lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mai ceton baki dayan al’umma Al’imamul Muntazar

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hadafi da manufa kan sanin Imam

Ka sani cewa hadafin kan sanin wane ne Imam (as) bawai shine kadai ka san hakikar sa ta kankin kansa da nasabarsa da imamancin sa da tarihin yanda ya rayu, bari dai dole ne ka san ma’ana da hadafin imamancinsa, ka san ismarsa ta zati da iliminsa da ya shawo daga wurin ubangiji da alakar sa da sama da kasantuwar sa hujja kan sauarn halittu, sai ya zama dabi’ance a halitance da shari’ance ka san imamancina, da yake baiwa shari’a kariya, kamar yanda ya kamata ace ka san jagorancin sa kan siyasa da zamantakewa, da tsinkaya kan wilayar sa ta halitta da ta shari’a, kamar yanda ya kamata ka san yaya ilimin sa ladunni da na ishara na kwankwasar kunnuwa da sanya haske cikin zukata yake kamar yanda ya zo cikin madaukakan hadisai, duk wanda bai san Imamin zamanin sa ba da wannan sani na yayewa da kyawunta da kamala to sanin sa tauyayye ne nasasshe ne, ba irin sanin da ake dan shi’a ya kasance tareda shi ba ne, idan da farko kana so ka kasance rayayye, rayuwarka ta kasance rayuwa kan tsarin hankali da mutumtaka to da farko ya zama dole ka fara sanin waye Imamin zamanin ka, ka san shi sani na wilaya da hujjantakar sa kan halittu, ka san ma’asumancin sata zati da ilimin sa ladunni wanda kai tsaye ya danganta shi da sama, sannan ba buy aba cewa Ma’sumai goma sha hudu ne (as) na farko manzon Allah (s.a.w) Ali Almurtada (as) shugabar matan duk duniya Fatima Zahara (as) da Imamai goma sha daya daga `ya`yan Ali da Fatima (as) lallai nauyaya biyu littafin Allah da tsarkakakken tsaro, lallai su biyun ba za su taba rabuwa tun da farko har zuwa karshe duniya da lahira, duk abinda yake kunshe cikin kur’ani yana tattare da su, duk abinda yake tattare d asu yana cikin kur’ani, abinda yake shiryarwa zuwa ga kur’ani da shiryarwa dari bisa dari yana shiryarwa zuwa garesu, duk abinda yake shiryarwa da shiryarwa ta lazimta ma haka, sakamakon kasatuwarsu suna tafiya kafada da kafada da juna kuma har abada ba zasu rabu cikin wani abu, wanda bai san Imaminsa idan ya mutu to ya mutu mutuwar jahiliya, haka ma wanda bai san kur’ani ba idan ya mutu ya mutu mutuwar jahiliya, ba a nufin sanin kur’ani da ma’anar sanin kalmominsa kamar yanda yake cikin tafsirai, da kuma cewa shi littafi ne daga sama da ya sauka a daren lailatul kadri, da ya kunshi surori 114 da ayoyi 6000 da da kaza da kaza ko kuma ace mutum ya haddace juzu’I kaza ko kuma dukkanin kur’anin, duk da cewa ana bukatar haka kuma hakan abin yabawa nem sai dai cewa hadafi da manufa daga sanin kur’ani mai girma shine ya sabn wahayi da abinda yake bayansa daga manufofi da haduffa tsarkakku, ya kuma san cewa shi sako ne daga sama ya san wanda aka aiko da sakon da aka aiko shi da shi, duk wanda bai san kur’ani da wannan fuska idna ya mutu to ya mutu mutuwar jahiliya, idan kur’ani sanin sa sun kasance sababin rayuwar mutum da hankaltuwarsa, to haka zalika samuwa da sanin Sahibul Asri (Af) wannan kammalallen mutumi kur’ani na mai Magana, wanda yake tajalli cikin sunan Allah mafi girma, hujjar Allah kan halittunsa, albarkacinsa ake azurta halittum da samuwar sa ne kasa da sama suka tabbatu, kur’ani da abokin tarayyarsa Sahibul Zaman sun kasance sababi tsiran al’umma da rayuwarsu ta hankali, da kubutar su daga zalunci da dagawa da fasadi da bautar wanin Allah matsarkaki da kubuta daga jahilci rashin sani, dana aiki, hakan zai kasance da jihadi da dukkanin nau’ukansa daga Jihadul Asgar da Akbar da Ausad, yayin da Allah ta’ala yake cewa:

 

﴿هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَى تِجَارَةٍ لن تبور﴾.،

 

Shin in shiryar daku zuwa ga kasuwar da bata tasgaro.

