sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » darussan yakini cikin sanin asalan addini
- » Gudummawar da addu’a take bayarwa a rayuwa
- Tarihi » Rayuwar Imam Aliyu Bn Husaini Assadaj atakaice
- Tarihi » isar da sakon yunkurin Ashura
- » Kalmar Ustaz Sayyid Adil-Alawi ga daliban makarantar tadabburul kur’an
- Tarihi » Al'ummar Jahiliya gabanin aiko da Annabtar cikamaki
- » Darussan hauza> bahasul karijul fikihu 22 ga rabi'u Awwal shekara ta 1439 hijri- zartar da istis'habi da hujjiyarsa cikin shakka sa'ilin shafe shari'ar data gabata da mai riskuwa (38) Birnin Qum mai tsarki- tare da samahatu AyatollahAssayid Adil-Alawi
- » SAUTIN KIRAN HANKALI-TARE DA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
- » MASH'ARUL HARAM
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » WANENE YA FI HATSARI TSAKANIN NAFSUL AMMARA DA SHAIDAN?
- Tarihi » lokacin tsanani da kuntatawa
- » Falalar ilimi da malamai
- » falsafar humanism (mutumtaka) ka'ida ce ta mazhabar Almaniyanci
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Yaya dalibin ilimi zai iya sanin makomarsa?
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga mafificin halittun Allah Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Bayan haka: hakika mai hikima cikin littafinsa mai girma ya ce:
﴿يَرْفَعْ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ﴾.
Allah ya na daukaka darajojin wadanda sukai Imani da wadanda aka baiwa ilimi.
Babu kokwanto daukakar mutum da girmamarsa da daukakar mukaminsa kadai dai yana cikin iliminsa mai amfani, wanda ya tsayu da gaskiya da iklasi da cika alkawari, duk sanda mutum ya karu da ilimi da aiki sai ya karu cikin daukaka da dagawa da kusanci daga madaukaki mafi daukaka jalla jalaluhu, lallai Allah yana daukaka darajarsa a lahira da karatunsa da ayyukansa (yi karatu ka samu daukaka) babu shakka cewa darajojin lahira cikin aljannoni suna banbanta daga darajojin duniya da darajojin barzahu.
Shi ilimi tsani ne na samun daukaka ga mutum da hawansa zuwa ga kololuwar kamala, da kuma kololuwar mutumtakarsa, ya zuwa abin da Allah ya ajiye cikin halittarsa lafiyayya kuma samammiya daga son kyawu da alheri da kamala.
Lallai Allah matsarkaki yana kaunar masu neman ilimi wadanda suke fitowa daga gidajensu su tafi neman ilimi dare da rana, kadai dai ya kaunace su saboda shi Allah matsarkaki shi ne ilimi cikin zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, shi ne masani mai sani mai yawan sani gaibobi, ya san abin da yake sammai da abin da yake kasa, ya san sirri da boye, babu wani abu da yake buya daga iliminsa ko da gwargwadon kwayar zarra ne cikin sammai da kasa, ya san abin da rayuka ke boyewa da zukata, ya san mai ha’intar idanu, Allah Azza wa Jalla shi ne tsantsar ilimi, babu wanda ya san shi waye sai shi, idan ya so bawa sai ya bashi daga iliminsa ya fahimtar da shi rayuwa.
Sai dai cewa wannan ilimi na Allah bari dai da dukkanin wani abu mai kima da daraja, da abin da yake kishinyantarsa cikin duniya da abin da yake sabawa da shi da wani abu jabu da wanda ba a kwadayinsa, sai dai cewa shi yana bayyana mai cudanya da tufafin gaskiya mai yin ado da hakika, wannan shi ne abin da kur’ani mai girma yayi ishara zuwa gare shi kamar yanda yake cikin fadinsa madaukaki:
﴿فَأَمَّا الزَّبَدُ فَيَذْهَبُ جُفَاءً وَأَمَّا مَا يَنفَعُ النَّاسَ فَيَمْكُثُ فِي الأَرْضِ﴾،
Amma kumfa sai ya tafi kekasasshe amma abin da yake amfanar da mutane sai ya zauna cikin kasa.
Tafki lokacin da yake tuma yake cakuda igiyar ruwa a samansa za kaga wani yanki na kumfa yana bayyana da za ai tsammani cewa daga ruwa take, sai dai cewa cikin wannan kumfa babu komai sai iska, idan akwai ruwa ciki to lallai zai zauna cikin tafki.
