lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

HIKAYAR KARE DA MAI GIDANSA

 

An hakaito cewa a wata rana a wani zamani an yi wani mutum da yake sana’ar saro itace daga jeji da yake rayuwa a cikin wata `yar karamar bukka ciki daya daga cikin dazuzzuka , ya kasance yana rayuwa tareda dansa karami da wani Kare nasa mai kiyaye amana, wannan mai saran itace ya kasance a kowacce rana a lokacin hudar rana ya kan fita ya je daji domin saro itace ya tattaro ya daure bay a dawo wa gida sai dab da faduwar rana ya bar wannan da na sa karami cikin kulawar Allah Azza wa Jalla da gadin wannan Karen da yake da rikon amana wanda ya aminta da shi, wannan Kare a ko da yaushe ya kasance yana bada kariya ga wannan yaro karami da kuma mai gidansa da yake sana’ar saro itace, a wata rana a lokacin da wannan mutumi yake dawo wa daga aiki cikin wani yini mai tsayi da yake cike da wahala sai ya ji haushin wannan Kare yana tahowa daga nesa sabanin yanda ya saba da al’adantuwa a kai, wannan haushi sai kara dagawa da karfi yake yi hakan ya sanya shi shiga cikin damuwa da tunanin ko wani abu ne ya faru , sai yayi gaggawa zuwa wannan bukka yayin da ya je kusa da bukkar sai ya ga wannan kare yana gudu yana fuskanto shi yana haushi ga fuskarsa ta jike da jini , take sai wannan mutum ya fadi sumamme yana tsammanin wannan Kare ya ci amanarsa ya cine masa dansa karami yana farkawa sai ya dauki gatarinsa ba tareda tsayawa ya yi tunani da bincike ba, sai ya tunkari wannan Kare ya farmasa da sara yana dukan tsakanin idanuwansa har sai da wannan kare ya fadi kasa wanwar.

Wannan mutumi ya dinga rusa kuka cikin bakin ciki kan rashin dansa karami , daga bayan sai ya shiga wannan bukka sai ya zauna yana cizon yatsunsa sabida nadamar abin da ya aikata ta yanda da shigar sa sai ya ga yaron wasa a kan gadon sa cikin kwanciyar hankali da aminci sannan kusa da wannan yaro ga gawar wani katon maciji jike da jini , sai ya fahimci cewa wannan Kare ya Kare fuskarsa ta jike da jini sakamakon dauki ba dadi da yayi da wannan katon maciji da yayi yunkurin halaka wannan yaro, sai idanuwansa suka cika da hawaye bakin cikin sa ya tsananta kan kashe wannan Kare nasa `dan amana wanda ya kasance yana haushi saoda farin cikin tseratar da yaron da yayi yana mai jiran uban gidan sa ya zo ya yaba masa, sai dai cewa abin ban takaici maimakon sabun yabo sai ya halaka ce ta zama sakamakon sa. 

Tura tambaya