 

Lallai shi yana duba zuwa ga wannan jihadi ne da dukkanin ma’anonin sa da masadik.

 

﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ﴾

 

Yaku wadanda sukai Imani kuji tsoran Allah ku nemi tsani zuwa gareshi ku yi jihadi cikin tafarkinsa tsammaninku ku rabauta.

 

Wanene Muntazar na hakika?

Babu shakka mafi falalar ayyuka shine jiran ranar bayyanar sa, da jiran ranar da akai alkawarin bayyanar Mahadi Muntazar (Af) domin ya zo ya cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya, sai dai cewa wane ne wanda ake jira na hakika, wanne irin jira ne ake bukata daga garemu, hakika cikin mutane akwai wanda ya kasance abin jira na jeka na yika, akwai kuma wanda yake jiran nasa bai da amfani.

Muna cewa: Muntazar na hakika shine wanda yake ceto dav tseratar da sauran mutane, shi kamar misalin haske ne bayyananne da yake bayyana kansa yake kuma bayyanar da waninsa, hakika bayanin siffofin sa ya zo filla-filla cikin jumlar riwayoyi ingantattu, kamar yanda bayanin su ya zo a dunkule cikin kur’ani mai girma, hakika Allah yayi bayanin sa da cewa yana daga cikin mujahidai da masu hijira zuwa ga Allah da manzonsa, mai Imani da Allah da ranar kiyama da gsikya, yana tsayar da sallah da bada zakka da kumusi da sauke nauyin azumi da sauransu daga siffofin ilimi da aiki, sannan matanin asalin wannan bayani da rassansa tana dunkulewa cikin wanda ya kai ga hadafi daga manufofinsa da sirarsa, yana ganin sa cikin manufa, kamar yanda ya zo cikin fadinsa ta’ala: (ga mutanen da suke sani) da kuma (ga mutanen da suke hankalta) ai sun cimma makarkarar ilimi da hankali suna ganin hadafi shine Allah matsarkaki cikin hadafin ilimi da hankali, lallai yana daga cikin abu mai wahala mai ilimi da mai hankali su cimma hadafi suka hadafinsu cikin abinda suka nufa, lallai ba dukkanin mai ilimi bane ko mia hankali ke iya cimma hadafinsa bay a tsinkayi inda ya nufa cikin hadafinsa, bari da yawa daga cikinsu zaka samu wand ayake kan hanyar hadafinsa, kuma idan ya mutu ya mutu shahidi, Allah bai fadi cewa ma’abota hankali da ilimi suna cimma hadafinsu ba cikin inda suka nufa, bari ya kira su da mutane ma’abota hankali da mutane masu ilimi, wannan kaumiya tasu ba kaumiya ce da take danganewa da nasaba ko mukami ba, kamar sauran mutane da kabilu, bari dai tana daga tsayu kan wani abu, su basu kebantu da wani bigire ko wani zamani ba da ake ishara ya zuwa gareshi, su basu daga mutanen Larabawa ko Ajamawa ba, lallai abinda ya zo daga kur’ani da sigar (ga mutanen da suke hankalta) da kuma (ga mutanen da suke sani) da (ga mutane n da suke zurfafa tunani) da (ga mutanen d asuke Imani) abinda ake nufi daga garesu sune mazaje da mataye wadanda suke daga rayayyu ba matattu b, kuma sun kai ga hadafinsu da inda suka nufa, sun tsayu kan hankali da ilimi da Imani da tunani, bawai malamai ma’abota hankali muminai kadai ba. Banbanci nawa tsakanin wand aya ke sallah da kuma wanda yake tsayuwa kan sallah, kamar yanda ya zo cikin fadinsa ta’ala: (wadanda idan muka basu dama a doran kasa sai su tsayar da sallah) sune wadanda suke gaje kasar daga bayin Allah Salihai, banbanci nawa ne tsakanin masani da kuma aiki da ilimi da tsayuwa kansa, banbanci nawa ne tsakanin mai daidaito adalai da kuma mai tsayuwa kan adalci da daidaito, da dai misalin wadannan mahallai cikin siffofi da falaloli.