Cikin duniya akwai sinfi biyu masu kishiyantar juna a ko da yaushe kamar kishiyantar da ke tsakanin dare da rana, sune malamai da jahilai, sakamakon kishiyantar da take tsakanin ilimi da jahilci, sau da yawan lakuta jahili yana rigantuwa da rigar malamai sai dai cewa shi daga jabun kumfa yake.
Wannan lamari ne mai hatsari sakamakon cudanyar takardu da rikicewar lamari kan mafi yawan mutane, suna bin mutumin da bai kasance malami ba a hakikani da gaskiya, sai dai cewa shi kawai yana nuna cewa yana da ilimi, wannan rikicewar lamari yana gudana cikin da yawa-yawan abubuwa masu karo da juna da kishiyantar juna cikin dukkanin kasashe da zamani.
Mafahim din zamantakewar juna da siyasa nawa ne damu da abubuwa cikinsu suke rikicewa tsakanin hakikani da jabu tsakanin gaskiya da karya.
Kamar muslunci da ilimi da siyasa da fanni da juyin-juya hali, ta iya yiwuwa mutum ya kasance dan siyasa. haka ma musulmi zai iya kasancewa masani wani fanni daga fannoni ko kuma masani fanni musulmi, kuma mu samu dan juyin-juya hali mumini, ko kuma mumini dan juyin-juya hali, banbanci nawa ne tsakaninsu na tushe.
Bayanin haka: me ye banbanci tsakanin musulmi da dan siyasa da dan siyasa da musulmi? Wannan tambaya bijirarra ce a fage da wannan lokaci.
Domin kaiwa zuwa ga abin da muke muradi daga takaitaccen bayani cikin wannan lamari mai muhimmanci za mu buga misali kan haka domin ya kasance matsayin sharar fage domin shiga cikin maudu’i, daga bayyanannen lamari ne cewa buga misali daga bayansa akwai hikima da manufofi kamar yanda ya zo cikin kur’ani mai girma:
﴿وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ﴾ ﴿وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ﴾ ﴿لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ﴾.
{domin suyi tunani} {babu masu hankaltuwa da ita face masu ilimi} {saransu sa tuna}
Wane abu yake banbanta tsakanin mumini Ali bn Abu dalib (a.s) da Mu’awiya bn Abu Sufyanu dan wuta, dukkaninsu a wurin wasu musulmai suna siffantuwa da halifancin manzon Allah (s.a.w), sarkin muminai halifa na hudu wurin wasu mutane amma wurin mu Imamiya halifa ne na farko ba tare da yankewa ba ga manzon Allah (s.a.w) kamar yanda Mu’awiya kadai ya fizge sunan halifanci da zalunci da fin karfi a kansa, sai ya zama kowanne daya daga cikinsu yana siffanta da halifancin manzon Allah (s.a.w) dukkaninsu su biyun suna sallah suna azumi suna shaidawa da shahada biyu sai dai cewa daya daga cikinsu musulmi ne dan siyasa dayan kuma dan siyasa musulmi, dayansu haske ne kuma gaskiya ne, dayan kuma bata da duhu yaya za mu banbance tsakaninsu, dukkaninsu musulmai ne yan siyasa, sai dai cewa dayansu musulmi ne dan siyasa dayan kuma dan siyasa musulmi?
Muhimmanci banbance wannan maudu’i bai buya ba, lallai ya zama dole a yi Karin bayani kansa daga lafiyayyar mukaddima domin natija ta kasance lafiyayya ta hanyar lafiyar mukaddimar da aka gina kanta daga (sugrayat) da (kubrayat) kamar yanda yake cikin limin mandik.
A takaice muna cewa: lallai banbanci tsakaninsu shi ne lallai shi dan siyasa musulmi yana sanya addini da hukunce-hukuncensa kamar sallah da hajji cikin amfani da su a siyasarsa shin cikin gama garin maslaha ne ko kebantacciya, lallai shi duk da kasantuwarsa musulmi sai dai cewa yana siyasantar da addinin muslunci cikin maslahohinsa, ya dinga amfani da addini cikin bukatun siyasarsa, idan wata rana addininsa da siyasarsa sukai karo da juna lallai zaka same shi yana mai gabatar da siyasarsa da fifita ta kan addini, sai ya fice daga addini yayi munafunci ya dinga rigantuwa da muslunci a zahiri sabanin badini, kamar yanda shugaban shahidai (a.s) ya fada:
(والدين لعق على ألسنتهم يحوطونه أينما درّت معائشهم)،
Mutane bayin duniya addini kuma kadai damfare yake kan harsunansu sune kewayawa duk inda rayuwarsu ta juya.
