lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

HASKE DAGA RAYUWAR SHUGABA KOMAINI

Mujaddadin karni na goma sha biyar shugaban mujtahidai masu girman daraja, limamin yan gwagwarmaya masanin fikihu Arifi Abidi Ayatullahi Al’uzma Assayid Ruhullahi Musawi Komaini.

Hakika rayuwarsa abar kwaikwayo ce kuma haske ce mai haskaka kan hanyar Muminai, lallai shi mutum ne daya tilo cikin wannan zamani hakika ya tattaro siffofi da suka fi kusa da a kamanta su masu kishiyantar junam shi masanin hikima da falasafa fa shi kuma Arifi Mujtahidi, `dan gwagwarmaya da neman sauyi mutum mai cike da hamasa Mujahidi, ga shi Fakihi kuma masanin ilimin Usul da Rijal kwararre, ga shi masanin siyasa gogagge cikinta, wadnanan jumloli ba komai bane face cikin tafin hannu daga baiwowin da Allah yayi masa a rayuwa.1

Mahaifiyarsa: tsarkakka Hajara diyar bawan Allah nagari Yusuf Kan, hakika ta rungumi kula da marayan `danta tareda taimakon gwaggonsa tsarkakka wacce ake kira da Sahiba, Allah ya karbi ranta lokacin da bai gama kammala shekaru goma sha biyar ba a duniya, bayan kankanin lokaci da mutuwar gwaggonsa sai ita mahaifiyarsa ta amsa kiran ubangijinta ta koma ya zuwa gareshi.

Danginsa da matarsa: Assayid Komaini ya yi aure a shekara ta 1349 hijri lokacin yana da shekaru 28 a duniya ya auri diyar Ayatullahi Alhaji Mirza Muhammad Assakafi Taharani ya aureta tana da shekaru 16, sannan ta Haifa masa Ayatullahi Ashshahid Musdafa da Hujjatul Islam Assayid Ahmad da kuma `ya`ya mata guda uku,

Sannan Imam Komaini ya yi surukurtaka da Ayatullahi Shaik Shahabbudini Al’ishraki da Daktor Muhammad Burujudi Al’arabi  jikan Allah ya jikan rai Akundi.

Karatunsa:ya koyi karatu da rubutu a hannun wani malami a a garin Komaini wanda ake kiransa Mirza Mahmud sannan ya koyi adabin farisanci a wurin Abu Kasim da Shaik Jafar haka kuma a wurinsa ya koyi ilimin Nahawu da Sarfu, sannan ya halarcidarasin Mirza Ahmad Mahadi wanda ya kasance `dan’uwan mahaifiyarsa, ya koyi littafin Mandik Suyudi da Almudawwal a wurin dan’uwansa wanda ake kira da Assayid Murtada Fasandide har zuwa shekara ta 1338, sannan ya yi hijira zuwa Hauzar garin Arak wacce Ayatullahi Shaik Abdul-Karim Ha’iri ya shugabance ta , sai ya karanta littafin Allum’atu a wurin Shaik Abbas Araki, sannan yayi hijira tareda Shaik Ha’iri zuwa birnin Qum mai tsarki, Shaik Ha’iri ya assasa Hauza a Qum mai tsarki a shekara ta 1340 , Assayidul Komaini ya zauna a makarantar Darul Shifa a nan ne ya karanta darussan da ake karantawa a matakin suduhu a wurin Ayatullahi Muhammad Takiyu Kuwansarim haka ya halarci bahasul Karij na manyan malamai guda biyu Ayatullahi Ha’iri har tsawon shekaru goma da Mirza Assayid Ali Yasarabi Kashani, haka zalika samu halartar darasin Rida Najafi da Shaik Abu Kasim  da wurin Assayid Burujurdi , ya karanta ilimin Aklak da Sairi da Suluki a wurin Mirza Jawad Aga Maliki Tabrizi  mawallafin littafin Almurakabat da Risalatu Lika’allahi.

