lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Hakuri kan mutuwa `da daga cikin Kur'ani mai girma

 

Allah madaukaki yan cewa:

(وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ بِشَيْءٍ مِنَ آلْخَوْفِ وَآلْجُوعِ وَنَقْصٍ مِنَ آلاَْمْوَالِ وَآلاَْنْفُسِ وَآلَّثمَرَاتِ وَبَشِّرِ آلصَّابِرِينَ * آلَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُمْ مُصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا للهِِ وإِنّا إِلَيهِ رَاجِعُونَ * أُولئِکَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِن رَبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ وَأُولئِکَ هُمُ آلْمُهْتَدُونَ )[1] .

Lallai zamu jarrabe su da wani abu daga tsoro da yunwa da tawayar kudi da `ya`ya da rayuka da kayan gona ka yi wa masu hakuri bushara* sune wadanda idan wata musiba da same su suke cewa lallai mu daga Allah muke kuma gareshi zamu koma* wadannan kansu akwai albarkoki daga ubangijinsu da rahama wadannan sune shiryayyu.

A wani wajen kuma yace:

 (إِنَّمَا يُوَفَّي آلصَّابِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ )[2] .            

Kadai da ana cikawa masu hakuri ladansu ba tareda lissafi ba.

Madaukakin sarki yace:

 (وَآسْتَعِينُوْا بِالصَّبْرِ وَآلصَّلوةِ إِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلاَّ عَلَى آلْخَاشِعِينَ )[3] .

Ku nemi taimako da hakuri da sallah lallai ita tana da girma face kan masu kushu'i.

Dukkanin wanda yayi hakuri kan rashin dansa ba nuna raki da karaji ba bai yakushi fuskarsa ba bai kekketa kayansa ba saboda zafin rashi bi dinga yin kuraji da kuka ba lallai Allah da sannu zai yi salati kansa ma'ana zai saukar masa da rahama kamar yanda yake salati ga annabinsa (s.a.w) , sai ya shiryar da shi madaidaiciyar hanya ya dora shi kan hanya har zuwa aljanna, ya cika masa ladansa ba tareda lissafi ba, babu mai yin hakuri face wanda ya kasance mai kushu'I, shi kushi'I na kasantuwa ne ga wand aya kasance malami.

 (إِنَّمَا يَخْشَى آللهَ مِنْ عِبَادِهِ آلْعُلَمَاءُ)[4]

Kadai babu masu tsaoran Allah daga bayinsa sai malamai.

 wanda ya kasance malami daga maza ne ko mata zai saukaka gareshi hakuri da sallah, zai nemi taimakon Allah da su biyun kan dukkanin musibu da wahalhalu da suke gudana cikin rayuwarsa ta duniya, lallai ita duniya gidane na bala'i d ayake kewaye da ababen ki, babu hutu cikin duniya face ga wanda ya gujeta yayi hakuri kan dadinta da dacinta, sannan ya mika lamarinsa zuwa ga Allah, sai ka samu ya juyawa da ni'ima da falala da babu wani abun ki da ya shafesu, lamarin mumini yana da ban mamaki babu abinda ke samunsa sai alheri, idan abin farinciki ya same shi sai ya godewa Allah, ita ko godiya rabin imani ce, sai ya kasance tsakankanin godiya kan ni'ima da hakuri kanh musiba sai ka samu ya tattaro dukkanin imani, idan Allah ya azurta shi da samun `da sai ya gode masa, idan ya jarrabce shi da mutuwarsa sai yayi hakuri, amma wanda yake nuna Gadara da jin kai lokacin da ya ni'imtu, yake kuma raki da babatu da gigita lokacin da yake cikin musiba, lallai an cire masa ruhin imani, kwata-kwata imani ba shiga zuciyarsa ba, kadai ya kasance cikin musulmai lokacin ya fadi Kalmar shahada, ina muslunci ina imani?!    

يجري القضاء وفيه الخير نافلةً         لمؤمن واثق بالله لا لاهي

إن جاءه فرج أو نابه ترحٌ         في الحالتين يقول الحمد للهِ

Hukuncin Allah yana gudana sannan cikin akwai alheri kari* ga mumini wanda yake da yakini kan Allah ba mai yin wargi da wasa.

Idan yayewa ta zo ko wata musiba ta afka masa cikin dukkanin halaye biyu sai ka same shi ya godiya ga Allah.

Ayuba ya kasance duk sanda musiba ta same shi sai yace:

«أللّهمّ أنت أخذت وأنت أعطيت ، مهما تبقى نفسي ، أحمدک على حسن بلائک ، فمن يتصبّر يصبّره الله، وما اُعطي أحدٌ عطاءً خيراً وأوسع من الصبر».

Ya Allah kai ne ka karba kuma kai ne dama ka bayar, duk yanda raina ta kai ga wanzuwa, ina gode maka bisa kyawun jarrabawarka, duk wanda ya lazimci hakuri Allah zai hakurantar da shi, wani mutum bai samu wata kyauta ba mafi alheri daga hakuri.

Sannan matsarkakin sarki yana cewa:

(خَلَقَ آلْمَوْتَ وَآلْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً)[5]

Shi ne wanda ya halicci rayuwa da mutuwa domin ya jarrabaku ya ga wanene cikinku yafi kyawunta aiki.

Daga cikin falsafar rayuwar dabi'a cikin duniya shi ne cewa an halicci duniya tareda ita akwai mutuwa da rayuwa domin jarrabawa, daga cikin kyakkywan ibtila'i domin wand ayafi kyawunta aiki ya bayyana cikin mukami ilimi da aiki, domin babu aiki face sai da ilimi hakama babu ilimi idan ba a aiki da shi, idan ko bah aka ba sai ta kasance kamar yanda sarkin muminai  (as) yace:

«قصم ظهري إثنان عالم متهتک ـ لا يعمل بعلمه ـ وجاهل متنسک ـ يعبد الله عن جهل ـ».

Mutane biyu sun karya gadon bayana-malami mai keta alfarma da baya yin aiki da iliminsa, da mai ibada jahili da yake bautar Allah ba tareda ilimi ba.

Sannan cikin littafinsa mai girma yace:

 (إِنَّا لاَ نُضِيعُ أَجْرَ مَنْ أَحْسَنَ عَمَلاً)[6]

Lallai mu bama tozarta ladan wand aya kyawunta aiki.

Sai ya saka masa da aljanna da yardarsa, sai dai cewa kuma yardar Allah ita tafi girma.

Tura tambaya