Yana daga cikin munafuncin siyasa dan siyasa ya kasance musulmi, shi ne wanda yake sanya addinin cikin bukatarsa ta siyasa, matukar dai muslunci bai yi karo da bukatunsa na kashin kansa ba da siyasarsa to shi musulmi zai kuma dinga nuna muslunci da sallah, amma idan ya kasance addini yana cutar da siyasarsa lallai zaka same shi cikin gaggawar ya sauya ya bayyanar da ainahin aniyar da take boye cikinsa daga munafunci ya kuma yi wurgi da watsi da addini, ya kasance daga munafukan musulmai, lallai shi yana bayyana muslunci yana boye da kafirci, sai ya dinga shaidawa da kalmomin shahada biyu a zahiri kamar yanda zaka same shi ya na sallah sai dai cewa shi a badininsa cike yake da kafirci, kamar yanda Yazidu bn Mu’awiya (l.a) bayan kashe Shugaban Shahidai Imam Husaini (a.s) ya raira wake yana fadin:
(لعبت هاشم بالملك فلا خبر جاء ولا وحي نزل)،
Banu Hashim sun yi wasa da mulki ba tare da wani labari da ya zo ba ko wani wahayi da ya sauka ba.
Bari dai kakansa ma Abu Sufyan ya fadi kwatankwacin haka a lokacin halifancin Usman bn Affan yana mai cewa (Babu wata Aljanna ko Wuta) ya Banu Umayya ku jujjuya wannan mulki kamar jujjuyawar kwallon kafa, zahirinsa daga musulmai amma badininsa daga kafirai, wannan shi ne ainahin munafunci a cikin akida da aiki, wannan Kenan cikin tasnifin dan siyasa da ake kirga shi (dan siyasa musulmi) shi ne wanda yake sanya addini cikin hidimtawa bukatunsa da muradunsa da manufofinsa.
Amma musulmi dan siyasa kamar misalin sarkin muminai Ali (a.s) lallai shi ya ce (lallai Mu’awiya bai fini iya shirya makirci da dabara ba) domin Mu’awiya ya shahara wurin larabawa a wancan lokaci dacewa shi ne yana daga makiran larabawa, kadai dai tsoran Allah ne yake hana Imam Ali (a.s) aikata abin da Mu’awiya ya aikata, sarkin muminai ya kasance yana siffantuwa da zuhudu da tsantseni da tak’wa, abin da yake wajabta masa sanya siyasa cikin hidimtawa addini bawai akasi ba kamar yanda Mu’awiya yayi. Lallai shi tsantseni da tak’wa suna hana sanya addini cikin hidimtawa maslahohin siyasa, bari suna sanya siyasa cikin hidimar addini cikin tabbatar da shi da yada shi, matukar dai siyasa tana hidimtawa addini lallai zai dauketa kayan aiki domin kaiwa ga Allah matsarkaki madaukaki, da wannan ne musulmi yake kasantuwa dan siyasa bawai dan siyasa musulmi ba.
Wannan ma’ana na gudana cikin da yawa-yawan wurare masu kama da juna, misali masanin fanni musulmi yana sanya muslunci cikin hidimtawa fanninsa, musulmi masanin fanni ya na sanya fanninsa cikin hidimtawa musluncinsa, haka ma mawaki musulmi yana sanya da musulmi mawaki, da dan gwagwamaya mumini, da mumini dan gwagwarmaya, lallai shi mumini dan gwagwarmaya yana sanya gwagwarmayarsa cikin hidimar imaninsa, daidai lokacin da dan gwagwarmaya mumini ke sanya imaninsa cikin maslahar gwagawarmayarsa, ka lura sosai.
Banbanci nawa tsakanin dan gwagwarmayar juyin-juya hali mumini da kuma mumini dan gwagwarmaya, lallai na farko ko da larura ta hukunta masa wofinta daga imaninsa lallai shi da wahamansa da hiyalansa zai wurgi da Imani jikin bango, yayi tsammani cewa shi yana kyawunta aiki da aikata hakan, saboda ma’auni da abin la’akari a wurinsa shi ne gwagwarnayarsa, sai yayi kiyasi ya auna kansa da ma’auni da sikelin gwagwarmaya, idan addini da mazhaba da ilimi da fanni suna hidimtawa gwagwarmayarsa lallai zai rikesu a matsayin kayan aiki tsani don cimma bukatar gwagwarmayarsa, amma idan addini da mazhaba sukai karo da gwagwarmayarsa lallai anan ne zaka same shi ya bayyanar da munafuncinsa, ya wofintu daga addini da mazhaba a kimomin kyawawan halaye da madaukakan siffofi.
