lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wata yar takaitacciyar kissa da a gaske ta faru

a Zamanin da ya shude anyi wani tsoho  da ya kasance yana zaunawa tareda `dansa, wata rana suna cikin tattaunawa kwatsam sai suka ji ana kwankwasa kofa, sai matashin `dansa ya tashi ya je ya bude kofar, bude kofar ke da wuya sai ya ga wani mutum bako yana kokarin shogowa gidan ba tareda yin sallama ba yana mai nufar zuwa wajen wannan tsoho, yana cewa tsohon ka ji tsoran Allah ka biya bashin da yake kanka na yi hakuri fiye da haddin da ya dace yanzu kam hakurina ya rigaya ya kare , sai bakin ciki ya mamaye wannan matashi sakamakon ganin yanda ya yiwa wannan tsoho, hawaye suka dnga kwarara daga kuncinsa, sai ya tambayi wannan bako nawa ne kake binsa bashi?sai mutumin yace:  ina binsa fiye da dinare dubu casa’in, ka kyale babana kayi bushara da zuwan sabon alheri da izinin Allah, wannan matsahi ya tafi dakinsa domin kawo wannan kudade domin yana da dinare dubu ashirin da bakwai da ya tara daga albashinsa wadanda yake taskacewa saboda ranar aurensa sai dai cewa ganin abinda ya faru sai ya fifita kare mutuncin babansa kan auren da yake burin yinsa, wannan ya shigo wannan majalisi ya cewa wannan mutumin ga wani yankin daga kudaden da kake bin mahaifina, sannan ka jira sauran da sannun zamu biyaka su nan da ba jimawa ba da yardar Allah.

Sai wannan tsoho ya fashe da kuka yana neman wannan mutumin da ya dawo da `dansa wannan kudade da ya bashi, lallai `dan nasa yana cikin bukatar kudaden, bai da wani laifi cikin abinda bashi ya aikata ba, sai dai cewa wannan mutumi yaki yarda da bukatra tsohon, sai wnanan matashi ya shiga cikin sa’insar da suke yi ya cewa da mutumin ya rike wannan kudade a hannunsa, kuma daga yanzu wurinsa zai zo neman biyan bashin sauran, ya dena zuwa wajen wannan tsoho, sai wannan matashi ya dawo wajen mahaifinsa ya sumbaci goshinsa yana mai fadin: ( ya mahaifina mutuncinka da girmanka ya girmama daga wadancan kudade kowanne abu yana da lokaci da jin haka sai wannan tsoho ya rungume wannan matashi ya fashe da kuka yana fadin: (Allah ya yarda da kai ya baka dacewa ya datar da takunka) rana ta biyu yayinda matashin ya shagaltu da aiki a inda yake aiki sai daya daga abokansa wadanda yaji bai gasnu ba ya ziyarce shi, bayan sun gaisasai abokinsa nasa yace masa: ya dan’uwa jiya na kasance da daya daga cikin manyan ma’aikata ya nemi da in binciko masa amintaccen mutum mai kyawawan dabi’u mai tsarkakakkira zuciya, wanda yake da buri da kwadayi cikin gudanar da aikinsa cikin nasara, sai dia cewa ban sami wani mutum da yake da wadannan siffofi ba wanda ya wuce ka, yanzu menene ra’ayinka cikin karbar wannan aiki, da barin aiki da kake yi yanzu take ba tareda bata lokaci ba, domin mu je wurin mutumin da maraice mu gana da shi, sai zuciyar wannan matashi ta cika da bushara yana mai cewa: lallai wannan addu’ar mahaifina ce hakika Allah ya amsa, sai yayi godiya ga Allah kan falalolinsa masu tarin yawa.

Da yamma tayi sai suka wajen mutumi suka ganshi zuciyar mutumin ta nutsu da shi matuka gaske, sannan ya tambaye shi kan albashin da yake dauka, sai yace masa: albashina ya kasance dinare 4970, sai mutumin yace masa ka je gobe da safe ka dawo sannan ka gabatar da janye aiki daga inda ka kasance kana aiki, sannan zan dinga baka dinare 1500 daga yanzu, da kari kan kashi goma cikin dari da zaka dinga samu duk wata, da kuma kudin hayar gidan da zak zauna, sannan zan baka mota ta zamani da kuma albashin wata shida domin kaje ka kara kintsawa da yin gyare-gyare, da jin wannan Magana sai ya fashe da kuka yana cewa: kayi bushara da alheri ya mahaifina,

Sai wannan da ya bashi aiki ya tambaye shiakn dalilin da ya sanya shi kuka, sai ya bashi labarin dukkanin abinda ya faru kwana gabanin zuwan sa wurin sa, sai wannan mutumi take ya bada umarnin a biya bashin da ake bin mahaifinsa.

Wannan itace riba da amfanin biyayyar iyaye.

  

Tura tambaya