lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kur’ani cikin rayuwar imam kazim tare da alkalamin shaik abdul-jalil mikrani


Kur’ani cikin rayuwar imam kazim tare da alkalamin shaik abdul-jalil mikrani

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Hakika ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu na daya daga cikin nauyaya guda biyu cikin wannan al’umma da abin da ke hukunta daidaituwarsu wanda manzon Allah (s.a.w) ya tabbatar cikin hadisin saklaini lallai ahlil-baiti sune masu tarjama kur’ani sune wadanda Allah ya ajiye sirrikan kur’ani da ilimummukansa a wajensu, wannan daidaituwa tana tabbatar da cewa ahlil-baiti (as) sune kwararru kebantattu cikin tafsirin kur’ani da tawilinsa da bayanin hadafofinsa.

 

Imam kazim (as) da rawar da ya taka cikin ilimi da ma’arifa:

 

Imam (as) ya mike tsaye dauke da nauyin mas’uliyar imamanci da shiriyarwa mafi girma  bayan wafatin mahaifinsa  imam sadik (as) karkashin kiyaye ilimummukan shari’a da tarbiyya da rainon jama’a muminai da shayar da su kur’ani mai girma da fahimtar da su da tafsirin kur’ani da koyar da su ilimummukan sunna mai daraja wacce ya rawaito shida mahaifansa tsarkaka daga kakansu manzon Allah (s.aw) Allah ya sanya albarka cikin wancan kokari mai ma’ana mara yankewa don kiyaye addini da kare shi sai makarantar imam kazim ta samar wani adadi daga malamai da masana ilimin fikihu da manya-manyan malaman ilimin hadisi wadanda suka mike da daukar nauyin mas’uliyar yada ilimin muslunci daga makarantar ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu.

Hakika imam kazim (as) ya rayu cikin zamani da yake cike da kungiyoyi  da makarantun tunani da akidoji daban-daban, wannan lokaci na makarantun fikihu da ijtihadi da ya yi zamani da imam sadik (as)  da samar babban matattakala da tsani zuwa ilimummukan ahlil-baiti (as) cikin wannan lokaci da ilhadanci da zindikanci ya sulalo sannan kuma makarantun karkacewa hanyar Allah da bata da sufanci suka kafu, kamar yadda bakin ilimummuka suka shiga harkar istinbadin hukunce-hukuncen shari’a wadanda aka fake da wani adadi mai yawan gaske daga kirkirarrun hadisai kagaggu danganannu cikin sunna annabi mai daraja.

Babu shakka cewa dukkanin wadannan makarantu  da wadannan fahimtoci da tunanunnuka na karkacewa daga hanyar gaskiya sun sanya raunana tunanin muslunci kuma sun zama barazana kan muslunci cikin hakikar shari’a da akidu.

Cikin wannan marhala bukata na bayyana zuwa ga karfafa sakafar kur’ani ingantacciya  da yada wayewar muslunci da kuma bayanin ingantattun hadisai  na sunna da yaye kagaggen batu mara tushe sannan babu wanda yafi dacewa da wannan aiki fiye da imam kazim (as) da daukar nauyin taka rawar sakafa  domin katange bangon muslunci baki daya daga fadawa bayan shubuha da karkatar akida.

Duk da tsananin matakai na siyaysa da siyasar ta’addanci da kisa da dauri wacce gwamnatin abbasiyawa ke amfani da ita kan alawiyawa a kebance kuma kan imam kazim (as) wanda shi ne cibiyar mafi girma nauyaya biyu cikin al’ummar musulmi, sai dai cewa hakan bai hana imam kazim (as) cigaba da taka rawarsa ba da sauke nauyin dake kan wuyansa a mtasayinsa na imamin al’umma katangarta a tunani da akhlak da mutumtaka.

Kan karya wannan yaki na tunani da ilimi ya zama dole mu koma zuwa ga masdarin farko cikin shari’ar muslunci mu nemi amsa daga gare shi daga dukkanin abin da muslmi ke bukata zuwa gare shi cikin abincinsa na ruhi da tunani da zamantakewa, kur’ani masdari nr da tsuhen ilimi da shari’a a cikin muslunci. Duk sanda aka nesantu daga kur’ani tabbas zace-zace da shubuhohi za su shigo tare da ijtihadodi da bayyana ra’ayoyi na kankin kai cikin addini, shari’a ta samu kanta cikin da’irorin bukatun kai da son rai da karkata mara iyaka.

Hakika makarantar ahli-baiti (as) ta kwadaitar kan wayar da kan musulmai cikin nuna musu larurar riko da komawa kur’ani cikin komai cikin dukkanin abin da ya kebanci al’amuran rayuwarsu cikin addininsu da rayuwarsu zuwa janibin haka riko da sunnar annabi mai daraja mai bayani da sharhi ga nassoshin kur’ani masu tsarki.

