lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

fassarar alheri da kashe-kashensa zuwa kasi da ami kebantacce da gamamme

  • Ba dukkanin abinda mutane ka ambata yake kasancewa shine abind ake gasgatuwa da alheri ba, dole ya zama a bayan ta'arifinsa akwai asali daga ubangiji daga wahayi da hankali, Ahlil-baiti (as) sune mafi sani daga abinda yake cikin gida, ga yanda suka fassara Alheri :

    قال أمير المؤمنين علي  7: ليس الخير أن يكثر مالک وولدک ، ولكن الخير ان يكثر علمک ، وان يعظم حلمک ، وان تُباهي النّاس بعبادة ربّك ، فانّ أحسنت حمدت الله، وان أسأت استغفرت الله[1]  
  •  Sarkin muminai Ali (as) yanma cewa: alheri ba shine dukiyarka da yayanka su yawaita ba, sai dai cewa alheri shine iliminka ya yawaita, hakurinka ya girma, kayi wa mutane kwarjini da ibadarka, duk sand aka kyawunta aiki ka godewa Allah, idan kuma ka munana ka nemi gafararsa.

  • Sau da yawa mutane kanyi tunanin cewa alheri yana ga mai tarin dukiya da `ya`ya kadai, sai dia cewa hakikar al'amari shine cewa alheri yana wurin wanda yake da wadannan abubuwa na ma'anawiya, wato hakuri ilimi, mutum bai gushewa cikin zantukansa da ayyukansa yana mai kyawunta aiki, wannan wata ni'ima ce mai girma da yakewa Allah godiya kanta da yaba masa, idan kuma ya kasance mai munana aiki, sai ya nemi gafarar Allah ya tuba zuwa gareshi, shi ya kasance tsakankanin godiya da neman gafara. Allah yace:

  • «فعل الخير ذخيرة باقية وثمرة زاكية».

  • Aikin alheri wani tanadi wanzazze ribace tsarkaka

  • قال الإمام الحسن  7: «الخير الذي لا شرّ فيه : الشكر مع النعمة ، والصبر على النازلة

  • Imam Hassan (as) yace: alherin da babu sharri cikinsa shine: godiya tareda ni'ima, hakuri kan musiba da ta suka kan mutum

  • وقال  7: «العلم رأس الخير كلّه ، والجهل رأس الشرّ كلّه» «من يزرع خراً يوشک أن يحصد خيراً».

  • Yace : shi ilimi shine jagoran dukkanin alheri, jahilci shine jagoran dukkanin sharri, dukkanin wanda ya shuka alheri yayi kusa ya girbi alheri.

  • قال أمر المؤمنين علي  7: «ما خير بخير بعده النّار، وما شر شر بعده الجنّة ، وكلّ نعيم دون الجنّة فهو محقور. وكلّ بلاء دون النّار عافية».

  • Sau da yawa tana kasancewa ka samu mutum yana da tarin `ya`ya da yawa da dukiya mai tarin gaske, sai ka samu cewa hakan bai zamanto masa alheri ba ka samu yana rayuwa a wulakance, haka akasin haka ka samu talaka futik babu `ya`ya amma yana rayuwa cikin alheri da farin ciki, ma'auni cikin sanin alheri da sharri shine shiga aljanna da fadawa wuta, wannan na nuni da alakar duniya da lahira

  • ربّنا آتنا في الدنيا حسنةً وخيراً، وفي الآخرة حسنةً وخيراً، وقنا عذاب النّار والشرور والأشرار، ونعوذ بک من شرور أنفسنا

  • Ya ubangijinmu ka bamu kyakkaywa da alheri a duniya da lahira, ka tseratar damu azabar wuta, muna neman tsarinka da sharrin kawukanmu

 

Tura tambaya