lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU

 

6- Sadik (a.s) ya ce: mata sun kasu zuwa kashi hudu: daga cikinsu akwai wadda cikin dakin ta tana rainon `da sannan tana jiran haihuwar wanda take dauke da shi aciki 2 kamammiya wadda take tare da alheri mai tarin yawa 3 mai munana halayya 4 misalinta wajen mijinta kamar misalin kwaron kaska.

da wannan hadisi mai daraja zamu san halayyar mata, mafi daraja cikinsu ita ce wadda a dakinta tana halin raino tana kuma jiran zuwan wanda take dauke da shi a ciki, hakan na ishara da yawaita zuriya.

sannan manzon Allah (saw) ya ce: kuyi aure ku hayayyafa ni zan yiwa al'ummu alfahari daku kai hatta da jiririn da akayi barinsa.

daga cikin mata akwai wadda ke kare karamcin mijinta da kame Kanta daga barin mazajen da ba muharramanta ba, hakika ta kasance mai tarin alheri da kyawun dabi'a, wadannan suna daga mataye masu daraja amma mai munin halayya tareda mijinta mai cutar dashi da ayyukanta da harshenta bata kare karamcinsa da dukiyarsa yayin fakuwarsa, wannan bala'i ne da musifa mai girma da ke dunkufar da iyali.

عن داود الكرخي,قال قلت لأبي عبد الله(ع): ان صاحبتي هلكت وكانت موافقة وقد هممت أن أتـزوج ,فقال:انظر أين تضع نفسك ومن تشركه في مالك وتطلعه على دينك وسرك وأمانتك, فان كنت لا بد فاعلا فبكر تنسب الى الخيروالى الحسن الخلق.

7 - An karbo daga Dauda Karaki ya ce:na cewa baban Abdullah (a.s) matata mai biyayya ta rasu na himmatu da son kara yin aure, sai imam ya ce: ka duba inda zaka sanya kanka da wadda zakayi tarayya da shi cikin dukiyarka da tsinkayar da ita kan addininka da sirrinka da amanarka, idan ya zama dole sai kayi auren to ka zabi budurwa da ta alakantu da alheri da kyawun dabi'a.

Wani mawaki ya rera baiti kan mata kamar haka:

Ku saurara su fa mata an haliccesu daban daban

cikinsu akwai wanda suke kamar ganima da kauna

cikinsu akwai wadanda suke kamar jinjirin wata idan ya yaye ga sahibinsa,

cikinsu akwai wadanda su duhu ne kawai

duk wanda ya nasarar samun salihan cikinsu zai azurta

wanda kuma ya yi kasgaro da rashin samun salihai ba zai taba samun tsaruwa ba.

wannan hadisi yana ya ye hakikanin mata da halayyar su da dabi'unsu cikin rayuwar aure, zamu rairaye da takaita bayani cikin wadannan `yan kalmomi masu zuwa:

1 mace mahallice ta da namiji saboda haka dole ne mahalli da zaka sanya kanka ya zama tsaftatacce har ruwa ya wanzu tsaftatacce.

2 mace abokiyar tarayyar rayuwa wadda ke tarayya da kai cikin dukiyarka.

3 mace taskar sirrika, zai yi kyawu mutum ya suturce zinariyar sa da matafiyar sa da tafiyar sa, kamar yadda ya zo cikin hadisi, kamar yanda ake neman taimako kan ayyuka da boye sirrika, duk wanda ke neman aboki dole ne ya nemi wadda ba za ta ha'intarsa ba  cikin amanarsa da kiyaye masa sirri da mazhaba da addini, domin al'amarin yadda yake tana iya yiwuwa ya wayi gari cikin hukumar wani sarki azzalumi da yake bukatuwa da ya boye akidarsa daga wannan sarki  idan matarsa ta zamanto ba amintacciya ba to tabbas zata iya tona masa asiri da zama sanadiyyar fadawarsa hannun wannan sarki azzalumi, hakama idan ta kasance jahila doluwa.

Mafi alherin mata budurwa, hakika ita budurwa tana daga ahalin alheri da ihsani da kyawun hali.

عن أمير المؤمنين(ع): تزوج عيناء سمراء عجزاء مربوعة, فان كرهتها فعلي الصدق.

8-Sarkin muminai aliyu dan abu dalibi (a.s) ya ce: ka auri mace wadda launin idonta ya ke baki, sannan launinta wankan tarwada matsakaiciya, idan kaji batai maka ba ba ka sonta toni zan biya sadakinta.

 عن أمير ألمؤمنين(ع): من أراد الباء فليتزوج بامرأة قريبة من الأرض بعيدة ما بين المنكبين سمراء اللون, فان لم يحظ بها فعلي مهرها.