Alakar musulmi da kur’ani:

Himmatuwa da kur’ani da bayyanar da tsarkakarsa da kasantuwarsa tushe cikin rayuwar musulmi yana daga mafi muhimmancin haduffan muslunci cikin gina daidaikun mutane da al’umma, kur’ani mai girma da sunnar annabi sun karfafa wajabcin bin kur’ani da yin aiki da koyarwarsa  da sunnonin Allah wadanda suka zo cikinsa, hakan bai tabbatuwa sai da karatun nutsuwa bana gaggawa ba wanda shi ne karatun tadabburi kamar yadda kur’ani ya siffanta hakan.

Hakika imam (as) ya kasance daga mafi kyawuntar mutane cikin tilawar kur’ani da mafi kyautata sautinsu darensa ya ksance tilawar da karatun ayoyin kur’ani, ta yaya imam (as) ba zai kasance haka ba, alhalin Allah ya yi izinin cewa su ahlilbaiti (as) marhalolin ambaton sunansa da tilawar ayoyinsa      

 (فِي بُيُوتٍ أَذِنَ اللَّهُ أَنْ تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا اسْمُهُ يُسَبِّحُ لَهُ فِيهَا بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ * رِجَالٌ لا تُلْهِيهِمْ تِجَارَةٌ وَلا بَيْعٌ عَنْ ذِكْرِ اللَّهِ وَإِقَامِ الصَّلاةِ وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ يَخَافُونَ يَوْماً تَتَقَلَّبُ فِيهِ الْقُلُوبُ وَالأَبْصَارُ )

Cikin wasu gidaje Allah ya yi izini da a `daga cikinsu a ambaci sunansa ana tsarkake shi cikinsu safe da yamma* mazaje kasuwanci ko saye bai shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da sallah da bada zakka suna tsoron ranar da zukata da idanu ke jujjuyawa.    

فقد روي عنه× أنه روی عن آبائه علیهم السلام قال: (سُئل رسول الله – صلی الله علیه وآله – عن قوله تعالی: (وَرَتِّلْ الْقُرْآنَ تَرْتِيلاً )   قال: بیّنه تبیاناً، ولا تنثره نثر الرمل، ولا تهذّه هذّ الشعر، قفوا عند عجائبه، وحرّکوا به القلوب، ولا یکون همّ أحدکم آخر السورة)

Hakika an rawaito daga gare shi amincin Allah ya tabbata gare shi daga babanninsa (as) ya ce: an tambayi manzon Allah (s.a.w) gameda fadinsa madaukaki (ka kyautata karanta kur’ani daki-daki) sai ya ce ka bayyana shi bayyanawa, ka da ka `dai`daita shi irin `dai`daita kasar yashi, kada kayi sururin shi irin sururin wake, ku tsaya wurin mamakinsa, kuma zukata da shi, ka da damuwar dayanku ta kasance kai karshen sura.

 

Shi karatun kur’ani ba daidai yake da yadda ake karatun sauran litattafai ba, bari dais hi karatunsa wani aiki ne mai tarkibi da ke cude da mu’amalolin zuciya da badini da tunani domin ya kasance mashigar fahimta da koyo daga abin da kur’anin mai girma ke shiftawa daga hikima da wa’azozi da koyarwa da suke assasa farin ciki mutum da daukakarsa ta cigaba da mutumtaka.

Da wannan karatun ne na wayewa mafi muhimmancin fa’idojin badini da ruhi ke tabbatuwa karkashin tilwar littafin Allah da duba da nazari cikinsa.

Matsalarmu cikin wannan zamani shi ne lallai karatunmu ya wayi gari misalin karatun jarida da sauke wajibi kamar yadda malaman fikihu ke fadi. Karkashin wannan hadisi mai albarka wanda imam kazim (as) ke rawaito shi daga kakansa manzon Allah (s.a.w) zamu iyakance malhamomi alaka ta misali tsakanin littafin Allah da musulmi.

 

Ma’auni cikin tilawar kur’ani:

tilawa ita matakin farko ce cikin buduwar musulmi mumini kan littafin shiriya da sasannnin hasken  Allah mai girma, bai kamata ga muslmi ya yi watsi da tilawar kur’ani ba da guzurintuwa daga haskayensa da albarkokinsa, ya zama daga mabayyani cewa tsanantuwa matsaloli da musibu da radade-radade wadanda mutum ke fuskanta cikin ruhinsa da nafsu da cikin zamantakewa  lallai suna daga muhimman dalilai da suke sanyawa komawa ga littafin Allah da neman mafitarsa da warakarsa, bai kamata waccan tilawa da karatu su zamanto wani abu daban face dai kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya sifffanta su:        

(بیّنه تبیانا، ولا تنثره نثر الرمل، ولا تهذّه هذّ الشعر)

Ka bayyana shi bayyanawa, kada ka daidatita irin daidaita kasar yashi, kada kayi sururinsa irin sururin wake.

Karatu mai amafani da natija shi ne wanda ya kasance da fadin kur’ani da yanayi tsarkaka da yake kewaye da wannan littafin Allah mai girma, shi makarancin kur’ani bai yin tilawarsa kamar yadda yake tilawar wake da kasidu lallai girman kur’ani yafi karfin karanta shi da yanayin  karatun wake da kasidu.

