lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Imam Hadi (a.s) tareda Makarantun Kalam (Tauhid)

A zamanin Imam Hadi (a.s) an samu yawaitar makarantun Akidu misalin Mu'utazilawa, Asha'ira sun kasance suna yada ra'ayoyinsu da fahimtarsu tsakankanin al'ummar musulmi, kasuwar bahasosin Jabar da Tafwizi da bahasin yiwuwar ganin ubangiji da rashin yiwuwar hakan sun kashe cikin tashensu , hakika Imam Hadi (a.s) ya bada gudummawa mai girma cikin amsa shubuhohi da martani kan wadannan ra'ayoyi ya zage dantse matuka kan yakar miyagun Akidu misalin Jabariyanci ta hanyoyi daban-daban domin taka burnin yaduwar wadadannan Akidu tsakankanin shi'a, ya bakin kokarinsa cikin kare ingantacciyar akidar muslunci daga karkacewa wannan faftuki da gwagwarmaya na daya daga cikin sanannun dabi'un wannan babban Imam amincin Allah ya tabbata a gareshi.

Bincike kan rayuwar ilimi ta Imam Hadi (a.s) na nuna cewa akasiin munazarorinsa sun kasance kan batun tauhidi da akida, riwayoyi masu tarin yawa da aka nakalto daga gareshi sun bada gudummawa ne cikin gina maginan akidun shi'a a bayyane hakan yake, alal misali zamu iya daukar wasikar Almufaddal Ibn Umar cikin amsa ga tambayoyin mutanen Ahwaz zuwa ga Imam (a.s).

Dangane da maudu'in Jabaranci da Tafwizi cikin wannan wasika yayi bayani da bada amsa mai gamsarwa da yankakken dalili, ya bayyana ingantacciyar fahimta tsaka-tsaki it aba jabaranci b aba kuma tafwizanci ba.


Tura tambaya