Dalibin ilimi da Imani:
Idan kana son sanin makomarka da ka jahilta to hakan zai kasance da tunani da zurfafa tunani domin shi tunani shi ne jagoran hankali, idan baka da tunani ta yaya hankalinka zai kasantu, idan tunani ya kasance mara kyawu hankali zai kasance mara kyawu, idan kuma ya kasance mai kyawu to hankali ma zai kasance mai kyawu, kamar yanda hankali yake jagoran zuciya, abin da yake darsuwa kan zuciya kadai dai daga wahayin hankali yake, sannan ita ma zuciya itace sarauniyar gangar jiki, gabbai da jijiyoyi suna bin iradar zuciya da abin da take so da umarnoninta da haninta.
Duk wanda yake son sanin makomarsa da ya jahilta, daidai lokacin da lallai shi bai sanin meye karshen lamarinsa da karatunsa, to kaka kuma makomar imaninsa, domin lallai daga Imani akwai wanda yake tabbatacce zaunanne har zuwa ranar tashin alkiyama, haka daga Imani akwai wanda yake na ajiya ana kwace shi lokacin fitar rai da mutuwa ko kuma gabaninsu.
Imani na ajiya ana sanya shi wurin mutum kamar matsayin kayan ajiya zuwa wani tsawon lokaci, sai ka samu kufaifayi da alamomin Imani suna bayyana gare shi da alamomin mumini kamar misalin sallarsa da azuminsa da riko da addini, sai dai cewa shi a gobe nan gaba za a cire shi daga gare shi, sai ya koma bayansa, ya shiga da’irar bata ya kasance batacce, idan kuma ya batar da wasu sai ya zama mai batarwa, wannan yana daga tsiyata ta dindin kuma karshensa wuta da azaba.
Wanda kuma imaninsa ya kasance zaunanne har zuwa ranar tashin kiyama, lallai shi guguwa ba ta iya girgiza shi, shi kamar dogon dutse yake, kafarsa na tabbace, mai karfin zuciya da tsaurin Imani, kayace-kayacen duniya basa iya rudar da shi, haka ma dadin siyasa da alfarmar da mukami.
Haka zalika dalibin ilimi cikin hauzozin ilimi, lallai shi bai san me ye makomar rayuwarsa da iliminsa ba, shin zai kasance daga ilimi mai amfanarwa cikin addini da duniya da lahira, ya janyo daukakar darajarsa da kusancinsa zuwa ga rayayye tsayayye, lallai Allah matsarkaki madaukaki daddadan zance yana hawa zuwa gare shi aiki na gari yana daukaka shi, daukaka aiki na tare da daukakar ma’aikaci, lallai shi aiki ma’aluli ne illarsa kuma itace mai aikata shi mai yinsa, idan ya daukaka aiki to babu shakka da kokwanto zai daukaka mai yi aikin, sai ya kasance cikin aljannoni da koramu, cikin matsugunin gaskiya wuroin sarki mai ikon yi.
Misalin wannan ilimin mai cike da haske Allah yana jefa shi a zuciyar wanda ya so shiryar da shi, yana kuma janyo daukakar darajarsa, lallai Allah yana daukaka wadanda sukai Imani daraja daya, domin su bude kofar taskokin aljannoninsu da hakan, sannan yana daukaka masu ilimi da darajoji (yi karatu ka smu daukaka) hakan na kasancewa ne sakamakon neman haske da sukai cikin rayuwa, misalin wannan ilimi zai amfanar da mu a rayuwarmu ta nan gaba da ma bayan mutuwarmu, da cikin kabari da barzahu da ranar tashi daga kabari a taron kiyama da ma cikin aljanna, lallai shi yana daga haske wanda Allah ya sanya shi gare shi cikin rayuwarsa domin yayi tafiya tare da shi, kamar yanda yake kai kawo a gabansa da geffansa damansa ranar kiyama, domin ya dauke shi ya kai shi cikin aljanna, kamar yanda julmar riwayoyi da ayoyi suka zo da bayanin haka.