9 - An karbo daga sarkin muminai Aliyu (a.s) dukkanin me son wadata ya auri mace makusanciyar daga kasa, mai fadin tsakankanin kafadu, launinta wankan tarwada, idan ya zamanto bai samu wadata ba to sadakinta yana wuya na.

من أمالي الشيخ أبي جعفر بن بابويه ، عنه (عليه السلام) ، قال  : عقول النساء في جمالهن ، وجمال الرجال في عقولهم

10 - Daga littafin Amali Saduk ya ce: hankulan mata na cikin kyawunsu sannan kyawun maza na cikin hankulansu.

Hankali kyautace ce da Allah ya baiwa maza da mata da wannan hankaline ya kallafa hukunce hukuncen shari'a, sannan shi hankali ya karkasu zuwa kashi kashi daban daban, daga ciki akwai hankalin al'adu da zamantakewa da na siyasa wanda da shi ne mutum ke gudanar da rayuwar zamantakewa da siyasa, misalin wannan hankali mai zartarwa da gudanarwa shi ne da farko Allah sanya shi cikin maza  a kansa ne Allah ya dorawa maza wasu nauye nauye sai ya zamanto hankulansu sun yi galaba kan soyayya da tausayi, sabanin mata wanda saboda rainon kananan yara da tarbiyantar dasu da bukatuwar yaran ya zuwa tausayi da kauna daga uwa  fiye uba, sai Allah matsarkaki ya sanya musu tausayi da so suyi galaba kan hankalinsu.

Wannan shi ne ma'anar fadin: (namiji ke kammala mace) (mace ke kammala namiji) kowanne daya daga cikinsu na da bukatuwa ya zuwa dayan don samar iyali tabbatattu masu tsari da nasara cikin rayuwa. cikin wannan fage muna iya cewa dayan cikinsu bai fifici daya ba da wata falala.

Kowannensu idan yayi aiki da nauyin da aka dora a wuyansa to shi ne mafifici babu banbanci cikin kasantuwarsa namiji ko mace, hakika mafi daraja cikinku shi ne wanda ya fi kowa tsoran Allah.

Kyautar hankali ga da namiji ba ya nufin fifikon sa kan `ya mace, kyawun `ya`ya maza na cikin hankulansu saboda suna ajiye abubuwa a muhallinsu rayuwa ta kasance cikin arziki da kyawu, hankulan `ya`ya mata na cikin kyawunsu, kyawunsu na da kaso mai fadi cikin rayuwar da namiji da hutun zukata, kyawunsu fadinsa ya game zahiri da badini, jigo shi ne mace ta zamanto da ka kalleta ta faranta maka da kyawawan halayenta da kyawunta na badini koda kuwa ta rasa kyawan zahiri.

كان رسول الله (صلى الله عليه وآله) إذا أراد أن يتزوّج امرأة بعث إليها من ينظر إليها ، وقال  : شمّ ليتها ، فإن طاب ليتها طاب عرفها ، وإن درم كعبها عظم كعثبه

11- manzon Allah(saw) ya kasance idan yay i nufin yin aure sai ya tura wanda zai duba masa ita gareta ya ce masa ka sansana wuyanta idan yayi dadi to lalle kamshinta zai dadada. Sannan ka duba idan diddigenta ya yi kauri to za ta yi ni'ima.

قال عليّ بن الحسين (عليه السلام)  : خير نسائكم الطيّبة الريح ، الطيّبة الطعام ، التي إن أنفقت أنفقت بمعروف ، وإن أمسكت أمسكت بمعروف ، فتلك من عمّـال الله ، وعامل الله لا يخيب ويندم

12 - Aliyu dan Husaini (a.s) ya ce: mafi alheri matanku masu daddadan kamshi daddadan abinci, wadda idan zata ciyar tana ciyarwa da ma'arufi, idan za ta hana tana hanawa da ma'arufi, wadancananka na daga cikin hadiman ubangiji hadimansa basa tozarta da nadama.

Wannan hadisi na ishara zuwa hakika mabayyaniya, shi ne cewa ba'arin mata rundunar ubangiji hadimansa, mai ya fi girma daga wannan mace da ta ke danganewa ga Allah matsarkaki, ta kasance hadimarsa bisa kasa wadda ke da wadannan siffofi, tare da kasantuwa mai daddadan kamshi da abinci kari kan haka kuma idan ta ciyar tana ciyarwa da ma'arufi ba tare da barna da almubazzaranci ba  idan ta kame tana kamewa da ma'arufi ba tare da takaitawa ba,  ai ita ta kasance matsakaiciya cikin ciyarwarta da kamewa, to irin wadannan mata na daga hadiman Allah akan kasa, a bayyane ya ke cewa hadimin Allah akan kasa bai tozarta da nadama  cikin rayuwarsa da ayyukansa, domin abin da ya aikata ya kasance daga hikima da hankali da iya gudanarwa, misalin wannan mu'amala ta ubangiji na da wasu siffofin daban.

