lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Imam Sadik (as)

 

Hasken rana ilimi da malamai

Tunda aka haifi Imam Sadik (as) hasken tunaninsa yake haskaka kalamansa suke yaduwa da jawo hankula ta yanda zukata suka karkato zuw aga soyayyarsa daga kowanne da kwari, Imam Sadik ya kasance alkiblar gama garin mutane da malumma shi iliminsa babban tafki ne ta yanda malamai basu iya kamfata daga gareshi face cikin cokali saboda tsananin yalwarsa mara iyaka.

Imam Sadik (as) ya zo domin ya tunbuke dukkanin wata tsiya daga cikin duniya daidai lokacin da mutumtaka take halin shashshakar mutuwa daga barin ma’anawiyyarta.

Ilimin Imam Sadik (as) ya kyalkyala sararin samaniya kamar yanda ya yadu cikin dukkanin wani bigire daidai lokacin da Daular Umayyawa da Abbasiyawa da sauran mutane suka shagaltu da abubuwa marasa muhimmanci suka kuma nesanta muslunci daga mahallinsa na jagorantar rayuwa sakamakon kulle tunani da sanya sasarin kan bakunan manyan masana da kawar mahaskakan kwakwale!!

Imam Sadik (as) ya kasance mafi kamalar hankali cikin mutane mafi kyawun dabi’u da fasalin halitta saboda shine cigaban tsatson annabta da imamanci, ya kasance yana cewa:

 [ حدثني ابي وحديث ابي حديث جدي وحديث جدي حديث ابيه وحديث ابيه حديث علي بن ابي طالب وحديث علي بن ابي طالب حديث رسول الله صلاى الله عليه واله

Babana ya bani labari kuma hadisin babana shi hadisi ne daga kakana hadisin kakana hadisin babansa ne Ali bn Abu Dalib kuma hadisin Ali bn Abu dalib hadisin manzon Allah (s.a.w) ne.

Ya bayyanar da mafi girma sauyi na sakafa cikin tarihin dan Adam baki daya cikin zantukan masu tsada da uslubinsa mai yayewa domin karfafar da katange mafahim din muslunci daga tsatsantuwa da bushewa.

Shine ya fara assasa Jami’ar ilimin addini ta farko a birnin Madina wanda adadin dalibanta yakai mutum 4000 sun kwararo zuwa gareta daga dukkanin rango mai zurfi, sun karanta dukkanin abinda suke kwadayi cikinta daga mabanbanta ilimummuka da nazariyoyin falsafa da ra’ayoyin malamai da fannoni daban-daban, kuma shine wanda ya dasa irin ilimin zamani wanda akafi sani da ilimin kimiyya da fasaha (technology)

Imam Sadik (as) shine wanda ya fara kirkirar tsarin takasssusi cikin ilimummuka ya kuma kirkiri asasi na zamani ga ilimin kimiyya da pysics da lissafi da likitanci da…..

Ya iya samun nasarar tarbiyar manyan malaman muslunci da habbaka kwakwalensu domin su bada gudummawa kan cigaban al’umma kamar misalin Jabir bn Hayyan, kamar yanda jagororin mazhabobin muslunci sukai karatu a hannunsa misalin Abu Hanifa wanda da bakinsa yake cewa: (ba da ban shekaru biyu da Nu’umanu ya halaka).

Hakika Imam Sadik (as) yayi kira kan hadin kan addini da ilimi shima dama sha’aninsa kamar sha’anin sauran tsatson tsarkaka ne ya kuma watsi da rayuwa sufanci da bushewa, sanna ya tabbatarwa da duniya cewa muslunci adddini ne na ilimi da aiki da tsantseni da takawa gabanin kasantuwarsa addini ibada hakan ya tabbata cikin fadinsa:       

 (( عالم افضل من الف عابد )) .

Malami guda rak yafi mai ibada dubu.

Ya kkar da mutane yaya zasu fita daga cikin rayuwar jumudi mai cike da duhu hakan ya kasantu ne da kewayar iliminsa mai yalwa mai haskaka wanda cikinsa ya koyar da mutane ya fuskantar da su ingantacciyar fuskantarwa har takai ga sun samu damar iya mayar da kasa zinariya!!

Imam (as) ya taimaki addini muslunci da tunanunnukansa maus haske ya yaye makauniyar jahiliya da mafahin na jabu wadanda sarakunan lokacin ke kansu da kuma amfani da labulen muslunci wanda hakan yakai ga girgiza karagar mulkin dagutan sarakuna, a dai wannan lokacin sai karbuwar Imam ta dinga habbakuwa da bunkasa tsakankanin jama’a musammam ma zamanin mulkin Abbasiyawa, ta yanda dukkanin mutanen kirki suka dinga kaunarsa kai hatta sauran halitt!!!

Hukumar zalunci ta tilastawa Imam (as) zaman gida ta kuma yanke dukkanin sadarwa daga gareshi musammam shekaru goma na  karshen rayuwarsa, dalilin hakan shine sarakunan Abbasiyawa wadanda dukkanin himmarsu ta kasance cikin son mulki da biyewa sha’awe-sha’awe suna jin tsoran gocewar karagar mulkinsu daga barazanar samuwar Imam cikin jama’a.

Hakika sun yaki Imam da dukkanin hanyoyi takunkumi da munanen hanyoyi daga ciki akwai aika yan liken asiri cikin sahun sahabbansa da aikin jirkita muslunci da sukan ilimin Imam.

Sarakunan Abbbasiyawa sun kwace litattafansa sun kona su sun salwantar da nazariyoinsa da darussansa hakan ya kasance lokacin rayuwarsa ba bayanta, lallai abinda muke gani yau bai wuce digo daga tafkin iliminsa ba, saboda darussan Imam Sadik (as) da ilimummukansa wadanda ya bayar da su suna matukar yawa ta yanda dukkanin alkalumma cikin duniya na iya karewa basu gama rubuta su ba.

Abbasiyawa basu tsaye hannaynesu kame ba suna ganin yadda hasken Imam yake yaduwa cikin kowacce zawiya da bigire daga ban kasa ko mina mutane suna ta batun iliminsa, sai suka dinga nuna kiyayyarsu da hassada suna rura wutar makauniyar jahilyarsu har takai ga sun sanya masa guba sun kashe shi sun dusashe haskensa, sai dai cewa sun manta da cewa hanyar Imam Sadik (as) ta riga wanzu har zuwa tsawon mikawar zamani ba kuma zasu iya kau da it aba, sannan lallai dalibansa masu cika alkawali sun wayi gagari matsayin manyan taurari masu haskaka cikin duhun dare bayan shahadarsa, sai ya zamanto sun mike tsaye cikin tarjama tunaunnukansa zuwa ga al’ummar musulmi domin daukaka tutar muslunci da musulmai.

Amincin ya tabbata ga Sadik musaddak na shida daga imamai ma’asumai (as)       

Tura tambaya