lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Hasken sasanni cikin sanin arzuka

 

Allah mai yawan azurtawa ne kuma shi ma’abocin karfaffen karfin ne ya umarce mu daga ludufin sa da mu roke shi mu nema daga gare shi, abin ban mamaki daga hakan shi ne cewa shi ubangiji bai damuwa da bawa ba don addu’ar da yake yi ba da nema daga gare shi, hakan yana kasantuwa daga mukamin bauta da kaskantar da kai ta yiwu ma cikin mukamin shagwaba, lallai yanda lamarin yake a wani lokaci bawa yana kaskantar da kansa cikin fagen girman ubangijinsa mabuwayi, wanoi lokacin lokacin kuma ya kanyi shagwaba sakamakon kusancinsa kansa daga failolinsa matsarkaka, shi bawa yana tsakankanin kaskantar da kai da shagwaba, hakikar bauta shine yankewa zuwa ga Allah wannan shi ne ma’anar addu’a da gundarinta, dukkanin wanda yake yankewa zuwa ga ubangijinsa baya ganin kowacce irin samuwa ga kansa, bari dais hi yana ganin hakikanin talauci cikin kansa da cewa shi lallai bai ikon cutarwa ko amfanarwa ko rayuwa ko tashi ba ga kansa, ita addu’a itace bargon ibada kuma itace makamin annabawa da muminai, itace mabudin dukkanin gyara da gyaruwa, lallai addu’a tana yanke bala’in da bashi da makawa daga afkuwa  tana kuma saukar da arziki da saukaka samunsa  da kara yalwarsa  da dawwamar da albarkars, daga nan ne muka samu Kur’ani mai girma da sunnar annabi  dakuma cikin makarantar Ahlil-baiti wani mai da hankali da karkata kebantatta kan addu’a da fuska mai gamewa, da kuma karkata kan arziki da kebantacciyar fuska da sura, hakika annabawa da wasiyyai da waliyan da wadanda sukai Imani da Allah girmansa ya girmama zaka samu basa gajiya ko kosawa daga yin addu’a da neman arziki.

Cikin kamus din muslunci a janibin addu’o’i da wuridai da Azkaru akwai wani yanki cikakke da yake bijira da bayani kan neman arziki da dukkanin nau’ukansa da sinfofinsa da masadik dinsa, sai dai cewa ba dukkanin neman karuwa bane yake iya zama arziki, domin sau da yawa zaka samu mutum ya nemi dukiya mai tarin yawa da za ta zamanto ta cutar da shi domin kasantuwar ta sababin dagawarsa:

       (لَيَطْغى * أَنْ رَآهُ اسْتَغْنى )

 Tabbas yana dagawa * sakamakon ganin cewa shi ya wadata.

 

Saboda haka babu alheri cikin misalin wannan karuwa da dukiya, bari dai kamata yayi muminai su nemi Karin da dadin arziki na halaliya tsarkakakke mai albarka mai alfanu, ma’ana tabbatacce madawwami, ya zo cikin addu’a

(اللّهمّ زد وبارک)

Ya Allah ka kara ka sanya albarka cikinsa.

 

Karin ya zamanto cudanye da albarkar Allah, ita albarka tana daga tajallin sunan Allah mai albarka girmansa ya girmama.

Sannan bai buya ba cewa addu’o’i da sallolin arziki suna da tarin yawa, da ace mun samu damar tattaro da sun kai ga mujalladodin litattafai, sai dai cewa zamu wadatu da ambaton jumla daga cikinsu don zama samfuri domin ya kasance makullin alheri ga ma’abota addu’a, ya zamanto sun roki Allah da su ko da kuwa sau daya ne yayin nazarin littafin, me ya sanar da kai ta yiwu ba’arin muminai maza da mata su dauki ba’arinsa domin ya kasance addu’arsu cikin alkunut dinsu cikin sallolin su, ko kuma ya kasance addu’o’in bayan idar sallolin wajibi, sai ubangijinmu mai karamci mai yawan kyauta ya kasance tareda mu cikin ladansa, abinda na rubuta ya kasance daga ilimi mai amfanarwa da izinin Allah bayan mutuwa ta ya kuma amfanar da ni cikin kabarina da barzahuna  da ranar tashina daga kabari ranar da dukiya da `ya`ya basu amfanarwa face wanda ya jewa Allah da lafiyayyar zuckiya, karshen zancenmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai

Tura tambaya