 

Ma’auni cikin fa’idantuwa daga kur’ani:

 idan ya kasance ga harshe da furuci cikin karatun maudu’i da ya dace tare da kur’ani mai karamci kamar misalin share fage don fa’idantuwa da wa’aztuwa da kur’ani, to fa hakika fahimtar ma’ana da farautarta kan mustawar tasirantuwar ruhi da alakantuwar zuciya da tunani tare da kur’ani yanada sharuddansa da dokokinsa sau da yawa kakan samu makarancin kur’ani kwararre cikin ka’idojin tajwidi masanin fannin sauti da rairawa sai dai cewa yana cikin masifar gafala daga tunani da wayewa ga ma’anonin kur’ani da abubun da yake nuni da bayanansa, domin kada mu haramtu daga fuskantar fahimtar da dadadar wa’aztuwa da fa’idantuwa lallai hadisi mai daraja yana fadakarwa da nusantarwa zuwa ga dokokin karanta kur’ani na tunani dadana badini bayan ya bayyana dokin kira’a na lafuzzansa da sautins.  da tsari wanda annabi (s.a.w) ya zana mana cikin karatun kur’ani da tadabburi cikin ayoyinsa da yake misalta taku biyu na asasi:

 

Taku na farko: tsayuwa wajen abubuwa masu sanya mamaki dake cikin kur’ani:

Babu shakka aboki mai karatu lallai annabi (s.a.w) bai nufin abubuwa masu sanya mamaki da bara`buwa kan tunani irin na karatun kissoshi da tatsuninyoyi da tunannuka na karkata bisa ma’anar harafi  ga kalma cikin mafi yawan aikin da ake da ita, kamar yadda lallai nassin annabi mai daraja bai kasance don bayanin mu’ujizozin balaga na lafazi kamar yadda wasu ba’arin mu ke wahamin hakan ta yadda suka takaita mas’alar mu’ijizanci kur’ani cikin da’irar lafazi da sihirin lafazi da balaga kamar yadda bayyane cikin harshen larabawa? Idan haka ne to menene manufar tsyuwa cikin abubuwan mamakin kur’ani?

Amsa: mamakin kur’ani shi ne dukkanin ayoyinsa da koyarwarsa da kimomi wacce ya magana kanta cikin rauwar mutum baki dayanta, daga cikinta janibin zamantakewa da abin da shari’ar Allah ta sunnanta daga hukunce-hukunce ga alakokin zamantakewa, daga ciki akwai janibi tattalin arziki da abin da Allah ya shar’anta cikin kiyaye dukiya da raba ta aikin nemanta da masdarorin samunta.

Sannan daga abubuwan ban mamakin cikin kur’ani mai girma akwai tsarin gina akidu da addini ga mutum bisa kan bayanin ilimi da hujja mai girma ta hanyar faraway da karami da matsakaicin dalilai kan samuwar mahalicci da tukewa da mafi muhimmancin hujjoji da dalilai mabayanna kan tsara halitta da tsarin motsinta da tafiyarta  ta samuwa.

Daga nan abokina mai karatu lallai ita ma’anar tsayuwa kan abubuwan masu mamaki cikin kurani shi ne tsayuwar hankali da tunani da nazari kan abin na nufin lura da shi da tsinkaya  kan abin da ke kunshe cikinsa, annabi mafi karamci yana kiranmu zuwa ga ilimi da ma’arifa da guzuri na tunani daga littafin Allah mai girma wannan tsayuwa ita ce motsin hankali da basira.

Taku na biyu: motsa zukata da kur’ani

Idan motsa hankali ya kasance shi ne farkon maudu’i ingantacce don samun ma’arifa da ilimi, lallai motsin zuciya tana misalta natija da fa’ida ta ilimi daga motsin hankali,  mai hankali ba zai wadatu cikin motsin hankalinsa da zagayen tunaninsa  matukar dai bai kasance  a janibin wannan tunani akwai motsin dabi’a da tausayi ba, saboda hankali bai kera mutum mumini kadai idan ya raba shi da motsin ruhi da zuciya, shi hankali wani lokaci ya kanyi motsi  ya kan jimawa cikin motsi sai dai cewa shi motsin na kasancewa mara amfani ko kuma motsi na (mechanic) makanikiya, hankali na ilimi na taknoloji fasahar zamani ya motsa cikin fagage masu tarin yawa  ya gano abubuwan da aka jahilta a zamanin ya gabace shi wadanda mutane suka gaza cimmmusu da isa zuwa garesu a zamanin baya a tarihin da ya shude, sai dai cewa wannan hankali shi kadai ya jagoranci mutane zuwa ga kera mafi girman tabewa da hasara cikin tarihin mutum  lokacin da akai amfani wannan hankali cikin kera mutuwa da rusau.