A shekara ta 1347 Assayidul Komaini ya shagaltu da koyar da darasin Falsafa a dukkanin ranakun karshen sati Alhamis da Juma’a haka zalika ya kasance yana koyar da darasin Aklak cikin hallarar adadi masu yawa daga masoya ilimi da begensa, a shekara ta 1364 ya fara bada darasin a matakin bahasul Karijul fikhu wal usul a lokacin yana da shekaru 44, hakika Imam ya kece tsaraikunsa sunansa ya daukaka ya yadu cikin zaurukan karatu kasantuwarsa mai dogon bincike da dandaka da sanya lura da zuwa da sababbin nazariyoyi da ra’ayoyi.

Bayan wafatin Ayatullahi Al’uzma Burujurdi sai wasu adadi daga Ahlin ilimi suka kafe kan cewa sai sunyi taklidi da shi amma sai Imam yaki yarda ya janye hannunsa daga buga Risalar taklidi, sai dai cewa bayan dagewa da naci da suka yi tayi sai ya yarda aka buga hashiayr da ya rubuta kan littafin (Wasilatul Najati) Risalar taklidi ta Assayid Abu Hassan Al’isfahani wanda ya bar duniya a 1337 sannan suka buga hashiyarsa kan littafin Urwatul Wuska  sannan daga bisani aka buga Risalar taklidinsa.

Sakamakon yana dauke da hange mai huda da tunani mai kyawu da wayewa da hamasa da cika da Imani mai zurfi domin daukaka muslunci cikin baki dayan duniya, sannan ya dauki nauyin marja’iyya da jagorantar juyin-juya halin muslunci a kasar Iran domin farkawar muslunci ta mamaye duniya baki daya.

Malamansa cikin riwaya: daga cikinsu akwai Muhammad Rida Isfahani ijazarsa tana kaiwa zuwa ga Shaik Ansari, daga cikinsu akwai: Shaik Abbas Qummi mawallafin littafin Mafatihul Jinan daga Mirza Husaini Nuri daga Shaik Ansari, daga cikinsu: Assayid Muhsin Amin mawallafin littafin A’ayanul Shi’a daga Assayid Muhammad Hashim Musawi Ridawi daga Shaik Ansari, daga cikinsu akwai: Assayid Abu Kasim Aldehkardi daga Mirza Muhammad Hashim Isfahani daga Shaik Ansari.

Dalibansa: hakika an samu daruruwan manyan malamai da masana fikihu daga makarantarsa daga cikinsu akwai: Shahidan ilimi da wurin ibada misalin Shahid Shaik Murtaza Mutahhari da Assayid Mudni da Assayid Muhammad Husaini Baheshti da Assayid Mustafa Komaini da Assayid Muhammad Ali Kazi Tabrizi da Assayid Muhammad Rida Sa’idi da Assayid Abdul Karim Hashimi Nejadi da Shaik Fadlullahi Mahallati, ha zalika daga cikin rayayyu akwai Shaik Murtaza Ha’iri da Assayidul Ali Kamna’i  da Shaik Ali Akbar Hashimi  da Ayatullahi Rafsanjani da Shaik Abdullahi Jawadi da babban malaminmu Shaik Fazilul Lankarani  da sauransu.2

Wallafe-wallafensa: ana cewa lokacin tasnifi da talifi ga malaman addini lokacin kankani ta togace tsakankani lokacin da suka kai kololuwa a cikin ilimi da lokaicn suke zama shugabanni da jagororin addini, Assayidul Imam bai tsira daga wannan Magana,  ai dai cewa shi hannunsa ta kyawunta  ta hanyar wallafa talifi mai daraja da litattafai madaukaka kimarsu bata wofinta daga dakunan nazari na shi’a da sunna, daga cikin rubuce-rubucensa akwai abinda da mai karatu ba zai taba wadatuwa daga barinsa ba, lallai shi mutum ne `dan gwagwarmaya `dan kawo gyara kuma Fakihi Usuli Arifi, dukkanin mai kishi zai sha daga daddadan ruwan iliminsa, hakika an buga wallafe-wallafensa lokuta da daman gaske an fara bugawa tun yana dan shekara 28, daga cikinsu akwai:

