lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MUTUMIN DA YA NEMI TAIMAKO

Daidai lokacin da yake bude hutunan rayuwar da yayi a zamanin da shige ya shude yana kuma tuna kwanakin ya barzu a bayansa, kamar misalin kwanakin bai kasance yana iya samarwa da kansa da matarsa da yayansa abincin da zasu ci a yini ba, a cikin wannan hali sai ya fara jin karar murya daga wani mai kwankwasa kofa yayi ta jin wannan kara har sau uku lamarin da ya tasar da fata da sa rai da ya ceci rayuwarsa daga kangin talauci, bayan da matarsa ta ga cewa talaucin ya kai iyaka ya kure ya kai makura sai bashi shawara da ya je wajen Annabi (s.a.w) ya bayyana masa halin da yake ciki ya nemi taimako daga gareshi, da jin haka sai ya wanke kafafunsa ya tafi wurin Annabi (s.a.w) domin ya bashi labarin halin matsanancin talaucin da yake ciki da kuma shawarar da matarsa ta bashi na neman taimako daga gareshi, sai ya ji bayani daga Annabi (s.a.w) da cewa duk wanda ya tambaye mu zamu bashi, kuma duk wanda wadatu bai roko ba Allah zai wadata shi, sai ya juyo ya dawo gida  cikin tozartar fata cikin matsanancin talauci, sakamakon tsananin talauci sai ya zama dole gareshi ya kara komawa wurin Annabi (s.a.w) domin neman taimako, kwatsam sai ga sautin Magana ya kara ji: duk wanda ya roke mu zamu bashi duk wanda ya wadatu Allah zai wadata shi, sai ya ki tambaya ya kara dawo gida ba tareda ya bayyanar da buktarsa ba, sai dai cewa sakamakon damkar talauci ya samu kansa cikin yanayi rashin mafita da matserata, sai ya mike ya nufi Annabi (s.a.w) a karo na uku sai dai ya kara jin maganar manzon Allah (s.a.w) har sai da zuciya ta cika da sa rai da nutsuwa da yakini sakamakon ya samu yakini kan cewa makullin matsalarsa yana hannunsa, sai ya fito yana tafiya yana cikin yakini, cikin ransa yana fadin b azan kara tunanin neman taimako daga kowa ba, zan dogara da Allah shine mai isar mini, zan kuma nemi taimako daga abinda Allah ya bani daga karfina, babu inda dacewa ta take sai da Allah, daidai lokacin da ya nutse cikin tunani, sai ya fara tunani cewa to yanzu wanne aiki ne zan iya yi

Kwatsam sai wani tunani ya fado msa da cewa ya tafi sahara ya tattaro itace da kirare, sai ya karbi aron gatari ya dauki hanya ya tafi zuwa sahara, sai ya saro kirare ya dauko ya taho da su zuwa cikin gari, yaje ya sayar, ya dandani dadin wahalar da ya sha, sai ya cigaba da saro itace  har ta kai gay a iya sayen taguwa da bayi guda biyu da dukkanin kayan aikin da yake bukatuwa da su cikin sana’arsa, kwatsam sai gashi ya zama mai kudi, wata rana sai ya hadu da Annabi (s.a.w) ya bashi labarin dukkanin abinda ya faru da yarda ya zo wurinsa don neman taimako, sai Annabi (s.a.w) yayi mursmushi yace: tabbas ina iya tuna sanda na fadi haka nace) duk wanda ya tambaye mu zamu bashi duk wanda ya wadata Allah zai wadata shi.

Wannan kissa ta zo cikin littafin Usulul Kafi juz na biyu shafi na 139

Tura tambaya