lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Rayuwar Imam Aliyu Bn Husaini Assadaj atakaice

Shi ne Aliyu Bn Husaini `da na uku daga cikin jerin`ya`yan Imam Husaini (a.s) sunan babarsa Sharu Banu, mafi shahara daga lukubbansa sune Zainul Abidin, an haifi Imam Sajjad (a.s) shekara 38 bayan hijira, ya taso birnin Madina, ya riski shekaru biyu cikin halifncin kakansa Sarkin Muminai Aliyu Ibn AbuDalib, saannan ya rayu shekaru goma tareda baffansa Imam Hassan Almujtba(a.s) duka a gaban idonsa abubuwan da suka faru suka faru, bayan shahadar baffansa a shekara 50 bayan hijira ya rayu shekara goma zamanin Imamanci babansa Imam Husaini (a.s) ya kasance tareda mahaifinsa adaidai lokacin tashen iko da karfin Mu'awiya Ibn Abu Sufyan da ya kasance cikin fito na fito da rigima da shi.

A watan Muharram shekara 60 bayan hijira cikin lamarin da ya tuke da shahadantar da mahaifinsa Imam Husaini (a.s) a kasar Karbala hakika Imam Sajjad ya halarci wannan fagen daga, bayan musiba da bala'in da ya kasance a filin Karbala a bayan shahadar mahaifinsa kai tsaye Imamanci, sojojin Ibn Murjanatu sun kamashi tareda sauran fursunoni suka tasa keyarsu zuwa kasar Sham fadar Yazid Ibn Mu'awiya (l.a) a kan hanyarsu ta kaisu kasar Sham shi ne jagora dukkaninsu ya kasance cikin matsanancin bala'a da bakin ciki, hakika cikin wannan tafiya yayi wani zazzafan jawabi da kone rukunan hukumar Yazidu ya tona musu asiri, bayan dawowa daga Sham Imam Sajjad (a.s) ya zauna a garin Madina har zuwa shekara 94-95 bayan hijira da yayi shahada, kabarinsa nan kusa da kabarin baffansa Imam Hasssan Almujtaba (a.s) cikin sananniyar makabartar Madina mai suna Baki'a.

Halifofin da suka yi zamani daya da shi:  

Hakika Imam Sajjad (a.s) yayi zamani da halifofi guda shida kamar haka:

1 Yazidu Ibn Mu'awiyatu 61-64 hijiri.

2 Abdullahi Ibn Zubairu 61-73 hijiri

3 Mu'awiyatu Ibn Yazid cikin wasu yan watanni a shekarar 64 hijiri.

4 Marwanu Ibn Hakam `yan watanni cikin shekara 65 hijiri.

5 Abdul Malik Ibn Marwan 65-86 hijiri.

6 Walid Ibn Abdul Malik 86-96 hijiri.

Rashin lafiyar da Imam yayi fama da ita wata maslaha ce daga ubangiji:

Abin ban takaici wasu mutane sakamakon jahicli da rashin fadakuwa sun kasance suna kallon Imam Sajjad (a.s) matsayin mutum mara koshin lafiya mai fama da ciwo gajiyayye da fuskarsa tayi canja zuwa ruwan dorawa mara kwarin jiki da ruhi tsoho tukuf, sai dai cewa a hakika ya kasance akasin wannan siffa da tunani nasu domin gaskiya batu shi ne idan ka cire dan gajeran lokaci da yayi wata yar gajeriyar rashin lafiya a filin Karbala to fa bayan ya samu lafiya ya cigaba da rayuwarsa cikin koshin lafiya kamar sauran Imamai (a.s).

Babu shakka Imam Sajjad (a.s) cikin wancan gajeriyar rashin lafiya ya kasance cikin kulawar ubangiji domin ya zamana ya samu uzuri daga barin halartar fagen daga da kwami da kuma jihadi, samuwarsa mai daraja da tsira daga hatsarin kisan sojojin haya `yan neman kudi da hakan ne silsila da tsatson Imamanci ya samu dorewa da dawwama.

Shaik Sibdu Ibn Jauzi ya rubuta cewa: Imam Sajjad ya tsira daga kisa a filin Karbala sakamakon bashi da lafiya.

Muhammad Ibn Sa'ad ya rubuta cewa: a ranar Ashura a filin Karbala Imam Sajjad ya kasance tareda mahaifinsa yana da shekaru 23 a wani fadin 24 saboda haka fadin cewa wai ya kasance karamin yaro a lokacin wannan karya ce tsagwaronta kadai ya kasance cikin rashin lafiya wannan uzuri ya hana shi tarayya da shiga cikin yakin.


Tura tambaya