Sannan lallai wannan ilimi na haske mai cike da albarka, yana sanya kabarin malami cikin dausayi daga dausayoyin aljanna.
Amma ilimi idan bai kasance domin Allah ba bai kasance ana aiki da shi ba, zai kasance mafi girman hijabi zai janyo tsiyata a duniya, kamar yanda zai mayar da kabari ramin wuta.
Duk wanda yake neman ilimi don Allah da Allah zuwa ga Allah jalla jalaluhu, lallai shi da wannan niyya zai shiga hanya zuwa ga aljanna, lallai tabbas wadanda suke sama da kasa zasu dinga nemar masa gafara, kai hatta kifaye da suke ruwa ba a barsu a baya ba wajen nema masa gafara, sannan a sama za a kira shi mai girma.
A nan akwai wata tambaya ta larura da take bijirowa, shi ne yaya zan san gobe ne ta ilimi, shin ilimina yana daga ilimi mai amfanarwa, ko kuma dai yana daga ilimin da annabi (s.a.w) yake neman tsari daga gare shi
(اللّهم إني أعوذ بك من علم لا ينفع)
Ya Allah ina neman tsarinka daga ilimin da ba ya amfanarwa.
Kamar yanda yake cikin addu’a bayan idar da sallar la’asar cikin kowacce rana, sai ka lura, ta yiwu cikin kowacce rana mutum ya jarrabtu da ilimin da bazai amfanar da shi ba, bari dai ma zai cutar da shi ne ya kuma kasance hijabi mafi girma wanda zai hana shi kaiwa zuwa ga Allah, zuwa ga aljanna da ni’imarsa, sai ya zama ya bayyana karara cewa akwai ilimi mai amfani akwai mai cutarwa, akwai ilimi wanda karshensa yake kasancewa dausayi daga dausayoyin aljanna, dayan kuma karshensa rami daga ramukan wuta, ilimin da yake jawo azurtuwa cikin gida biyu, dayan kuma yana jawo tsiyata cikin duniya da lahira.
Ilimi ne da ma’abocinsa zai farantawa yan aljanna da shi, dayan kuma ilimi ne da zai cutar da hatta yan wuta daga warinnsa!!
Kamar yanda ya zo cikin hadisi.
wanne ilimi ne wannan da har yan wuta ke cutuwa da shi, ballantana yan aljanna, da har za su roki Allah matsarkaki ya kubutar da su daga wannan malami da aka tashe su daga kabari tare da shi sakamakon doyin da wari da yake yi, lallai hakan yafi tsanani daga azabar jahannama, me yafi girma daga misalin wannan azaba ta ruhi da ta gangar jiki shi kasantuwa kusa da malamin da bai yi aiki da iliminsa ba, wannan wani abu da dalili da kur’ani da dabi’a suke gasgatawa, duk wanda Allah ya bude masa idanunsa na barzahu cikin duniya lallai zai cutu daga malami fasiki lalatacce, ya ji warinsa yayin zama tare da shi.
Farin ciki ga malami mai tsoran Allah, wanda ya koyi karatu don Allah, yayi aiki don Allah, ya koyar don Allah, lallai za a kira shi cikin malakut samawat mai girman matsayi, kamar yanda hakan ya zo daga Imam Sadik (a.s)
الإمام الصادق×، وبئس العلم والعالم الذي لم ينتفع من علمه، بل كدّس العلوم في ذهنه حتى صار كالمكتبة السّيارة، وكالحمار يحمل أسفاراً، وكان علمه حجابه الأكبر.
Tir da ilimi da malami wanda bai amfanu da iliminsa ba, kadai dai ya taskace ilimummuka cikin kwakwalwarsa har ya zama kamar dakin nazarin karatu mai tafiya, kamar misalin jaki yana dauke da manyan litattafai, iliminsa ya zama hijabi mafi girma.
Yaya zan san makomar ilimina da karshen lamarina cikin duniya ta da lahirata, me zai kasance makomata, daga ina zuwa ina cikin ina, me ake nema daga gareni, mene ne falsafar da hikimar halitta ta da rayuwata, yaya zai zama ban zama kamar malamin da ya tofa yawu kan kur’ani mai girma lokacin mutuwarsa, in kasance daga malamin da zai salati kan waliyan Allah A’imma tsarkaka, kamar yanda yayi sallama ga Mala’ikun da aka umarce su da karbar ransa.
