lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 14 GA WATAN SAFAR CIKIN MAS’ALAR BAYYANA KARATU DA BOYESHI CIKIN SALLOLI

Darussan Hauza Ilimiya

Cigaban kan darasin da ya gabata a 13 ga watan Safar

Mahalli Qum mai tsarki Muntada Jabalul Amil yareda-Samahatus Ustaz Assayid Adil-Alawi (H)

Cigaba kan bahasin da ya gabata cikin mas’alar bayyana karatun sallah da boye shi cikin sallolin farilla na kowacce rana sannan cikin sallar Juma’a cikin ranar Juma’a Mashhur din malamai sun tafi kan Shuhura Azima kamar yanda hakan ya zo cikin littafin  Jawahirul Kalam ra’ayin ya kusa kaiwa ga Ijma’i, bari dai bayanin da ya zo karara cikin littafin Algunyatu shine da’awar Ijma’i haka daga Shaik Dusi da zahirin kalaman wasu malaman, wannan Ijma’i ne Mankuli, mawallafin littafin Jawahir yayi da’awar cewa zai yiwu a samu Ijma’i a mas’alar sai ya zamanto anyi ijma’i biyu cikin Mankuli da Muhassali, hanyar da aka same shi: shine cewa bamu samu sabani cikin batun ba, kamar yanda baka hakaito sabani ba cikin in banda bangaren Assayidul Murtada (K) da Ibn Junaidu Al’iskafi (K).

Sabawarsu da tafiyarsu kan cewa bayyanar da karatu cikin sallolin Magariba da Isha’i mustahabbi koma bayan wajibi bai cutarwa, hakan ya tabbatu sakamakon sanin dangantawa garesu, na biyu ba a la’akari da sabawar Ibn Junaidu Al’iskafi da Assayidul Murtada cikin da yawa-yawan mukamomi, na uku: kamar yanda wasu ba’ari daga manyan malamai su kai inkarin zuhurin kalamin Assayidul Murtada cikin abinda aka danganta shi zuwa gareshi daga wannan sabawa da tafiya kan mustahabbanci mai karfi kamar yanda bayani ya gabata, na hudu hakaito Ijma’i daga Shaik Dusi da Abu Makarim Ibn Zuhura yana daga abinda yake shiryarwa kan rashin sabawar Assayid Murtada da Ibn Junaidu tareda girmamar Assayid gurin Shaik Dusi musammam ma wurin Ibn Zuhura da nuna kulawa kan maganarsu su biyun, koma wanne ya kasance lallai sabawar Al’iskafi da Shaik basa bada gudammawa cikin samar da ijma’i da ittifakin Fakihai cikin zamanunnuka sa garuruwa bisa gini kan mafi yawan hanyoyinsa, bisa gini kan tabbatar kulluwar ijma’i cikin da yawan zamanunnuka da suka zo daga bayan zamanin Al’sikafi da Shaik Dusi, har ta kai ga tsayuwa Mazhabar shi’anci da haduwar Kalmar manyan malamansu na fikhu ya zuwa wadannan zamanunnuka na baya, sannan an samu karkata ya zuwa wannan ijma’i daga ba’arin malamai, mawallafin littafin Jawahir ya tafi kan cewa sabani daga ba’arin wasu malamai baya cutarwa tama iya yiwuwa ya kasance daga Ijma’ul Madaraki  wanda ba hujja bane a cikin kankin kansa, sai ka lura.

Duk ma yanda ta kasance jigo dai cikin dalilan Mashhur shine ingantattun riwayoyin Zurara guda biyu daga Bakir amincin Allah ya kara tabbata a gareshi kamar yanda suka gabata, kuma isnadinsu ingantacce ne bai da wata matsala, babu abinda ya rage sai bayanin fuskar kafa dalili da su kan wajabcin bayyanar da karatu cikin sallolin da ake bayyana karatu da boye karatu cikin sallolin da ake boye shi.

Ingantacciyar riwaya ta farko: ta zo da bayani ne cikin wani mutum da ya bayyanar da karatu a wurin da bai kamata ya bayyana ba, ko kuma ya boye shi inda ba a boyewa, sai Imam Amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yace: idna hakan ya kasance bisa ganganci hakika sallarsa ta warware kuma dole yayi sabuwa, idan kuma hakan ya faru ne sakamakon mantuwa da rafkana bai sani ba to babu komai a kansa sallarsa ta cika.

Fuskar dalili: hakika fadinsa (a.s)  (Fakad Nakada) da harafin zadi mai digo a samansa kamar yanda cikin littafan da suke hannu cikin Usul da Furu’a cikin litattafan riwaya da hadisi kamar misalin litattafan Hudu na Hadisi  Alkafi, Alfakihu, Attahzibu, Al’istibsar, da sauran litattafan hadisai na muhammadawa uku: Alwasa’il Biharul-Anwar, Alwafi, na daga abinda yake shiryarwa kan gurbata ma’anar nakada na nufin gurbatar sallah wanda haka yana lazimta bayyanar da karatu, lallai da bai kasance wajibi da barin bayyanawa bai gurbata sallah ba, kamar yanda umarni da sake sallah yake shiryarwa.   
 idan ya karanta (Nakada) da harafin sadun (Fakad Nakasa salatuhu wa alaihi I’ada) kamar yanda wasu ba’arin malamai daga wadanda suka zo a makare suka tsammace shi, lallai zai shirywar kan gurbatar sallah saboda gurbata na daga hukunci nakasa tawaya a hakika.

Sannan yana shiryarwa zuwa gareshi daga karinoni da shaidu abinda ya zo daga bayansa (Alaihi I’ada) na daga abinda ya nuni kan gurbatar sallarsa.