فعن رسول الله (صلى الله عليه وآله) ، قال  : ألا اُخبركم بخير نسائكم  ؟ قالوا  : بلى . قال  : إنّ خير نسائكم الولود الودود الستيرة ـ  أي المستورة التي لا يراها الأجانب  ـ العفيفة ـ  في عرضها وكلامها وحياتها وحجابها  ـ العزيزة في أهلها ، الذليلة مع بعلها ـ  وهذان وصفان مهمّان في حياة المرأة ، فمن ذاقت العزّة في بيت أبيها ، وهذا يعني أنّ على الوالد أن يعزّ بناته فلا يحتقرهن لا سيّما أمام الأولاد الذكور ، بل يتعامل مع بناته بلطف وإحسان كما سنذكر تفصيل ذلك إن شاء الله  ـ فالمرأة التي كانت عزيزة في بيت والدها ، لا تبيع الغالي مع زوجها ، بل تأخذ جانب الذلّة يعني التواضع والرفق مع بعلها ، وكلّما ازدادت تواضعاً لبعلها أحبّها وأكرمها وأعزّها ودافع عنها وصانها من كلّ حادث ، أمّا إذا تكبّرت وشمخت على بعلها ، فإنّه يستصغرها ويستحقرها ولا يعيرها أهمية ، بل يفوّض أمرها إليها ، وربما يخذلها ليثبت لها أ نّها ضعيفة في الحياة ، ومن ثمّ تنهدم حياتهما المشتركة ، فلا يكون الزوج حينئذ شريك الحياة المدافع والناصح

13 -An karbo daga Manzon Allah (saw) ya ce : yanzu bazan baku labari da mafi alheri cikin matanku ? sai suka ce  na'am,  ya ce : mafi alherin matanku ita ce mai haihuwa mai nuna kauna suturtacciya wadda baki  basa ganinta, kamammiya cikin mutuncinta kalaminta  rayuwarta da hijabinta, madukakiya cikin ahalinta  kaskantarta idan tana tare da mijinta, wadannan siffofi biyu na karshe siffofi ne muhimmai cikin rayuwar mace, duk wadda ta dandani daukaka a gidan mahaifinta hakan na nufi mahaifi ya darajanta `yarsa  ka da kuma ya dinga wulakantata musammam ma gaban kananan yara maza, bari ma dai ya kamata ya dinga mu'amala da `ya`yansa mata da tausayi da kyautatawa da sannu zamu kawo bayanin haka dalla dalla insha'Allah .

Macen da ta kasance mai daraja da daukaka gidan mahaifanta bata tsaurarawa ga mijinta tana mu'amala da shi cikin kaskantar da kanta gabansa, duk sanda  ta karu da tawali'u ga mijinta shi kuma zai kara santa ya karramtata da mutunta ya zama garkuwa gareta daga dukkanin abin da zai iya cutarta da ita, amma idan ta zo da girman kai da takabburanci tayi dagawa ga mijinta tabbas mijinta zai kaskantar da ita da wulakanta ta bazai bata wani muhimmanci ba, zai barta da al'amarinta, daga nan rayuwarsu ta tarayya shi da ita zata fara rugujewa, mijinta ba zai taba zama abokin tarayyarta ba garkuwarta mai nasiha.

ثمّ قال الرسول الأعظم (صلى الله عليه وآله)  : « المتبرّجة مع زوجها الحصان على غيره

Manzon Allah (saw) ya ce: itace mai tabarruji tare da mijinta mai kame kanta ga bare.

Abin nufi da tabarruji nan shi ne kwabe dukkanin kayan jikinta don motsa sha'awar mijinta su dandani dadin junansu da more rayuwarsu ta aure, kada ta yi ganganci katange kanta daga barinsa ta yi tunanin cewa zata fi samun girmamawarsa, kamar yadda mata suka saba zantawa da junansu kan hakan da cewa kada ki saurin mika kanki da sallamawa  mijinki abinda ke tare da da ke, sam sam al'amarin ba haka ya ke ba manzon Allah (saw) ya fi kowa sanin hakikani da ainahin rayuwar aure mai kwanciyar hankali arzuki da nasara  waccan da take kaskanatar da kanta gaban mijinta haka shi ma mijin ya zama wajibi gareshi kiyaye hakkokinta  da kauce abinda zai kawo bacin ranta

misalin wannan mata ana kidayata bayan muslunci daga mafi darajar fa'idoji  da mafi cikar ni'ima, babu mai samu irin wannan mata sai ma'abocin rabo mai girma , mai yafi kyawu daga kasantuwar mutum ya rayu tare da ma'aiki daga masu aiki don Allah, ta san dukkanin abin da ya wajaba kanta tana kuma sauke nauyin dake kanta, kamar yadda ta kasance tana magana da mijinta da kalmomin da zasu yardar da ubangijnta, sai ta samu lada mai girma da matsayi madaukaki  aljanna da aka tanadarwa masu takawa daga maza da mata.