Daga nan lallai kur’ani mai girma lokacin tilawarsa da wannan siffofi yana kiranmu zuwa sauraren sautin zuciya da motsa abin da ya daskare daga tausayi da tausasawa da rahama cikin zuciyar da ihsasinmu, babu dalili da yafi bayyana ga wannan ma’ana daga shardanta kur’ani a farko da ambaton lafazin jalala mai daraja (Allahu) da cudanya rahamaniyya da rahimiyya, domin rahama da tausayi su kasance taken motsin musulmi da tsarin rayuwarsa.

 

Kur’ani masdarin saukar da halascin hukumar siyasa:

cikin mafi yawan matakan imam kazim (as) tare da halifa abbasi  imam yana kokarin bayyanar da shakku da tambaya kan halascin hukumar abbasiyawa  da kimarta  karkashin kur’ani mai girma musammam ma ita wannan hukuma ta ginu kan ma’anar gadar annabi (s.a.w)  da dauka cewa lallai ma’abotan wannan hukuma sune ahlin gidansa mafi kusanci da shi ta bangaren dangantaka da asali sun rattaba kan wannan hakki mudlaki garesu cikin jagrantar al’umma da hawa kan kujerar halifancin manzon Allah (s.a.w)  mafi karamci da dunkufar da al’umma da mamaye dukiyoyinta da sunan muslunci, saboda wannan dalili ne imam kazim (as) ya yi kokarin toa asirin wannan hukuma da dajjalan ma’abotanta lokacin tunatowa mamaimaici  ga kur’ani  mai girma  da ayoyin Allah masu daraja cikin muhawararsa  da zamansa tare da harun Rashid (l.a) wannan wani yanki ne daga tattaunawar imam kazim (as) tare da dagutun zamaninsa harun Rashid (l.a)  imam kazim (as) yana rawaito tattaunawar kamar haka    

 (قال...- هارون الرشید-: کیف قلتم أنّا ذریة النبي والنبي لم یعقب، وإنما العقب الذکر لا الأنثی، وأنتم ولد الابنة ولا یکون ولدها عقبا له. فقلت: (أسألک بحق القرابة والقبر ومن فیه، إلا أعفیتني عن هذه المسألة).

فقال: لا أو تخبرني بحجتکم فیه یا ولد علي! وأنت یا موسی یعسوبهم، وإمام زمانهم، کذا أنهي إلي، ولست أعفیک في کل ما أسألک عنه، حتی تأتیني فیه بحجة من کتاب الله، وأنتم تدعون معشر ولد علي أنه لا یسقط عنکم منه شيء ألف ولا واو إلا تأویله عندکم، واحتججتم بقوله عز وجل: (مَا فَرَّطْنَا فِي الْكِتَابِ مِنْ شَيْءٍ)  واستغنیتم عن رأي العلماء وقیاسهم.

فقلت: (تأذن لي في الجواب؟)

Ya ce: ta yaya zaku dinga cewa mu ne zuriyar annabi bayan annabi bai bar kowa ba bayansa, kadai ya bar diya mace, ku kuma `ya`yan diya mace ne alhalin `ya`yan `diya mace basu zama bayansa, sai na ce masa: (ina rokonka don matsayin makusanta da kabari da wanda yake cikinsa da Alllah ka kyale ni daga wannan batu)

Sai ya ce: ba zaka bani labari da hujjarku ba cikinsa ya kai `dan Ali! kai ya musa kai ne shugabansu imamin zamaninsu , haka ya zo mini, lallai ni ba zan maka afuwa ba cikin dukkanin abin da na tambayeka har sai ka zo mini da hujja daga littafin Allah cikinsa, ku jama’ar `ya`yan Ali kuna da’awar cewa babu abin da ya fadi daga gareku daga alifun ko wawun duka tawilinsu yana wurinku, kuna kafa hujja da fadinsa madaukaki mai girma da daukaka: (wani abu bai fauce man aba daga cikin littafin Allah) kuka wadatu daga ra’ayoyin malamai da kiyasinsu, sai nace kayi mini izinin bada amsa?    

قال: هات.

Sai ya ce: zo da ita.

فقلت: (أعوذ بالله من الشیطان الرجیم بسم الله الرحمن الرحیم: (وَمِنْ ذُرِّيَّتِهِ دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَى وَهَارُونَ وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (84) وَزَكَرِيَّا وَيَحْيَى وَعِيسَى وَإِلْيَاسَ كُلٌّ مِنْ الصَّالِحِينَ) من أبو عیسی یا أمیر المؤمنین؟

فقال: لیس لعیسی أب. فقلت: إنّما ألحقناه بذراري الأنبیاء علیهم السلام من طریق مریم علیها السلام وکذلک ألحقنا بذراري النبی| من قبل أمنا فاطمة، أزیدک یا أمیر المؤمنین؟ قال: هات.