1-Misbahul Hidaya ila Kilafa wal Wilaya, dangane da Irfani da suluki da mas’alolin fikhu

2- Sharhul Du’a’u Sahar Shahri Ramadan, ya wallafa shi a shekara 1347 cikin Irfani

3-Arba’una Hadisan bakwai daga cikin abubuwan da suka shafi hankali sauran talatin da uku cikin Aklak.

      4-Tahrirul Wasila mujalladi biyu, babban malaminmu Fazilul Lankarani yayi masa sharhi ami suna: Tafsilul Shari’a fi Sharhi Tahrirul Wasila mujalladi 40 haka zalika Shaik Ahmad Mudahhari yayi masa sharhi mai suna Mustanad Tahrirul Wasila.

5-Almukasibul Muharrama cikin fikihun istidlali mujalladi biyu.

6- Albai’u mujalladi biyar shima fikhul istidlali ne.

7-Kitabul Dahara mujalladi uku fikhul istidlali.

8-Arrasa’il mujalladi biyu ya kunshi bahasi kan ka’idojin fikhu misalin ka’idar La darara Atta’adul da sauransu.

9-Asrarul Salat, risala ce kan Aklak da Irfani.

10- Risala fi Dalabul wal Idara (Usulul Fikhu).

11- Adabul Salat (Fikhul Aklak).

12- Sharhu Hadis Ra’as Jalut (Kalam wal Falsafa).

13- Sharhu Hadis Junud Akli wal Jahli.

14- Kashaful Asrar(littafi ne kan siyasa raddi kan wani littafi da ya taba mutuncin addini.

15-Nailul Audari fi Bayani Ka’idati La darara wa La dirara (Usulil Fikhu Istidlali.

16- Hukumat Islami.

17- Mubaraze ba Nafsi.

18-Hashiyatu ala Miftahul Gaibi (Falsafa wal Irfan)

19-Tahzibul Usul (Takriratul fil Usul tareda Alkalamin Samahatus Shaik Jafar Subhani mujalladi uku.

20- Risala fil Ijtihad Wat taklid(Fikhul Istidlali)

21-Tafsir Suratul Hamdi wal Alak.

22-Manasilul Hajji.

23-Tuzihul Masa’il (cikin harshen farisanci)

24-Takriratul Ayatullahi Al’uzma Assayid Burujardi, Usulil Fikhi.

25-Hashiya ala Asfar (Falsafa)

26-Diwanul Shi’iri.

27- Ta’alikat wa Hawashi ala Kitabil Irsi wallafar Alhaji Mulla Hashim Kurasani.

28- wata Risala da ta tattaro fa’idoi da warware matsalolin ilimi.

29-Zubdatul Ahkam (takaitacciyar Risalar Taklidi).

3- an tattaro wasu bayanansa da hudubinsa da sanarwarwowinsa da taken Sahifatul Nuru cikin mujalladi 20.

Rayuwarsa a siyasance: tun tasowarsa ya kasance dauke da ruhin yakar zalunci da Azzalumai da `yan mulkin mallaka, ya kalubalanci Sarki Sha karan farautar Birtaniya, ya sadaukar dukkanin karfinsa cikin tafarkin samar da `yanci da adalci da cion gashin kan kasa da yanke hannayen Azzalumai daga madafan iko wadanda suka yada barna a ban kasa, suka yi barna cikin dukiyar al'umma suka ci suka kwasa yand aransu yake so, Assayis Komaini ya kasance a tsahon rayuwarsa yana cikin sa'ayi don daukaka Kalmar muslunci ya tsaya kyam kamar babban dutse babu wata guguwa ko iska da take motsa shi, bai ta gajiya ba ko raunana cikin abinda yayi imani da shi daga gaskiya sai ya tashi tsaye yayi gwagwarmaya domin neman yardar Allah don ceton raunana wadanda ake zalunta a cikin duniya baki daya, domin ya share fage ga bayyanar Adalci cikin duniya da kuma hukumar Sahibuz Zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja.