قال الإمام الصادق (عليه السلام)  : ما استفاد امرئ بعد الإسلام أفضل من زوجة مسلمة ، تسرّه إذا نظر إليها ، وتطيعه إذا أمرها وتحفظه إذا غاب عنها في نفسها وماله

14-Imam Sadik (a.s) ya ce: Mutum bai fa'idantu da wata fa'ida bayan muslunci fiye da mata musulma wadda kallonta ke sanya masa farinciki, me biyayya idan ya umarce ta, mai kiyaye masa alfarma cikin kanta da dukiyar sa yayin da ya faku gabarinta.

جاء رجل إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال  : إنّ لي زوجة إذا دخلت تلقّتني ، وإذا خرجت شيّعتني ، وإذا رأتني مهموماً قالت  : ما يهمّك ، إن كنت تهتمّ لرزقك  فقد تكفّل به غيرك ، وإن كنت تهتمّ بأمر آخرتك فزادك الله همّاً ، فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : بشّرها بالجنّة ، وقل لها  : إنّك عاملة من عمّـال الله ، ولكِ في كلّ يوم أجر سبعين شهيداً ، وفي رواية  : إنّ لله عزّ وجلّ عمّـالا ، وهذه من عمّـاله ، لها  نصف أجر الشهيد . وأجر الشهيد كما ورد في الخبر الشريف عظيم جدّاً ، فإنّ الشهداء أحياء عند ربّهم يرزقون ، فرحون بما آتاهم الله من فضله ، وما أن تسقط القطرة الاُولى من دمه على الأرض إلاّ غفر الله له كلّ ذنب أذنبه ويدخله الجنّة بغير  حساب .

15-wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (saw) ya ce: ina da wata mata idan na shigo gida sai tayi sauri ta tarbeni, idan kuma na fito daga gidan sai ta rakani, idan taganni cikin damuwa sai tace mai ya saka cikin damuwa, idan ka kasance kana damuwa saboda arzikinka to waninnka ya dauke nauyinsa, amma idan ka kasance kana damuwa ne saboda lahirarka to Allah ya kara maka damuwa, sai manzon Allah (saw) ya ce: kayi mata bushara da aljanna, kace mata ke ma'aikaciya ce daga ma'aikatan Allah, kuma cikin kowacce rana kinada ladan shahidi saba'in 70, a wata riwayar : Allah mai girma da dauka  na da ma'aikata wannan mata na daga cikinsu, ta nada rabin ladan shahidi  sannan shi ladan shahidi kamar yadda ya zo cikin riwaya mai daraja yana da girma matuka, hakika su shahidai rayayyu wajen ubangijinsu ana azurtasu, suna farin ciki da abin da Allah ya basu daga falalar sa  digo daya daga jinin shahidi bai sauka kasa face Allah ya gafarta masa dukkanin zunubin sa da ya aikata,  kuma ya shigar dashi aljanna ba tare da hisabi ba.

maisalin wannan mace mumina wadda ke taimakom mijinta cikin duniyar sa da lahirar sa za ta kasance cikin hadiman Allah kuma ta samu ladan shahidi saba'in, sannan tafi kyawu da falala daga matan aljanna.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : الخيرات الحسان من نساء أهل الدنيا هنّ أجمل من الحور العين

16 - An karbo daga Imam Sadik (a.s) ya ce: mafi alherin kyawawa daga matan duniya, sun fi kyawu daga matan aljanna.

misalin wannan mata mala'iku na musu bushara da aljanna, kuma suna shigar dasu cikin aljanna ta kofar da suke so.

عن جابر ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إذا صلّت المرأة خمسها ، وصامت شهرها ، وأحصنت فرجها ، وأطاعت بعلها ، فلتدخل من أيّ أبواب الجنّة شاءت

17 -daga Jabir ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: idan mace tayi salloli biyar na farilla ta azumci watan Ramadan ta kiyaye farjinta tayi biyayya ga mijinta, to za ta shiga aljanna ta dukkanin kofar da take son shiga.

wani wajen kuma ya ce: dukkanin matar da ta taimaki mijinta kan aikin hajji da jahadi ko kuma neman ilimi, Allah zai bata lada misalin wanda ya baiwa matar Annabi Ayuba (a.s)

hakika matar annabi ayuba ta kasance mai hakuri wadda har Allah ya buga misali da hakurinta, hakika Allah ya yi alkawarin aljanna ga masu tsoronsa wadda fadinta ya kai misalin fadin sama da kasa.

daga cikin abubuwan da ke sanya rayuwar aure ta zama rayuwa me cike da arziki shi ne yin hakuri da danne fushi, bari ma dai mace ta narke cikin abin da mijinta ke so, su hada hannuwan juna don warware matsaltsali da wahalhalun yau da gobe.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : أي امرأة أعانت زوجها على الحجّ والجهاد أو طلب العلم ، أعطاها الله من الثواب ما يعطي امرأة أيوب (عليه السلام

Manzon Allah(saw) ya ce: dukkanin matar da ta taimaki mijinta kan zuwa aikijn hajji ko neman ilimi, Allah zai b ata irin ladan da ya baiwa matar Ayyuba (a.s).