Sai nace: ina neman tsarin Allah daga shaidani jefaffe, bismillahi rahmanir rahim: (daga cikin zuriyarsa dauda da sulaimanu da ayuba da yusuf da musa da haruna haka na muke sakawa masu kyautatawa* da zakariya da iliyasu dukkaninsu daga salihai) wanene mahaifin musa ya sarkin muminai? Sai ya ce isa bai da mahaifi, sai nace: kadia dai mun riskar da shi cikin zuriyar annabawa amincin Allah ya kara tabbata garesu daga hanyar maryam  (as) haka ma mun risku da  da zuriyoyin annabi (s.a.w) ta fuskanin fatima, kana son in kara maka ya sarkin muminai? Sai ya ce zo da shi.

قلت: قول الله عز وجل: (فَمَنْ حَاجَّكَ فِيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَكَ مِنْ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةَ اللَّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ)  ولم یدع أحد أنه أدخله النبي| تحت الکساء عند مباهلة النصاری إلا علي بن أبي طالب× وفاطمة، والحسن والحسین أبناءنا الحسن والحسین ونساءنا فاطمة، وأنفسنا علي بن أبي طالب× علی أن العلماء قد أجمعوا علی أن جبرئیل قال یوم أحد: (یا محمد إن هذه لهي المواساة من علي) قال: (لأنه مني وأنه منه).

Sai nace: fadin Allah mai girma da daukaka: (duk wanda ya yi maka jayayya cikinsa bayan abin da ya zo maka daga ilimi to kace ku zo mu kirayi `ya`yanmu da `ya`yayenku  da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku sannan mu kankantar da kai sannan mu sanya tsinuwar Allah kan makaryata) ba wanda ya yi da’awar cewa annabi (s.a.w) ya shigar da shi cikin mayafi a sa’ilin mubahala da kiristocin najran face aliyu ibn abu dalib (as) da Fatima da hassan da husaini, `ya`yayenmu sune hassan da husani, matayennmu it ace Fatima, kawukanmu aliyu ibn abu dalib (as) kan cewa malamai sunyi ijma’ai kan cewa jibrilu ranar uhud ya ce: ( ya Muhammad wannan ita ce taimako daga ali) sai ya ce: (saboda shi daga gare shi nima daga gare shi nake).  

فقال جبرئیل: (وأنا منکما یا رسول الله) ثم قال: لا سیف إلا ذو الفقار ولا فتی إلا علي، فکان کما مدح الله عز وجل به خلیله× إذ یقول:

(قَالُوا سَمِعْنَا فَتًى يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُ إِبْرَاهِيمُ)  إنا نفتخر بقول جبرئیل أنه منا فقال: (أحسنت یا موسی ارفع إلینا حوائجک)

 

Sai jibrilu ya ce: (nima dagta gareku nake ya manzon Allah) sannan ya ce: babu wata takobi face takobin zulo fikar babu wani saurayi face Ali, sai ya zama kamar yadda Allah ya yabi badadinsa ya yinda yake cewa: (sukace munji wani yaro yana ambatonsu ana kiransa Ibrahim) lallai mu muna alfahari da fadin jibrilu da cewa shi daga cikinmu yake sai ya ce ka kyautata ya musa kawo mana bukatunka.

 

Kur’ani da kira’ar harafi

An jarrabi muslunci da kungiyoyi da mazhabobin bata da karkata daga hanyar gaskiya masu batarwa wadanda suka sabbaba da yawa-yawan rauni ga al’ummar muslunci kamar yadda suka tunanin ta’addaci da akidu kan baki dayan al’ummar musulmi.

Ma’abotan wadannan tunanunnuka marasa kyawu suka zo da kage da karairayi da munanan abubuwa da suka damfara su kan addinin muslunci suka tabbatarwa da Allah ido da hannu da kafafuwa Allah ya tsarkaka ya daukaka daga barin abin da suke fadi daukaka mai girma. Kamar yadda basuyi taka tsantsan ba cikin damfara zalunci da tilashi da fin karfi kan sa`buka daga Allah da ya tilasta bayinsa kan aikata su sannan ranar kiyama ya tuhume su ya azabtar da su kan aikata su. Muna ganin wadannan kungiyoyin masu tsaurin ra’ayi da karatu wand aba tsaftatacce ba da mau’du’i ga ayoyin kur’ani mai girma wanda wannan lamari ya yi matukar yaduwa a zamanin imam kazim (as) bata da shubuhohi sun yawaita a wancan lokaci.

 

Shubuhar daidaituwa kan al’arshi

 

Wadannan jahilan masu tsattsaturan ra’ayin basu da wani aiki da ya wuce bahasi da bincike kan wurin da zasu samu wai cewa Allah ya zauna kan karagarsa, Allah ya daukaka ya tsarkaka daga barin haka, tabbas sunyi watsi daga dukkanin taklifinsu na shari’a da addini babu abin da ya rage garesu sai binciken siffofi da gabobi na jikkantuwa ga Allah makagi madaukaki, tare da cewar ma’abota wannan ra’ayi sun nesantar da hankulansu da kawukansu daga yin bincike kan siffofin shugaba na shari’a da siffofinsa da halascin hukumarsa da halifancinsa da hukumantuwarsa kan wuyayen musulmi.

Shin wai hakan na daga shri’ar kur’ani shin hakan yana daga fadin Allah?