Idan aka ce: lallai cikin hadisin Kalmar (yanbagi) ta zo wacce take nuni ya zuwa mustahabbanci, sai mu bashi amsa da: hakan bay a kore wajabci bayan nufar gwargwadon fuskar da akai tarayya ciki tsakanin wajabci da mustahabbanci, ba da ban hakan ba da misalin Zurara bai kyawunta gareshi yayi tambaya ba, bai kamata a sanya lura ba cikin dalalar ingantacciyar riwayar kan abinda ake cigiya daga wajabcin bayyanar da karatu ba da boye shi a mahallan boyewar.

Hakika an ambaci wasu fuskokin don kafafa dalili karkashin abind aya zo cikin ingantacciyar riwaya daga karinoni da shaidu da suke shiryarwa kan zahirin abinda ta kunsa da mafhumi daga fuskoki guda biyar, kamar yanda ya zo cikin littafin Aljawahirul Kalam juz 9 sh 366.

Ingantacciyar riwaya ta biyu:

عن زرارة عن أبي جعفر عليه السلام قال: قلت له رجل جهر بالقراءة فيما لا ينبغي الجهر فيه، أو أخفى فيما لا ينبغي الإخفاء فيه، وترك القراءة فيما ينبغي القراءة فيه أو قرأ فيما لا ينبغي القراءة فيه، فقال: أيّ ذلك فعل ناسياً أو ساهياً فلا شيء عليه.

Daga Zurara daga Abu Jafar amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: nace masa mutum ne ya bayyanar da karatu a wurin da bai kamata a bayyanar ba, ko kuma ya boye karatu a wurin da bai kamata aboye ba, ko kuma ya bar karatu a wurin da bai dace a bar karatu ko kuma yayi karatu a wurin da bai da ayi karatu cikinsa ba, sai Imam (a.s) yace: idan ya aikata haka yana cikin mantuwa da rafkana to babu laifi a kansa.

Fuskar kafa dalili: mafhumin (babu laifi kansa) a mukamin mantuwa da rafakana yana nufin Kenan idna da ganganci yayi akwai laifi a kansa, hakan ya nuni kan gurbatar sallarsa, abinda yake lazimtar hakan shine wajabcin bayyanar d akaratu cikin wuraren da ake bayyanar da shi, da wajabcin boye a wuraren da ake boyewa.

Wadannan ingantattun riwayoyi guda biyu a zahirin lafazinsu kamar yanda ya kasance a farko da kuma mafhuminsu kamar yanda yake a na biyu da wasunsu daga wasu hadisain kamar yanda ya gabata cikin wadanda suka kafa hujja da su daga Mashhur kan wajabcin bayyanawa da boyewa.

الوسائل بإسناده عن علي بن جعفر عن أخيه موسى عليه السلام قال: سألته عن الرّجل يصلّي من الفريضة ما يجهر فيه بالقراءة جعل عليه أن لا يجهر؟ قال: إن شاء جهر وإن شاء لم يفعل([1]).

Alwasa’ilul Shi’a da isnadinsa daga Aliyu Ibn Jafar daga dan’uwansa Musa (a.s) yace: na tambaye shi dangane da mutumin da yake sallar farilla da ake bayyanar da karatu ya sanya masa kada ya bayyanar da karatu? Sai yace idan ya so ya bayyanar da karatu idan ya so ya boye.

Fuskar kafa dalili: a bayyane yake hakika hadisin yana shiryarwa kan zabi da wannan hadisi ne mawallafin Almadarik juz 3 sh 357 ya kafa hujja kan rashin wajabcin bisa tattara bangarorin hadisan guda biyu da suke karo da juna da dora su kan mustahabbanci, ya kuma yi da’awar cewa lallai ingantacciyar riwayar Aliyu Ibn Jafar  tafi bayyana cikin sanadi da dalala daga ingantacciyar riwayar Zurara babu fuskar dora ta kan takiya.

Mawallafin littafin Alwasa’il (k.s) yace: ni ina cewa: Shaik Dusi ya dora riwayar Aliyu Ibn Jafar kan takiyya sakamakon riwayar ta dace da riwayar mazhabar sunna, wasu daga ba’arin malamanmu sun dora shi kan babbar bayyana da ma’anar daga sauti kari kan mafi karancin bayyanarwa sakamakon abinda ya gabata da sannu bayani zai zo da yardar Allah, bayanin kan mushabbanci bayyanar da karatun bismillah a wuraren da kae boye karatun sallah ya gabata, maganarsa ta zo karshe an dage mukamin sa.

Sai dai cewa kuma ya bada amsa kan wannan tattarowar a wurin mawallafin Almadarik kamar Assayid Murtada (k) ya zabi mustahabbanci tunda farko: 1- da rashin amintuwar malamai daga ingantacciyar riwayar Aliyu Ibn Jafar hakan na nufin cewa riwayar ba hujja ba ce a kankin kanta bata karfin da zata iya jayayya da bangaren farko na riwayoyi.

2-zahirin ingantattun riwayoyin yana umarni da dawo da mandukin kamar yand ayake cikin riwayar farko da dawo da mafhumi kamar yanda yake cikin ta biyu, zahirinsa bai kasance daga babin hukuncin taklifi ba, bari dai yana daga abinda yake shiryarwa kan gurbatar sallah, wannan yana daga umarni na Irshadi ya zuwa ga baci da rashin faduwar umarni na farko, sai wajabci ya zama maimaitawa bisa dogaro da hukuncin hankali, a bayanne yake mustahabbanci bai dauke da ma’anar baci saboda haka riwayoyin biyu basu karbar mustahabbanci kadai suna shiryarwa zuwa ga wajabci ne karara. Ka sanya lura sosai, zamu cigaba da yardar Allah ta’ala.

 

Tura tambaya