Da yawa-yawan malamanmu sun kasance suna sallama kan wanda suka halarce su daga Mala’iku da A’imma (a.s) lokacin mutuwarsa, shi mai kakakin mutuwar ya kasance shi yana ganin Mala’iku duk da cewar wanda suke kewaye da shi basa ganinsu kamar yanda ya zo a hadisai.
Yaya makoma ta za ta kasance?! Daga wanne sinfi zan kasance daga sinfofi uku wadanda sarki mumini Ali (a.s) ya ambace su ga Kumailu bn Zayad Naka’i (rd), daga cikin malamai akwai malami mai tsoran Allah, daga cikinsu akwai mai koyan ilimi don neman tsaro, kashi na karshe yan abi yarima asha kida, suna amsa sautin dukkanin mai kira suna juyawa tare da kowacce iska.
Malami na Allah dangananne zuwa ga ubangijin talikai, wanda ya tarbiyantu da tarbiyar Allah malakutiyya, hakika yayi zuhudu cikin duniyarsa, ya tsarkake niyya cikin iliminsa, sai da farko in fara da mai neman ilimin don samun tsira, sannan in tsallaka zuwa ga marhalar malami na Allah waliyin Allah in dinga shiryar da mutane zuwa hanyar shiriya, su malamai na Allah jagorori al’ummu magada annabawa da wasiyyai (a.s) sun gaji ilimi da Akhlak da mas’uliyar tablig da isar da sakon sama.
﴿الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالاتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَهُ وَلا يَخْشَوْنَ أَحَداً﴾ .
Wadanda suke isar da sakon Allah suke jin tsoransa basa jin tsoran kowa.
Kamar yanda fakihai shugabanni suke shiryar da su zuwa daidai da ayyuka da mafi alherin aiki, ya zuwa hanya mikakka tafarki madaidaici.
Shugabanci da jagoranci nagari kadai suna hannun malamai nagargaru da fakihai yardaddu, abin nema daga dukkanin wani dalibin ilimi cikin Hauza ilimiyya, shi ne ya kasance kan mustawar da kae bukata daga gare shi, daga malamai na Allah wdanda zargin mai zargi cikin Allah kansu musammam ma siddikai, kalamansu kalamai ne na rabautattu, masu raya dare masu zama fitila manara da rana, masu riko da igiyar kur’ani da tsatso tsarkaka (a.s) suna raya sunnonin Allah da manzonsa, zukatansu na cikin aljannoni jikkunansu na cikin aiki.
Matafiyar dalibin ilimi shi ne da farko ya yi kokari ya nesantar da kansa daga biyewa sha’awe-sha’awen dabbanci, yayi samu iko kan danne fushinsa da sha’awarsa cikin samuwarsa, da sanya hankali da dalci da hikima, sannan ya kasance mai neman ilimummukan Allah domin neman tsira, haka ma ya hau jirgin tsira, jirgin Muhammad da iyalansa (s.a.w) sannan misalin Alil-baiti gidan annabi mafi girma kamar misalin jirgin annabi Nuhu (a.s) duk wanda ya hau ya tsira duk wanda ya juya baya ya nutse cikin teku ya halaka, makomarsa ta kasance tsiyata da wuta da azaba, sannan cikin marhalar ta uku ya kasance daga malamai na Allah ya jagoranci mutane ya zuwa bakin gabar amintuwa da aminci ya zuwa ni’ima da aljannoni.
Anan ina da tambaya kai ma kana da tambaya dukkanmu muna tambaya, yaya zan kasance malami na Allah ta yaya zan lamintar da makoma ta wacce take jahiltacciya ban santa ba?!
Tsoro da fata:
Babu kokwanto cikin kasancewa lallai shi mumini yana rayuwa tsakankanin tsoro da fata, su tsoro da fata haske ne guda biyu cikin zuciyar mumini da za a auna daya kan daya da bai rinjaye shi ba, ba a san makoma da goben dalibi ba tun farkon shigarsa Hauza Ilimiyya, ta yiwu nan gaba ya zama kamar misalim Mirza Ali Muhammad Bab wanda yayi da’awar na’ibantakar Imam Mahadi (a.s) sai ya zamanto ya bace ya kuma batar da mutane, shi ne wanda ya haifar da kungiyar Baha’iya ta wannan zamani domin yakar shi’anci, ko kuma ta iya yiwuwa ya zama kamar Shaik Muhammad bn Abdul-wahab Najadi wanda ya assasa mazhabar wahabiyanci masu kafirta musulmai, ta yanda yake kafirtar da duk wanda bai bin mazhabarsa shin daga shi’a yake ko daga sunna kamar misalin Ash’arawa da sufaye babu banbanci.