 

Cikin fadar mai kawo gyara a baki dayan duniya:

Babu kokwanto kan cewa Sahibul-Amri shine wanda zai kawo gyara a baki dayan duniya ya kuma cikata da daidato da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya, saboda shine Ka’im mai tsayuwa kan adalci da hankali da Imani a karshen zamani, bai wadatarwa ga mai kawo gyara ya isu da kasantuwarsa adali masani ma’abocin hankali mumini kadai ba, bari dai dole ne ya tsayu ya tashi kan hankali da ilimi da adalci, kamar gini, lallai shi magini a wani lokacin na kasantuwa maginin gida, a wano karon kuma na kasancewa mai tsayuwa kan ginin gida kamar misalin injiniyan gini, duk wanda mai tsaya kan hankali da adalci da ilimi ba lallai ba zai iya warware matsaltsalolin sa b, hakama bazai iya warware matsalolin al’umma ba da jama’ar da yake rayuwa cikinsu ba, bazai iya kawar musu da nauye-nauye da sasaran da suke wuyansu ba,

 

﴿وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالأَغْلالَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ﴾

 

Ya dauke nauyinsu daga barinsu da sasarin da ya kasance kansu.

 

Kadai da yana aikata haka da kudura da iko da karfin Allah wanda ya kasance yana tsayuwa da hankali da ilimi da daidaito da adalci, wannan shine abinda muke samu cikin Sahibuz- Zaman (Af) lallai shine Ka’im da yake tsayuwa da hankali da ilimi, kamar yanda ya zo cikin hadisai za ai kari kan hankulan mutane da daya cikin arba’in, lallai waliyin Allah zai shafa shafa hankulan mutane a wannan lokaci, kamar yanda Hujjatu bn Hassan (as) ya kasance mai tsayuwa da yake tsayuw ada hankali da adalci da daidaito haka zalika yana tsayuwa da tauhidi tsantsa da annbta da Imani da ma’ad

Lallai shi Allah ya gaggauta bayyanarsa zai farkar da duniya da al’umma da jama’ar mutane da Imani daga barci ya dawo musu da kyakkyawar rayuwa,duk wanda ya kasance cikin halin barci lallai zai farkar da shi domin ya tsayu da adalci

 

. ﴿وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ﴾

 

Da mizani domin mutane su tsayu kan daidaito.

 

Wannan ita samfurin Allah cikin sammai tun lokacin halittar Adam (as) kamar yanda itace hadafin annabta wanda ya gaza tabbatuwa, kadai Allah matsarkaki yayi alkawrin tabbatar da ita a hakika cikin zamanin bayyanar Ka’im, jama’a rayayyu masu hankali masana masu gwagarmaya da sannu zasu kasance masu masu rabautattu da rayayyu, za a bautawa Allah shi kadai ba tareda yi masa shiraka ba, wasu bangare ba zasu bautar da wasu bangare ba, bari dai shi zai kira zuwa ga bautawa Allah da yi masa `da’a tsantsa, ya zuwa tsayar da sallah da zai kasance mai karakta bakomai Gadara da barna da zalunci , bazai saurari wargi baba zai bada dama ga fasadi ba da ahalinsa ba , Allah matsarkakin sarki yana cewa:

 

﴿الَّذِينَ إِنْ مَكَّنَّاهُمْ فِي الأَرْضِ أَقَامُوا الصَّلاةَ وَآتَوْا الزَّكَاةَ وَأَمَرُوا بِالْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا عَنْ الْمُنْكَرِ وَلِلَّهِ عَاقِبَةُ الأُمُورِ﴾. ﴿وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِي الزَّبُورِ مِنْ بَعْدِ الذِّكْرِ أَنَّ الأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِي الصَّالِحُونَ﴾.﴿وَنُرِيدُ أَنْ نَمُنَّ عَلَى الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا فِي الأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَنَجْعَلَهُمْ الْوَارِثِينَ﴾

 

Wadanda idan muka basu dama a ban kasa sai tsayar da sallah su bada zakka su yi umarni da kyakkyawa su yi hani da mummuna ga Allah makomar al’amura take.

Hakika mun rubuta cikin Zabura bayan Ambato lallai bayina nagargaru su ne zasu gaji kasa.

Kuma muna son muyi falala kan wadanda aka raunana mu sanya su jagorori mu sanya su magada.

 

Al’amari a wannan lokaci za kasance da yanani mai tsanani ta yanda bai wadatarwa ga mutum gay a isu da iya kasantuwarsa adali da daidato, bari dai wajibi ya kasance mai tsayuwa da adalci

﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ بِالْقِسْطِ﴾

 

yaku wadanda sukai Imani ku kasance masu tsayuw akan adalci.

 

Masu tsayuwa kan hankali da ilimi da Imani, misalin wadannan al’umma kjo da sun kasance tsiraru sai dai cewa gyaran duniya da shirayra da ita bazai yi musu wahala ba.

 

Tura tambaya