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : خير نسائكم التي إن غضبت أو اُغضبت قالت لزوجها  : يدي في يدك ، لا أكتحل بغمض حتّى ترضى عنّي .

19- An karbo daga Imam Sadik (a.s) ya ce: mafi alherin matayenku ita ce wadda idan ran mijinta ya baci ko kuma aka bata masa rai sai ta cewa da mijinta: hannuna na kan hannunka bazan rintse idona inyi barci ba har sai ka yarda dani.

 babban burinta shi ne ta yardar da mijinta saboda tasan cewa yardar Allah na karkashin yardar miji, cikin kasancewarsa mumini salihi mai son abin da Allah ya ke so.

Ya zama wajibi ga mumini ya zabi mace mafi alheri, haka suma mata su zabi namiji nagari mafi alherin cikin mazaje, hakika tsarkakakkun mazaje na ga tsarkakakkun mataye, munanansu na tare da munanan mata, dukkanin jinsi na karkata ya zuwa jinsin sa, tare da haka Imamai (a.s) sun yi ishara game da nau'in mataye da kashe kashen su da tasirinsu kan `ya`ya da siffofin su.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : الشجاعة لأهل خراسان ، والباءة في أهل البربر ، والسخاء والحسد في العرب ، فتخيّروا لنطفكم

20- An karbo daga imam sadik (a.s) ya ce: jarumta ta na wurin mutankurasan, karfin jima'i na ga ahalin barbar. kyauta da hassada na wurin larabawa, kuyi zabe saboda kwayar digon maniyyinku.

عن الصادق ، عن أبيه (عليهما السلام) ، قال  : ما أفاد عبد فائدة خيراً من زوجة صالحة إذا رآها سرّته ، وإذا غاب عنها حفظته في نفسها وماله[1]

21-Imam sadik(a.s) ya ce: Mutum bai fa'idantu da wata fa'ida ba da mafi alheri daga mata saliha wadda kallonta ke sanya masa farinciki, me biyayya idan ya umarce ta, mai kyaye masa alfarma cikin kanta da dukiyarsa yayin da faku gabarinta.

عن الصادق ، عن أبيه (عليهم السلام) ، قال  : إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) قال  : إنّ من سعادة المرء المسلم أن يشبهه ولده ، والمرأة الجملاء ذات دين ، والمركب الهنيء  والمسكن الواسع[2]

22- Manzon Allah (saw) ya ce: hakika yana daga cikin azurtar musulmi dansa ya yi kama dashi, da mace kyakkyawa mai rikon addini da abin hawa mani'imci da yalwataccen gida.

  قال أبو عبد الله (عليه السلام)  : ثلاثة هي من السعادة  : الزوجة المؤاتية ، والولد البارّ ، والرزق يرزق معيشة يغدو على صلاحها ويروّح على عياله .

23

23- ankarbo daga baban Abdullah (a.s) ya ce: ariziki uku ne: mace mai mika wuya, da mai biyayya, azurtuwa da rayuwa da zai wayi gari kan gyara ta da kyautatawa iyalin sa.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : الدنيا متاع وخير متاعها الزوجة الصالحة  

24 - manzon Allah (saw) ya ce: duniya wani dan dadi ne mafi alherin dadinta mace saliha tagari.

وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّـنَا هَبْ لَـنَا مِنْ أزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا قُرَّةَ أعْيُن وَاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إمَاما[3] 

(ubangiji ka bamu sanyi ido daga matayenmu da zuriyarmu ka sanya mu masu tsoronka

25-Cikin mata akwai masu daraja da falala kamar yadda ya zo cikin alkur'ani mai girma:

 عَسَى رَبُّهُ إنْ طَـلَّـقَكُنَّ أنْ يُـبْدِلَهُ أزْوَاجاً خَيْراً مِنْكُنَّ مُسْلِمَات مُؤْمِنَات قَانِتَات تَائِـبَات عَابِدَات سَائِحَات ثَـيِّـبَات وَأبْكَار[4]ا

mai yiwuwa idan ya sake ku ubangiji ya sauya masa da wasu matan mafi alheri daga gareku musulmai, muminai, masu tawali'u masu tuba, masu azumi, da `yan mata da zawarwari.