Muhammad bn Abdul-wahab ya kasance cikin dangin ma’abota ilimi mahaifinsa yana daga cikin manyan shehunai haka ma dan’uwnasa, kai farkon ma wanda ya fara inkarin mazhabarsa ya bayyana shi a matsayin bataccce mai batarwa shi ne dan’uwansa Salman bn Abul-wahab, wannan Magana tabbatacciya ce a muhallinta.
Bai buya ba cewa yan mulkin mallaka suna cin amfanin misalin wadannan dalibai cikin Hauza Iimiyya, domin su batar da mutane da rusa addini da mazhaba da sunan addini da mazhaba, kadai suna daukar su aiki da jan hankalinsu da kudade masu yawa da mata da alfarma da mukami, sakamakon raunin da suke da shi da karkacewar tunani da yake cikin badininsu.
Babbar musiba itace sakamakon hura wutar fitina da bata yan mulkin mallaka kamar misalin kasar birtaniya, sai ka samu kowacce da’awa ta samu mabiya, da’awar ta yadu cikin mutane kamar ruruwar wuta cikin kirare, kamar cikin wannan lokaci da muke ciki ta yanda muke iya ganin wahabiyawa yan sunna da baha’iyawa daga shi’a basu gushe ba suna taka rawa cikin bata da batarwa, asasin wadannan mazhabobi biyu na bata daga daliban ilimi ya kasance, wannan shi ne abin da muke jin tsoro cikin nan gaba a hauzozin ilimi, lallai da sunan addini za ka samu wani daga dalibai ya assasa sabuwar mazhaba ya rarraba kawukan al’ummar musulmi, ya shuka fitina da munafunci da sabani da rigima da kiyayya da gaba tsakanin musulmai, wanda wannan shi ne kololuwar abin da makiya addini yan mulkin mallaka suke fata, daga mummunar siyasarsu ta nuna kiyayya da suke cewa (raba kansu sai ka mallake su) sai suna mulkin kasashen musulmai ta hanyar rarrabawa kawukansu da yada sabanin cikinsu da rigingimu na zubar da jini domin su samu iko kansu, da iko kan dukiyoyinsu, a irin wannan hali ni da nake dalibin ilimi yaya zan amintar da kaina da makoma ta, yaya zan katangeta da samun lamini kan tsiranta a nan gaba.
Ya zama dole a yi tunani da sanya wayewa da taka tsantsa, sannan kuma muyi riko da nauyaya guda biyu littafin Allah da tsatso tsarkaka (a.s) lallai matukar munyi riko da su ba zamu taba bata ba har abada kamar yanda manzon Allah (s.a.w) ya bada labari cikin hadisin Saklaini wanda bangarori biyu suka nakalto shi.
Ya zama dole a koma komawa ta gaskiya zuwa ga Ahlil-baiti ma’asumai (a.s) lallai zancensu haske ne, lamarinsu shiriya ne, wasiyyarsu tak'wa ce, aikinsu alheri ne, al’adarsu ihsani.
Idan kana son sanin makomarka da gobenka kan hasken makarantar Ahlil-baiti (a.s) to abin da ya zo daga sarkin mumi Ali (a.s) a littafin Nahjul Balaga ya isar maka:
(إذا إشتبهت عليكم الأمور فيعرف أواخر الأشياء بأوائلها).
Idan al’amura suka rikice muku to ana sanin karshen abubuwa daga farkonsu.
Wannan yana daga cikin mafi kayatarwar abin da ake fadi cikin sanin goben da aka jahilta, lallai kamar yanda yake a cikin ilimin mandik (natija na biye mafi karancin mukaddima) duk sanda dukkanin mukaddimomi suka kubuta daga sugrayat da kubriyat a wannan lokaci natija za ta kasance lafiyayya kubutatta ingantacciya da za a iya dogaro da ita da jingina gareta, za kuma a kafa hujja da ita a mukamin kawo hujja.
Duk wanda yake son sanin karshen karatunsa da neman ilimin muslunci da yake yi, da kasantuwarsa mai neman ilimin don samun tsira, sannan ya kuma kasance malami na Allah da yake shiryar da bayi, kadai zai san hakan tun ranar farkom shigarsa Hauzar ilimi.