Shin kur’ani ya bada damar yin zalunci da kisa ko kuma bai bayar ba?

Amsa shi ne lallai mabiya wannan karatuttuka munana sune masu taimakon azzalumai wadanda suka assasa sakafar makauniyar biyayya da iklasi mudlaki da zartar da abin da shugaba ke so ba wai abin da ubangiji talikai ke so ba.

Hakika wannan tunani da ra’ayi ya kasance cikin tafsirin kur’ani daga cikin mafi hatsarin ra’ayoyi na kiyayya da tsarin ahlil-baiti da imaman gaskiya, sai dai cewa  wannan kiyayya bata iya hana a’imma (as) cigaba da taka rawarsu ba ta sakafa da tunani cikin katange al’umma daga wadannan shubuhohi da kage-kagen akidu, saboda haka nema muke samun imam kazim (as) karakashin tafsirinsa wata tattarowa mai tarin yawa da ayoyin littafin Allah mai girma wadda marawaita hadisi suka rubuta tasu suka nakalto su yana mai bahasin ayoyin da `yan jumudi cikin zahirin lafazi suke riko da su da suke gina tunaninsu da mahangarsu ta daidaitar Allah kan karagarsa ayar shi ne fadinsa madaukaki:

 (الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى)

Allah ya daidaita kan al’arshi.

 

عن القاسم بن یحیی، عن جده السحن بن راشد، عن أبي الحسن موسی× وسئل عن معنی قوله الله "     " فقال: استولی علی ما دق وجل) .

An karbo daga kasim ibn yahaya daga kakansa sahanu ibn Rashid, daga baban hassan musa (as) an tambaye shi kan fadin Allah “    “ sai ya ce: ya mamaye iko kan abin da ya dandake da abin da girmama.

 

Maraja’iyyar kur’ani cikin gina akida

Imam bai isu da tafsirin aya ba ko kuma bada amsa kan tambaya cikin tabbatar da ingantacciyar mahanga cikin gina akidar muslunci, bari dai ya assasa ka’ida kan haka da wani gini da zai kasance tun daga kasa daga tushe cikin ginin akida da imani na addini.

 

فقد روی صاحب المحاسن عن الفضل بن یحیی قال: سأل أبي أبا الحسن موسی بن جعفر× عن شيء من الصفة فقال: (لا تجاوز عما في القرآن) 

Hakika mai littafin almahasinu ya rawaito daga fadalu ibn yahaya ya ce: ya tambayi baban hassan musa (as) gameda wani abu kan siffa, sai ya ce: kada ka ketare abin da ya zo cikin kur’ani.

 

Kimar hankali da ma’arifa karkashin hasken kur’ani

Hankali a mahangar muslunci shi ne shingen zawiyya don sanin mutumtaka yana kuma misalta wata baiwa ta Allah mai girman gaske ga mutum. Saboda shi tsanin alheri ne da sharri, kamar yadda shi hanya ce zuwa ga arziki da farin ciki, cikin zancen kur’ani da annabi muna samun karfafawa mara yankewa kan mutunta hankali da fahimta da tunani, da wanda daga cikin mutane ya yi ado da wannan siffofi masu girma, sai kur’ani ya Ambato wadanda suke sanya hankali suke sanya tadabburi suke kuma yin tunani, abin nufi daga wannan karfafawa  da sigar fi’ili mudari’i ba wani abu bane sai dai ishara da nuni ya zuwa girmamar hankali,  kimar ma’abocin hankali bata kasancewa face karkashin motsin hankali cikin hakikanin rayuwarsa hakan kuma bai kasantuwa face karkashin `yantar da hankali da haskaka shi.

Muna samun wasiyyar imam kazim (as) ga hisham ibn hakam yana bayyana ba’arin ayyukan hankali da kashe-kashensa da muhimmancinsa karkashin kur’ani mai girma da ayoyinsa masu karamci wadanda suka haskaka tunani da basira tahanyar yaye su kan kudirar hankali da karfinsa.

 

Kur’ani ya yi bushara ga ma’abota hankali

  

(یا هشام إن الله تبارک وتعالی بشر أهل العقل والفهم في کتابه فقال: (فَبَشِّرْ عِبَادِي * الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ أُوْلَئِكَ الَّذِينَ هَدَاهُمْ اللَّهُ وَأُوْلَئِكَ هُمْ أُوْلُوا الأَلْبَابِ) .

Ya hisham lallai Allah mai albarka da daukaka ya yiwa ma’abota hankali da fahimta cikin littafinsa bushara cikin littafinsa ya ce: (kayi bushara ga bayina wadanda suke sauraren zance suke bin mafi kyawunsa wadancananka Allah ya shirye su wadancananka sune ma’abota hankula.