 عن الرضا (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : خير نسائكم الخمس . فقيل  : وما الخمس  ؟ قال  : الهيّنة الليّنة المواتية التي إذا غضب زوجها لم تكتحل بغمض ـ  أي لا تنام  ـ حتّى يرضى ، والتي إذا غاب زوجها حفظته في غيبته ، فتلك عاملة من عمّـال الله ل[5]ا

26 -daga Imam rida (a.s) daga babannin sa (a.s) ya ce: sarkin muminai Aliyu dan Abi dalibi (a.s) ya ce:  mafi alheri cikin matayenku guda biyar ne: sai aka tambaye shi su waye biyar din? sai ya ce : mai saukin kai, mai mika wuya wadda idan yana cikin bacin  rai ba ta iya barci har sai ta kwantar masa da hankali, wadda idan ya yi tafiya zata kare shi halin tafiyarsa, to wannan mata tana daga cikin hadimai daga hadiman Allah da basu tabewa.

23 - daga Abdullah dan sinan daga ba'arin sahabbanmun, ya ce: naji baban Abdullah(a.s) ya na cewa: mace ba komai bace face misalin sarkar wuya, ka duba sarkar da za ka rataya.

24- Manzon Allah (saw) ya ce: mafi alherin mata wadanda suka hau rakumi sune matan kuraishawa mafi kauna da tausayin miji.

25- manzon Allah (saw) ya ce: na haneku da furen juji, sai aka tambayi manzon Allah(saw) wa cece furen juji? sai ya ce: kyakkyawar mace daga tushe mummuna.

 Shaik Saduk (rh) ya ce: abu Ubaida yana cewa an kira ta da furen juji saboda kamanceceniya da inda dabbobi keyin kashi da fitsari ma'ana turken dabbobi, waje da idan fure ya fito za ka ganshi gwanin sha'awa sai dai tushensa bai da kyawu.

عن عبد الله بن سنان ، عن بعض أصحابنا ، قال : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام)يقول  : إنّما المرأة قلادة ، فانظر ما تتقلّد ، وليس لامرأة خطر لا لصالحهنّ ولا لطالحهن ، فأمّا صالحتهن فليس خطرها الذهب والفضّة ، هي خير من الذهب والفضّة ، وأمّا طالحتهن فليس خطرها التراب ، التراب خير منه[6]

27-An karbo daga abdullahi dan sana an karbo daga ba'arin sabbanmu, ya ce: na ji baban Abdullah (a.s) ya na cewa: mace kamar sarkar wuya ce, saboda haka sai ka duba wadda ya kamata ka rataya, lalle mace ba ta da wani hatsari babu hatsari tare da salihansu haka ma azzaluman cikinsu. Amma salihan cikinsu hatsarinsu bai kasance daga azurfa ba ko zinariya ta fi azurfa da zinariya alheri. Amma azzaluman cikin su hatsarinta bai kasance turbaya ba domin turbaya ta fi zama alheri daga gareta.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : خير نساء ركبن الإبل نساء قريش ، أحناهن على زوج

28-Annabi (a.s) yace: mafi alherin mata da suka hau rakumi sune matan kuraishawa, mafi nuna tausayinyu ga miji.

وفي فقه الرضا (عليه السلام)  : واعلم أنّ النساء شتّى ، فمنهن الغنيمة والغرامة ، وهي المتحبّبة لزوجها والعاشقة له ، ومنهن الهلال إذا تجلّى ، ومنهن الظلام الحندس المقطبة ، فمن ظفر بصالحتهن يسعد ، ومن وقع في طالحتهن فقد ابتلي وليس له انتقام ، وهن ثلاث ، فامرأة ولود ودود تعين زوجها على دهره لدنياه وآخرته ، ولا تعين الدهر عليه ، وامرأة عقيمة لا ذات جمال ولا تعين زوجها على خير ، وامرأة صخّابة ولاّجة همّـازة تستقلّ الكثير ولا تقبل الكثير ، وإيّاك أن تغترّ بمن هذه صفتها ، فإنّه قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إيّاكم وخضراء الدمن . قيل  : يا رسول الله ، ومن خضراء الدمن  ؟ قال  : المرأة الحسناء في منبت سوء[7]

29- cikin Fikihu Imam Rida (a.s): ka sani lalle su mata daban daban ne cikinKu akwai ganima da kauna, ita ce mai son mijinta da nuna masa kauna, daga cikin akwai misalin jinjirin wata yayin da yaye, cikin su akwai dare mai tsanani duhu, duk wanda yayi damdagatar ya samu salihar cikin su zai yi farin ciki da azurta, wanda kuma ya gamu da lalatattun cikin su to lalle ya gamu da jarrabawa ba kuma zai samu daukar fansa ba. sannan sun kasha kasha uku , akwai mace mai yawan haihuwa mai yawan nuna kauna mai taimakon mijinta  duniyar sa da lahirar sa, ba ta cutar da shi, akwai kuma bakararriya wadda ba ta haifuwa  gashi kuma ba ta kyawu kuma ba ta taimakon mijinta kan aikin alheri, akwai kuma mai yawan raki da ihu mai yawan kutsawa mai ganin alheri mai yawa kadan ba ta kuma karbar, na haneka da ruduwa da mace mai wannan mai irin wanna siffa , hakika al'amarin yadda yak e  shine manzon Allah(saw) ya ce: na haneku da furen juji, sai ka tambayi Manzon Allah (saw) wacece furen juji? Sai yace: ita ce kyakkyawar mace daga mummunan tushe.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : تزوّجوا الأبكار ، فإنّهن أطيب شيء أفواهاً ، وأذرش أخلافاً ، وأحسن شيء أخلاقاً ، وأفتح شيء أرحاماً ، أفتح أنعم وألين .

