya zamana babu abin tsoro cikinsa, sabanin akasinsa lallai cikinsa akwai abin tsoro shine lazimta watsi da hususiyar magangarar da bata gushe ba daga munana domin idan mka dabaibaye sahihatu Mu'awiyatu da sahihatu Zurara da waninta muka dauki daya muka dora ciki kan tasbihi kubra zai zamana babu wani banbanci tsakanin mara lafiya da waninsa, abinda yafi dacewa cikin bada amsa shine ace shi mara lafiya da waninsa basu da banbanci cikin wannan sura, bawai Imam da yarda da tasbihi kafa day aba. Zahiri shine akwai banbanci tsakanin mara lafiya da waninsa, a wannan lokaci zai kasance daga dabaibayin da muka kafa hujja da shi shine watsi da unwanin rashin lafiya.

Wannan ya sabawa dabaibayin sahihatu Zurara da ta Mu'awiyatu  saboda haka baya lazimta abin gudu daga munana, bari dai iya abinda za a iya shine dora sahihatu Zurara da waninta kan wanda yake da lafiya kuma babu matserata daga kiyaye idlakin sahihatu Mu'awiyatu, natija daga wannan bayani zai zamana shi mara lafiya ya banbanta daga waninsa yana wadatuwa da kafa daya koda kuwa daga sugra ce, kan wannan zai zamana baya inganta kafa dalili da sahihatu Mu'awiya cikin fuskar farko ne daga abinda aka fahimta ko kuma ta biyu daga dabaibayin idlakokin

 


Tura tambaya