Hakika yunkurinsa ya doru kan wadannan nukdodin da zasu zo:

1-zaman lafiya kasa da kubutarsa daga zaluncin Azzalumai da ta'addancinsu.

2-kare cin gashin kan kasa da katse hannayen baki barai da karnukan farautan `yan mulkin mallaka cikin yankin gabas ta tsakiya da cikin kasar Iran

3-tarbiyantar mutane da tsarkake su da koyar da su muslunci muhammadi na asali.

4-girgiza karagun mulkin Dawagitan Iran da kakkabe mulkin Jabbeari a baki dayan duniya.

5-hada kawuka da sahu da Kalma tsakankanin musulmai don kishiyantar makiya muslunci.

6-tona asiri da bayyanar makirce-makircen mulkin mallaka da girman kan duniya da ya bayyana cikin Sahayoniya da gurguzanci da jari hujja.

7-shiryar da mutane  zuwa gaskiya da kara karfafa dangantaka da alakoki tsakankaninsu da malaman addini da ma'abota ilimi da Maraji'an addini.

8-samar da sabun fasali ga hukuma da ta doru kan turbar Wilayatul Fakihi.

9-wurgi da zalunci da Azzalumai da kishiyantarsu da yakarsu da makamai.

10- kin yarda da sassauci da sulhu tareda makiya addinin muslunci.

 

Hakika Assayidul Komaini ya ga mulkin shugaba Azzalumi na iko da kasar da aka haiafe shi yana halasta abubuwan da Allah ya haramta, yana tauye alkawari yana sabawa sunnar Manzon Allah (s.a.w) yana aiki da zaluncin da sabo kan bayin Allah, sai Imam ya tashi ya kalubalance shi da magana da aiki cikin babban juyin juya halin muslunci da ya haskaka `yan gwagwarmaya hanyarsu, ya farkar da musulmai ya ankarar da su larurar komawa ga littafin Allah mai girma da hukuncinsa a doran kasa.

Hakika Assayidul Komaini ya tsaya kyam cikin sauke nauyin da yake wuyansa na umarni da kyakkyawa da hani da munkari, ya nade marhalolinsa ta hanyar nasiha da nusantarwa da wa'azi da tabligi wanda sune matakai na farko cikin umarni da kyakkyawa da hani da munkari, sannan yayi gargadi hukuma ya yiwa  Sarki Sha jan kunne da ya bar zaluncin da dagawarsa, hakan ya faru ne ta hanyar hudubobinsa na hamasa da bayanai masu zafi, daga karshe Imam ya mike kan gwagwarmaya da ta kai ga hambarar da gwamnatin Sarki Sha karan farautar `yan mulkin mallaka maha'inta ya take Amerika ya katse hannuwan Barai baki masu yada barna.

Sakamakon haka ne ya zama lazim ga duk wanda yake son bin irin wannan tsari da hanya da ya karanta rayuwar Imam Komaini a siyasance tareda zurfafa bincike da dandakewa domin ya samu damar kwasar ruhin gwagwarmaya da da tsayuwa kyam, domin tafiyarsa ta kasance alama tuta mai haskaka da `yan gwagwarmayar tabbatar da ni zasu haskaka da ita cikin `yantar da al’umma daga faratan jahilci da talauci da cibiya da cibaya da mulkin mallaka, cikin rigar gwagwarmayar muslunci kan yakar dagutanci da zalunci da fasadi, kan wannan ne ya zama lazimi dan gwagwarmaya ya dibi darussa daga rayuwar Imam Komaini ga ma’anar yunkuri da jihadi cikin mafi daukakar marhalolinsa da mafi girmamar ma’anoni.