 

Kammala hujja da hankali

یا هشام إن الله تبارک وتعالی أکمل للناس الحجج بالعقول، ونصر النبیین بالبیان، ودلهم علی ربوبیته بالأدلة، فقال: (وَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ * إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَالْفُلْكِ الَّتِي تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِمَا يَنفَعُ النَّاسَ وَمَا أَنزَلَ اللَّهُ مِنْ السَّمَاءِ مِنْ مَاءٍ فَأَحْيَا بِهِ الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِنْ كُلِّ دَابَّةٍ وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ وَالسَّحَابِ الْمُسَخَّرِ بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ لآيَاتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ) 

Ya hisham lallai Allah mai albarku da daukaka ya kammalawa mutane hujjoji da hankali, ya taimakawa annabawa da bayami, ya shiryar da su ya zuwa ubangijintakarsa da dalilai, ya ce: (ubangijinku ubangiji guda daya babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi mai rahama mai jin kai* lallai cikin halittar sammai da kasa da sassabawar dare da rana da jiragen da suke tafiya kan ruwa da abin da zai amfanar da al’umma da abin da Allah ya saukar daga sama daga ruwa sai ya raya kasa bayan mutuwarta cikinta ya yada daga dukkanin dabbobi da jujjuyawar iska da girgije horarre tsakanin sama da kasa ayoyi ne ga mutanen da suke sanya hankali)

 

Dalilin hankali kan Allah

 

یا هشام قد جعل الله ذلک دلیلا علی معرفته بأن لهم مدبراً، فقال: (وَسَخَّرَ لَكُمْ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومُ مُسَخَّرَاتٌ بِأَمْرِهِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَاتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ)  وقال: (هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَابٍ ثُمَّ مِنْ نُطْفَةٍ ثُمَّ مِنْ عَلَقَةٍ ثُمَّ يُخْرِجُكُمْ طِفْلاً ثُمَّ لِتَبْلُغُوا أَشُدَّكُمْ ثُمَّ لِتَكُونُوا شُيُوخاً وَمِنْكُمْ مَنْ يُتَوَفَّى مِنْ قَبْلُ وَلِتَبْلُغُوا أَجَلاً مُسَمًّى وَلَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ)

 

Ya hisham tabbas Allah ya sanya hakan dalili kan saninsa da cewa garesu akwai mai tafiyarwa, sai ya ce: (ya horar muku da dare da yini da rana da wata da taurari horarru da umarninsa lallai cikin haka ay ace ga mutane masu hankaltuwa) ya ce: (shi ne wanda ya halicce ku daga kasa sannan digon maniyyi sannan gudan jinni sannan ya fitar daku karamin yaro sannan don kukai karfinku sannan don ku kasance dattawa daga cikin akwai ake cika masa gabani domin kukai wani ajali tsammaninku kwa hankaltu.

 

Wa’azin Allah ga ma’bota hankula

  

... یا هشام ثم وعظ أهل العقل ورغبهم في الآخرة فقال: (وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَلَلدَّارُ الآخِرَةُ خَيْرٌ لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ أَفَلا تَعْقِلُونَ) .

یا هشام ثم خوف الذین لا یعقلون عقابه فقال تعالی: (ثُمَّ دَمَّرْنَا الآخَرِينَ (136) وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِمْ مُصْبِحِينَ (137) وَبِاللَّيْلِ أَفَلا تَعْقِلُونَ) 

وقال: (إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَى أَهْلِ هَذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزاً مِنْ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ)

 

Allah ya yiwa ma’abota hankali wa’azi ya kwadaitar da su ranar lahira, sai ya ce: (rayuwar duniya bata bakin komai face wasa da wargi gidan lahira shi yafi alheri ga wadanda suke tsoron Allah shin yanzu ba zaku hankalta ba)

Ya hisham sannan ya tsoratar da wadanda basa hankaltuwa da azabarsa sai madaukaki ya ce: (sannan muka dammara wadansunsu* lallai ku zaku wuce ta gefansu kona masu wayar gari* da dare shin ba zaku hankaltu ba) ya ce: (lallai mu masu sauka da azaba ne daga sama ga mutanen wannan alkarya sakamakon abin da suke aikata na fasikanci)

 

Nazariyya da kallo kan gobe da zamanin da zai zo nan gaba karkashin kur’ani mai girma

Kur’ani yana kiran mu zuwa samar da canji da kawo gyara cikin matakin kankin kanmu da wasunmu, canjin da sauyin da kur’ani mai girma yake kiranmu zuwa gare shi ya zam adaole ya kasance cikin tsari da tsarawa, wannan shi ne abin da yake kasantuwa karkashin aikin samar da natija da muke aikatawa

 

(وَقُلْ اعْمَلُوا فَسَيَرَى اللَّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ وَسَتُرَدُّونَ إِلَى عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ)

 

Kace suyi aiki da sannnu Allah da manzonsa da muminai za su ga aikinku sannan ko komo wajen masanin gaibu da bayyane ya baku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.