Me ya sanya shi bari garinsa da zuwa wata kasa mai nisa don neman ilimi me ya sanya ya zabi karatun Hauzar ilimi mai albark, me yake nema da wannan karatu da yake da koyarwa da wallafe-wallafe da tabligi, da dukkanin abin da yake cikin sha’anin malaman addini cikin jama’a, shin ya sanya mafara da manufa ga Allah matsarkaki kuma don shi
(إنّا لله وإنا إليه راجعون)
Daga Allah muke gare shi za mu koma.
Ko kuma dai don duniya da tarkacenta da alfarma da mukami da riya da alfahari yake yin karatun.
Bai buya ba cewa yawancin daliban Hauza daga manisantan garuruwa da kasashe suke zuwa sun bar Ahalinsu da iyalansu don neman ilimi, sun yarda da talauci da bakunta da radadi da bakin ciki, dukkanin hakan domin su kasance makamai na Allah, su koma ga mutanensu domin gargadarsu dammaninsu su gargadu, kamar yanda Allah matsarkaki cikin littafinsa mai cike da hikima mai girma.
Ta yanda musulmai suka kasance farko-farkon muslunci da cikin zamani annabi mafi karamci, dukkaninsu suna fita zuwa jihadi saboda kaunar jihadi da shahada, sai matsarkaki madaukaki ya ce:
﴿وَمَا كَانَ الْمُؤْمِنُونَ لِيَنفِرُوا كَافَّةً فَلَوْلا نَفَرَ مِنْ كُلِّ فِرْقَةٍ مِنْهُمْ طَائِفَةٌ لِيَتَفَقَّهُوا فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُوا قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُوا إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ﴾.
Bai kamata dukkanin muminai su fita jihadi ba saboda haka me zai hana wata jama’a daga kowanne bangare ba zasu rage a gid aba domin su nemi ilimi cikin addini su gargadi mutanensu iadan sun dawo gare dammaninsu sa gargadu.
Idan Allah aka nufa, lallai shi yayiwa wadanda suke jihadi cikin tafarkinsa da cewa tabbas zai shiryar da su zuwa ga tafarkinsa madaidaici, da kuma tabbatar da diga-digansu
﴿وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ﴾.
Kuma wadanda suka yi kokari don neman yardarmu tabbas zamu shiryar dasu tafarkinmu lallai Allah yana tare da masu kyautatawa.
Idan niyya ta kasance ta gaskiya tsarkakka, abin nufi da neman ilimi shi ne neman kusancin Allah matsarkaki, ya kuma kasance mai kira zuwa ga tafarkin ubangijinsa da hikima da kyakkyawan wa’azi, da kuma jayayya da abokin rigima da wacce tafi kyawu, wannan shi ne abin da ake nufi da kyakkyawan karshe a dunkule, saboda ana sanin karshen abubuwa ta hanyar farkonsu.
Duk wanda ya kasance mai komawa ga Allah kamar yanda Ibrahim (a.s) ya kasance cikin kiransa zuwa ga hajji
(هلّموا إلى الحج)
Ku taho ku taho zuw aga hajji.
Kumar kamar yanda shugaban shahidai ya kasance cikin kiransa ranar Ashura
(هل من ناصر ينصرني)
Shin akwai wani mai taimako da zai taimakeni.
Lallai kiransu su biyun kira ne na Allah da annabta, ku amsawa Allah da manzonsa idan suka kira ku zuwa ga abinda zai raya ku.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- SHIN MUTUM YANA DA ZABI KO KUMA AN MASA TILAS NE_TAREDA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
- Ta Yaya dalibi zai iya sanin gobensa
- KARIJUL FIKHU 23 MUHARRAM 1441 H IHTIYADI SHINE RASHIN UDULI DAGA SURATUL JUMA’A DA MUNAFIKUN ZUWA WASUNSU RANAR JUMA’A
- KARIJUL FIKHU 17 MUHARRAM 1441 H CIGABAN BAHASIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA SURAR
- Kowacce rana ashura ce kowacce kasa ma karbala ce
- Akhlak din husainiyya tare da samahatus shaik husaini ansariyan
- Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- TAKAITACCE SAKO KAN ASALAN ADDINI DA RASSANSA
- Taskar Adduoi 4
- Wasu takaitattun bincike da zasu amfanar da mumini da mumina.