lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,

 

Ina cewa: daga cikin mustahabban sujjada akwai kallon gefan hanci a halin da yake sujjada, an danganta haka zuwa ga wasu jama’a daga Malamai kamar yanda ya zo cikin littafi Azzikra  sannan mawallafin Alhada’ik yace: abin da mai littafin Azzikra (K.S) yana ishara da rashin tsinkayar madogararsa da wannan waninsa daga Malamai ya yi ikirari karara.

Sai dai cewa madogararsa wacce na tsinkaya cikin littafin Alfihul Rida sh 8 inda amincin Allah ya tabbata a gareshi yace:

(ويكون بصرك في وقت السجود إلى أنفك وبين السجدتين في حجرك، وكذلك في وقت التشهد).

Kallonka ya kasance zuwa ga hancinka tsakankanin sujjadodi biyu cikin dakinka haka zalika a halin zaman tahiyya.

Sannan malamai da suka zo daga baya hakika sun nakalto wanna hukunci haka mustahabbanci kallo zuwa ga daki  a halin zaman tahiyya, hakika malamai sun yi ikirari da rashin samun ma dogara, kadai sun mallaki haka bayan karhancin rintse idanu cikin kamar yanda ya gabata-da mubalaga cikin kushu’i da fuskanta kan ibada, wannan hadisi an ambaci Riadawi kamar yanda kake gani karara yake cikin hakan bai kasance daga zahiri da har zai fa’idantar da zato ba, bari dai yana daga abinda yake karara da yake fa’idantar da yakini-kuma a zahiri madogarar hukuncin a wurin magabata sune Sadukaini kamar dai yanda ka sani a wani mukami ba wannan ba- maganarsa ta kare.

Assayid Ustaz cikin ta’alikinsa kan littafin Urwatul Wuska: (hukunci da mustahabbancinsa bayan raunin madogara da rashin tsayuwar dalilin tasamuhu domin tabbatar mustahabbancin mahallin kallo) ina cewa wannan yana shiryarwa abinda yafi dacewa ya zo da hakan da sa ran samun lada domin kauracewa shida bidi’a, ka lura.

Cikin littafin Almuntaha ya kafa dalili kan haka da fadinsa: (domin gudu kada ya shagaltar da zuciyarsa daga barin bautar Allah ta’ala) abinda nufi da illar dalili shine bayanin hikimar hakan bawai illa da ta zo cikin ilimin Mandik da Falsafa badaga koruwar ma’alulu sakamakon kruwar illarsa kamar yanda yake cikin halittu, abinda yake cikin shari’a kadai dai yana daga hikima bawia ill aba, ka lura.

Na takwas: addu’a gabanin fara zikiri yace:    

(اللّهم لك سجدت وبك آمنت ولك أسلمت وعليك توكلت وأنت ربي، سجد وجهي للذي خلقه وشق سمعه وبصره، والحمد لله ربّ العالمين، تبارك الله أحسن الخالقين).

Ya Allah kai na yiwa sujjada da kai na yi Imani kai na sallamawa da kai na dogara kai ne ubangijina, fuska ta tayi sujjada ga wanda ya halicceta ya tsaga jina da ganina, dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin Talikai, tsarki ya tabbata ga Allah mafi kyawun masu halitta.

Ina cewa: sujjada cikin mahiyarta da kaifiyarta tana daga abinda yake shiryarwa zuwa ga kurewar Kankan da kai da bauta ga Allah matsarkaki, kuma itace mafi kusancin abinda bawa yake kusantar ubangijinsa da shi, lallai sallah tana da kufaifaiyi da samarori zahiri da badini masu tarin yawa a duniya da lahira, wani lokaci  Aklak daga cikin tasirinta shine: tana hani dag aikata alfasha da munkari, a wani karon kuma sallar godiya ga Allah

﴿فَلْيَعْبُدُوا رَبَّ هَذَا الْبَيْتِ (3) الَّذِي أَطْعَمَهُمْ مِنْ جُوعٍ وَآمَنَهُمْ مِنْ خَوْفٍ﴾

Tabbas su bautawa ubangijin wannan Daki*wanda ya ciyar da su daga yunwa ya amintar da su daga tsoro,

Ta uku itace sallar debe haso:

 ﴿وَأَقِمْ الصَّلاةَ لِذِكْرِي﴾

Ka tsayar da sallah domin tunawa da ni.

Ubangiji matsarkaki yace: (ni abokin zaman wanda ya tuna dani ne) (duk wand aya debe haso da Allah zai tsorata daga mutane) ta hudu it ace kurewar kurewa cikin sallah: itace sallah neman kusanci da sanin Allah kamar yanda ya zo cikin suratu Alak a karshen aya daga ayoyinta cikin umartar annabi da sujjada domin samun kusanci zuw aga Allah (kayi sujjada ka nemi kusanto) duk wanda ya karanta wannan aya ko ya ji ta wajibi yayi sujjada kamar yanda yake cikin hadisai da Risaloli tana daga ayoyin sujjadarv wajibi.

Da addua’r sujjada wacce aka ambata cikin matani baki dayansa daga ayoyin tauhidi da bautawa Allah cikin kololuwar bauta.

Abinda yake shiryarwa kan mustahabbanci akwia abinda ya zo cikin Musahhihahtu Halabi daga Abu Abdullahi (A.S) yace: idna kayi sujjada ka yi kabbara kace (ya Allah domin kai…) har zuwa karshen abind aya zo cikin matanin addu’ar, sai dia cewa cikin nuskar Wasa’il da Alhada’ik da wasunsu shine: (Alhamdulillahi) ba tareda wawun ba (Wasa’il babi 2 daga babukan sujud hadisi 1) amma cikin nuskar Tahzib da muke da ita yanzu ka duba j 2 sh 79 hadisi 295 Allah ne masani amma abind ayafi dacewa ya kasance tareda wawun  da niyyar Allah ya bamu lada kamar yanda hakan shine ra’ayinmu 

Tura tambaya