lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

DAGA ZANTUKAN IMAM MUHAMMAM BAKIR A.S

 

Imami na biyar Muhammad ibn Aliyu Ibn Husaini ibn Aliyu Ibn Abu Dalib mai tsaga ilimin Annabi (s.a.w)

Daga cikin zantukansa (as)

قال  7 :

«يا بني ، إنّ الله خبّأ أشياءً في ثلاثة أشياء: خبّأ رضاه في إطاعته فلا تحقرنّ من الطاعة شيئآ فلعلّ الله رضاه فيه ، وخبّأ سخطه في معصيته فلا تحقرنّ من المعصية شيئآ فلعلّ سخطه فيه ، وخبّأ أوليائه في خلقه فلا تحقرنّ أحدآ فلعلّ ذلک الوليّ».

Amincin Allah ya kara tabbata a gereshi yace: ya kai `dana hakika Allah ya boye abubuwa uku cikin abubuwa uku: ya boye yardarsa cikin biyayyarsa ka da ka sake ka wulakanta wani abu daga biyayyarsa ta yiwu yardarsa ta kasance cikinsa, ya boye fushinsa cikin sabonsa ka da ka sake ka raina wani abu daga saba masa ta yiwu fushinsa ya kasance cikinsa, ya boye waliyyansa cikin halittunsa ka da ka sake ka raina wani mutum ta yiwu ya kasance waliyyinsa.

«صانع المنافق بلسانک ، وأخلص وذلّ للمؤمنين ، وإن جالسک يهودي فأحسن مجالسته ».

Aminci Allah ya tabbata a gareshi yace: ka lallabi Munafuki da harshenka, sannan ka tsarkake niyya da tausasa ga Muminai, idan Bayahude ya zauna da kai ka kyawunta zama da shi

قال له بعض شيعته : أوصني ، وهو يريد سفرآ، فقال  7 :

«لا تسيرنّ شبرآ وأنت حافي ، ولا تنزلن عن دابّتک ليلا لقضاء حاجة إلّا 
ورجلک في خفّ ، ولا تبولنّ في نفق ، ولا تذوقنّ بقلة ولا تشمّها حتّى تعلم ما هي ، ولا تشرب من سقاء حتّى تعلم ما فيه ، واحذر من تعرف ، ولا تصحب من لا
 تعرف ».

Wasu ba’arin Shi’a sun ce masa: ka yi mini wasiyya ya fadi hakan ne sabida ya daura damarar safara, sai amincin Allah ya tabbbata a gareshi yace masa: ka da ka sake ka tattaka shibiri daya alhalin babu takalmi a kafarka, ka da ka sauka daga kan abin hawanka da daddare domin biyan bukata face kafafunla na sanya da Huffi, ka da ka yi bawali cikin rami, ka da dandani dankali ka da ka shaki kamshinsa har sai kasan yaya yake, ka da ka sha daga ruwan salka har sai kasance menene yake cikinta, kayi taka tsantsan daga wanda ka sani, ka da kayi abota da wanda baka san shi ba.

وقال في الزوجة  :

«اللهمّ ارزقنى امرأةً تسرّني إذا نظرت ، وتطيعني إذا أمرت».

Dangane da mace yana cewa: ya Allah ka azurtani da da matar zata faranta mini idna na kalleta, zata yi mini biyayya idan na umarceta

وقال  7 :

عالم ينتفع بعلمه أفضل من سبعين ألف عابد.

Amincin Allah ya tabbata a gareshi: Malamin da ake amfanuwa da iliminsa yafi falala daga masu bauta dubu.

إن استطعت أن لا تعامل أحدآ إلّا ولک الفضل عليه فافعل .

Amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: idan ka samu dama kan kin mu’amala da kowa sai wanda kake da wata falala a kansa to ka aikata haka.

الكمال كلّ الكمال : التفقّه في الدين والصبر على النائبة وتقدير المعيشة

Amincin Allay a kara tabbata a gareshi yace: kamala da dukkanin kamala shine neman fahimtar addini da hakuri kan musiba da yin tsakatsaki cikin rayuwa

صانع المنافق بلسانک ، وأخلص مودّتک للمؤمن ، وإن جالسک يهودي فأحسن مجالسته .

Amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yana cewa: ka bi Munafuki sannu-sannu da harshenka, ka tsarkake kaunarka ga mumini, idan bayahude ya zauna tareda kai to ka kyautata zama da shi.

إعرف المودّة في قلب أخيک بما له في قلبک.

Imam (as) yace: ka san kauna cikin zuciyar dan’uwanka da kauna da yake da ita cikin zuciyarka.

الإيمان حبّ وبغض.

Imam (as) yace: bawani abu Imani ba face soyayya da kiyayya.

والله ما شيعتنا إلّا من اتّقى الله وأطاعه ، وما كانوا يعرفون إلّا بالتواضع والتخشّع ، وأداء الأمانة ، وكثرة ذكر الله، والصوم والصلاة والبرّ بالوالدين…..

Imam (as) yace: ba kowa ne ke zama Shi’armu ba face wanda yake jin tsoran Allah ya kuma yi masa biyayya, ba a sanin Shi’armu face da tawal’unsu da kushu’i, da sauke amana, da yawan zikiri, da azumi da sallah da biyayyar iyaye.

من صدق لسانه زكى عمله ، ومن حسنت نيّته زيد في رزقه ، ومن حسن برّه بأهله زيد في عمره ...

imam (as): duk wanda ya harshensa ya kasance mai fadin gaskiya ayyukansa zasu tsarkaka, duk wanda niyyarsa ta kyawunta arzikinsa zai karu, duk wanda ya kyautatawa iyalansa Allah zai kara masa tsahon rai.

Tura tambaya