 

Hakika gafalar da gobe da zamani mai zuwa cikin kowanne aiki hakan wani nau’i ne na ci baya da hasara ga aikin da mutum ya sa a gaba, daga nan ne nake kiran `yan’uwa abokai masu tsayuwa kan wannan aiki mai albarka da su zuraffa tunani da dagewa da karanta zamninsu mai zuwa da bata dare don samun nasara da cigaban aikin, a wannan lokaci wanda makiyan al’ummar musulmi ke kaikawo don raba kawukansu da rusa su da bata fuskarsu ta sakafa ta addini, lallai ya zama wajibi kan dukkanin musulmai malamansu da manyansu da wayayyunsu musammam masu himmatuwa kan sha’anin kur’ani da ma’abota kiyaye nauyin da yake kansu su sadaukar da zage dantse da kokari  don karfafa dokoki da asalai na hakikanin muslunci na sakafa ga al’umma musulmai, da bada kariya  don gina zatin al’umma kan asasi da tushen sakafar wahayi da annabta.

Hakan ba zai taba kasantuwa ba sai bayan jin nauyi mai girma da aka dora masu a gaban littafin Allah da sadaukarwa da bada himma madaukakiya, saman dukkanin wannnan shi ne dogaro da Allah shi kadai wanda shi ne tushen dukkanin wani karfi da kamala da dacewa da samun nasarar mutum cikin dukkanin abin da ya sanya gaba, tabbas Allah madaukaki ya yiwa muminai masu sadaukarwa da masu kyauta alkawali da albarkantar aikinsu da rubanya shi

  

(مَثَلُ الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنْبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنْبُلَةٍ مِائَةُ حَبَّةٍ وَاللَّهُ يُضَاعِفُ لِمَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ) 

Misalin wadanda suke ciyarda dukiyarsu cikin tafarkin Allah kamar misalin kwaya ce ta tsirar da zangarniya guda bakwai cikin kowacce zangarniya akwai kwaya dari Allah yana rubanyawa ga wanda ya so Allah mayalwaci ne masani.

 

Babu shakka ya zama wajibi mu yi riko mu kiyaye ruhin muslunci na asali sai hakan bai yiwuwa sai cikin riko da littafin Allah da haskakuwa da haskensa da tafiya kan shiriyarsa ta Allah katangaggiya daga karkata da bata.

Me ya sanae damu ta yiwu annabi mafi karamci (s.a.w) ya gargademu mu muatanen wannan zamani a kebance daga guguwar fitintunu tunannuka da akhlak da zamantakewa wadanda suke barazana ga imanin mutum da rikonsa ga addini da mutuncinsa hakika an nakalto da gare shi amincin Allah ya tabbata gare shi

 (لا خیر في العیش إلا لمستمع واع أو عالم ناطق. أیها الناس، إنکم في زمان هدنة، وإن السیر بکم سریع، وقد رأیتم اللیل والنهار یبلیان کل جدید، ویقربان کل بعید، ویأتیان بکل موعود، فأعدوا الجهاد لبعد المضمار.)

فقال المقداد: یا نبي الله ما الهدنة؟

قال: (بلاء وانقطاع، فإذا التبست الأمور علیکم کقطع اللیل المظلم فعلیکم بالقرآن، فإنه شافع مشفع، وما حل مصدق، ومن جعله أمامه قاده إلی الجنة، ومن جعله خلفه قاده إلی النار، وهو الدلیل إلی خیر سبیل، وهو الفصل لیس بالهزل، له ظهر وبطن، فظاهره حکم، وباطنه علم عمیق، بحره لا تحصی عجائبه، ولا یشبع منه علماؤه، وهو حبل الله المتین، وهو الصراط المستقیم... فیه مصابیح الهدی، ومنار الحکمة، ودال علی الحجة) 

Babu alheri ga rayuwa face ga wadanda ke saurare wayayye ko kuma masani mai furuci, ya ku mutane lallai ku kuna cikin zamanin hudna lallai tafiyarku tanada sauri, tabbas kunga dare da rana suna tsofaitar da dukkanin sabo suna kusantar da dukkanin mai nisa, suna zuwa da dukkanin abinsa akai alkawali, kuyi tanadin jihadi saboda nisan fagen sukuwa.

Sai mikdad ya ce: ya annabin Allah menene hudna? Sai ya ce: bala’ai ba tare da yankewa ba, idan al’amura suka cudanye suka rikice kanku kamar misalin yankin dare mai duhu to ku riki kur’ani, lallai shi ceto ne mai cetarwa, duk wanda ya sanya shi gabansa zai jagorance shi zuwa aljanna, duk wanda ya juya masa baya zai jagorance shi zuwa wuta, lallai shi mai shiryarwa zuwa mafi alherin hanya , shi bayani ne filla-filla shi ba wargi ba ne, yana da zahiri da badini, zahirinsa hukunci, badininsa ilimi mai zurfin gaske, tafkinsa ba a iya kidaita abubuwan mamakinsa, malamai basa koshi daga gare shi, shi igiyar Allah ce karfaffa, shi hanya ce mikakka, cikinsa akwai fitilun shiriya, da mahaskakar  hikima, shi mai shiryarwa zuwa hujja.

‹ النص علی إمامة الإمام الکاظم×بقلم: سماحة السید حسن الخباز

 

Tura tambaya