 30-manzon Allah (saw) ya ce: ku auri `yan mata hakika su sun fi komai dadin ga baki da kyawun halayyya cikin abubuwa da ruwan nono da budewar mahaifa.

 wani wajen kuma ya ce: ku auri `yan mata hakika sune mafi dadin baki da rufewar mahaifa, da saurin daukar ilimi da tabbatar kauna.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : اختاروا لنطفكم ، فإنّ الخال أحد الضجيعين

31-Manzon Allah (saw): ku yi zabe don digon maniyyinku hakika kyawaun fuskar mata dayan abokin kwanciya ne.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : تزوّجوا السوداء الولود الودود ، ولا تزوّجوا الحسناء الجميلة العاقر ، فإنّي اُباهي بكم الاُمم يوم القيامة[8]

32 - Manzon Allah (saw): ku auri mace bakar fata mai haihuwa mai nuna kauna da soyayya, kar ku auri kyakkyawa bakararriya mara haihuwa hakika ni zan yiwa al'umma alfahari da ku ranar kiyama, ashe baku san cewa yara suna karkashin al'arshin ubangiji suna nemawa iyayensu gafara Annabi Ibrahim (a.s) ya na kula da su matar sa saratu kuma nayi musu tarbiya cikin wani dutse daga Almiski da Anbar da Za'afaran.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إذا أراد أحدكم أن يتزوّج المرأة فليسأل عن شعرها كما يسأل عن وجهها ، فإنّ الشعر أحد الجمالين[9]

34-Manzon Allah (saw) ya ce:  idan dayanku ya yi nufin aurar wata mace to ya yi tambaya game da gashinta da fuskarta, hakika gashi dayan kyawawa biyu ne.

عن فاطمة بنت الحسين ، عن أبيها الحسين بن علي ، عن أبيه عليّ ابن  أبي طالب (عليهم السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من اُعطي أربع خصال فقد اُعطي خير الدنيا والآخرة وفاز بحظّه منهما  : ورع يعصمه من محارم الله ، وحسن خلق يعيش به في الناس ، وحلم يدفع به جهل الجاهل ، وزوجة صالحة تعينه على أمر[10][11]

35- daga Fatima `yar Husaini daga babanta Husaini dan Ali daga baban sa Ali dan Abi dalibi (a.s) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: duk wanda aka baiwa abubuwa hudu hakika an bashi alherin duniya da lahira, sannan ya rabuta da babban rabo daga gare su: 1 tsantseni da ke kare shi daga zakkewa haramun, 2 kyawun halayya da zai rayuwa da ita cikin mutane, 3 hakuri da zai tunkude jahilcin jahili da shi, 4 mace saliha da za ta taimake shi cikin al'amarin duniya da lahira.

عن الصادق ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : حسن البشر نصف العقل ، والتقدير نصف المعيشة ، والمرأة الصالحة أحد الكاسبين .

36-daga imam sadik (a.s) daga babanninsa (a.s) manzon Allah (saw) ya ce: kyawun mutum rabin hankali, tsara rayuwa rabin rayuwa, mace saliha dayan masu nema.

عن ربيعة بن كعب ، قال  : سمعت النبيّ (صلى الله عليه وآله) يقول  : من اُعطي خمساً لم يكن له عذر في ترك عمل الآخرة  : زوجة صالحة تعينه على أمر دنياه وآخرته ، وبنون أبرار ، ومعيشة في بلده ، وحسن خلق يداري به الناس ، وحبّ أهل بيتي

37- daga rabi'atu dan ka'abu ya ce: naji Manzon Allah (saw) ya na cewa: duk wanda aka bashi abubuwa biyar bai da uzurin kan kin yin aiki don lahira: mace saliha da take taimakonsa kan al'amarin duniya da lahirarsa, da `ya`yaye nagari, rayuwa cikin garinsa, da kyawawan halaye da ya ke mu'amala tare da mutane da su, da soyayyar ahalin gidana.