 

Daga cikin zantukan manyan mutane kan Assayidul Imam

1-      Ayatullahi Burajardi- samuwar Assayidul Imam ta sanyaya idanun Hauza ya tsere tsaraikunsa.

2-      Ayatullahi Shaik Taki Amuli-mukaman ilimi da aiki ga Ayatullahi Assayid Komaini basu buy aba da har zasu bukatu zuwa ga bayaninsu, lallai na san shi daga na farko-farkon Mujtahidai da Mraji’an Taklidi.

3-      Bakon da ya sauka cikin gidanku ya daga manyan Maraji’ai kuma babban samfuri cikin ilimi da tak’wa.

4-      Fitaccen mutum da ya amsa kiran ubangijinsa da babban jihadinsa da sadaukarwarsa  da jagorancinsa da yake cike da hikima d araya muslunci a wannan zamani, ya isar da kiran tauhidi ya zuwa dukkanin kusurwowin duniya , da dawo wa musulmai girmansu da ua subuce musu.ya girgiza zukatan masu girman kai da karfin duniya…shi Fakihi ne kuma Marja’in Taklidi ya koma ga ubangijinsa, hakika ya kasance daga ayoyin Allah cikin zuhudu da ibada da raya dare da tsoran Allah da fadar gaskiya da nemanta yana da wasu siffofin da sha banban da sauran mutane, inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Daga abinda Ayatullahi Assayid Ustaz Muhammad Rida Gulfaigani kan ta’aziyar rasuwar Assayidul Komaini.

5-      Ayatullahi Uzma Assayid Mar’ashi Najafi- Assayidul Komaini ya kasance daga Maraji’an duniyar shi’anci kuma jigo daga jiga-jigan malaman muslunci ababen alfahari.

6-      Wannan mutumin ma’ana Assayidul Komaini babban mutum ne yana da tsarkaka zuciya da badini, a bayyane cewa yana kan kyawawan dabi’u, tun da muka san shi tun gabanin shekaru hamsin babu abinda muka gani daga gareshi fae tsoran Allah da riko da addini da kyauta da jarumta da daukakar himma da fadin kirji da tsananin kwadayi cikin ilimi da madaukakan mukamai, lallai mutum mai tsoran Allah da dukkanin ma’anar tsoran Allah , mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga muslunci ya tsaya kyam a gaban kafircin duniya hannun gaibu ya tallafa masa da yanayi da yake gigita hankula, babu wata kusurwa daga kusurwowin Kasar Iran babu wani gid adaga gidaje face sun daga sautinsu suna masu fadin (mutuwa ga Sarki Sha) lallai shi ya sadaukar da ransa domin daukaka addinin muslunci, ya kasance yana neman shahada, Allah ya bashi karfi da samun irinsa ya karanta, ya kuma taimake shi irin taimakon Shugaban Manzanni da irin nasarar A’imma tsarkaka da Sahibul Amri Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja, bayani daga bakin Ayatullahi Al’uzma Shaik Muhammad Ali Araki.

7-      Assayidul Komaini task ace ga shi’anci. Bayanin Ayatullahi Mujahid Abdul Husaini Amini.

8-      Mutum daya rak tilo da muke fatan zai amfanar da Iran bayana shi ne Assayidul Komaini. Bayanin Ayatullahi Assayid Abu Kasim Kashani.

9-      Imam ya tattara ilimi da aiki da fifita wani a kansa da jihadi, a wannan duniya da zalunci yake mata jagoranci da bautawa sha’awe-sha’awe ya iya jagoranci da iklasi da daukaka Kalmar muslunci cikin duniya baki daya. Bayanin Ayatullahi Al’uzma Mirza Hashim Amuli lokacin rasuwar Assayidul Komaini.

Tura tambaya