lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya

Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin kai

Gabatarwa

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Mai shiryarwa ya zuwa hanyar daidai, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi darajar baki dayan Halittun Allah ta'ala Muhammad da Alayensa tsarkaka, madawwamiya la'ana ta tabbata kan baki dayan Makiyansu tun daga farkon halitta har zuwa ranar lahira.

Bayan haka: wadannan wasu `yan makalolin muslunci ne da suka ginu kan abubuwan da suka faru a tarihi da kuma ingantattun Akidu da na rubuta su cikin (Mujallar Sautul Kazimaini) wacce take fitowa daga Mu'assasar Tablig wal Irshad, Allah ya yarda ta wanzu ya kuma kareta da rugujewa, ya kuma cigaba da yassare damar buga wannan mujalla cikin sabon tsari na zamani mai kayatarwa.

Ina burin kara wasu sababbin abubuwa ciki, in harba kibiyar gaskiya daga haskakakken Kwari da Bakan tabbatattun abubuwa da tsarkiyar ilimi na gaskiya, don duniyar muslunci ta yi farin ciki da ganin karshen gubar Wahabiyanci da ma'abota bidi'a da bata, lallai faruwar hakan bai gagari Allah ba, lallai ita karya tana da iya lokacin kewayenta ita ko gaskiya itace mai wanzuwa da dawwama, da sannu ranar tabbatuwar gaskiya da gushewar karya zata zo:

 (جاءَ الحَقُّ وَزَهَقَ الباطِلُ إنَّ الباطِلَ كانَ زَهوقآ).

Gaskiya ta zo karya ta gushe lallai ita karya ta kasance mai gushewa.

Ashe Asubahi ba kusa-kusa take ba?!

Na kasance ina begen cancandawa takardun rayuwata ado da jihadi da ruwan Tawada da Takubban Alkaluma, rayuwa ba wani abu bace face shu'uri da take, Akida da jihadi, me yafi kyawu daga jihadi cikin tafarkin Allah domin daukaka Kalmar gaskiya da rusa Kalmar karya, sai dai cewa ayyukan Hauza ilmiyya daga koyarwa da talifi da sauran ayyukan alheri na zamantakewa da hidimtawa mutane suna hana mutum abin da yake son yi yake begen tabbatar da shi.

ما كلّ ما يتمنّى المرء يدركه         تجري الرياح بما لا تشتهي السَّفَن

Ba dukkanin abin da mutum yake buri yake iya cimmasa ba* hakika iska tana kadawa da abin da Jiragen ruwa basu kauna basa so.

Ina rokon Allah matsarkakin Sarki da ya gyara kura-kuraina ya sanya daidai cikin maganata da aikina, ya kuma datar da ni zuwa ga abin da yake so yake yarda shi cikin hidimar muslunci da mazhabar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu.

Ina saran zamani ya bani faraga da dama domin kara daura damara da zage dantse da yin jihadi a karo na biyu domin in bayyana karya da gurbatar Akidun Wahabiyawa da kage-kagensu kan dukkanin musulmi da kuma karyarsu da sharrance-sharrancensu kan `yan shi'a a kebance.

Da Allah na dogara da Manzonsa da tsatso masu tsarki nake kamun kafa, sannan ina da fata da sarai a nan gaba.

Bawan Allah Adil-Alawi


Tura tambaya