نهج البلاغة  : قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : خيار خصال النساء شرار خصال الرجال  : الزهو والجبن والبخل ، فإذا كانت المرأة ذات زهو لم تمكّن من نفسها ، وإن كانت بخيلة حفظت مالها ومال بعلها ، وإذا كانت جبانة فرقت من كلّ شيء يعرض له[12]ا

38- nahjul balaga: sarkin muminai aliytu dan abi dalibi(a.s) ya ce: kyawawan halayyar mata sune munanan halayyar mazaje: girman kai tsoro, rowa, idan ta kasance ma'abociyar girman kai ce ba ta ba da kanta, idan kuma marowaciya ce za ta yi rowan dukiyarta da mijinta idan kuma matsoraciya ce to tana tsoron duk wani abu da za'a bijiro mata da shi.

روي عن أمير المؤمنين (عليه السلام) أنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) قال  : أخبروني أيّ شيء خيرٌ للنساء  ؟ فقالت فاطمة (عليها السلام)  : أن لا يرين الرجال ولا يراهن الرجال . فاُعجب النبيّ (صلى الله عليه وآله) وقال  : إنّ فاطمة بضعة منّي[13]

39- an riwaito daga sarki muminai Aliyu (a.s) cewa Manzon Allah (saw) ya ce : ku bani labari wane abu ya fi alheri ga mata? sai fatima (a.s) ta ce : ka da ta ga maza, mazaje kada su ganta, sai manzon Allah ya yi mamaki ya ce : Fatima tsokar jikina ce.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : خير نسائكم التي إذا دخلت مع زوجها خلعت درع الحياء  

40- Manzon Allah (saw) ya ce: mafi alheri mata itace wacce idan ta kebance da mijinta sai ta cire sulken kunya waje guda.

قال الصادق (عليه السلام)  : خير نسائكم التي إن اُعطيت شكرت ، وإن مُنعت رضيت

41- Sadik (a.s) ya ce: mafi alherin matayenku itace wacce idan aka bata sai ta yi godiya idan aka hana ta sai hakura ta yarda.

وقال (عليه السلام)  : خير نسائكم نساء قريش ألطفهن بأزواجهن ، وأرحمهن

بأولادهن ، المجون لزوجها ، الحصان لغيره . قلنا له  : وما المجون  ؟ قال  : التي لا تمتنع

42- mafi alherin matayen ku kuraishawa sune mafi ludufi ga mazajen su, mafi tausayin ga `ya`yan su, marasa kunya ga mijinta, sai muka ce masa me ye rashin kunya? ya ce: wadda ba ta hana masa kanta idan ya bukace ta.

عن الرضا (عليه السلام) قال  : من سعادة الرجل أن يكشف الثوب عن امرأة بيضاء

43 - daga Imam rida (a.s) ya ce: daga cikin arzikin mutum yaye tufafi ga barin farar mace.

عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : المرأة الجميلة تقطع البلغم ، والمرأة السوداء تهيّج المرّة السوداء

عن أبي عبد الله (عليه السلام) أ نّه شكى إليه البلغم فقال  : ما لك جارية تضحكك  ؟ قال  : قلت  : لا . قال  : فاتّخذها فإنّ ذلك يقطع البلغم .

45- daga baban Abdullah (a.s) ya ce:  wani mutum ya kawo masa kukan ciwon majina, sai ya ce masa: shin ba ka da baiwa da za ta dinga saka dariya, sai mutumin ya ce: babu, sai ya ce masa ka nemi baiwa saboda hakan zai kawo karshen ciwon.

الفقيه بسنده ، قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : الناجي من الرجال قليل ، ومن النساء أقلّ وأقلّ ، قيل  : ولِمَ يا رسول الله  ؟ قال  : لأ نّهن كافرات الغضب ـ  أي عند الغضب تكفر بالنعم وبفضل الزوج  ـ مؤمنات بالرضا

46- Alfakihu: da isnadin sa Manzon Allah (saw) ya ce: masu tsira daga maza kadanne sannan kuma sun fi karantuwa cikin mata, sai aka tamabayi annabi menene ya sanya hakan?" sai ya ce: saboda su mata suna da butulci da kafirci yayin da suke cikin fushi ne, ma'ana suna kafircewa ni'ima da falalar miji yayin da suke cikin fushi, sannan su muminai ne cikin halin yarda da kwanciyar hankali.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّما مثل المرأة الصالحة مثل الغراب الأعصم الذي لا يكاد يقدر عليه ، قيل  : وما الغراب الأعصم الذي لا يكاد يقدر عليه  ؟ قال  : الأبيض إحدى رجليه

47- Manzon Allah (saw) ya ce: misalin mace saliha misalin hankakan da ke da wuyar samu ne, sai aka tamabyi shi wane hankaka ne haka? sai ya ce: shi ne wanda kafar sa daya ta ke fara.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) أ نّه قال لامرأة سعد  : هنيئاً لكِ يا خنساء ، فلو لم يعطكِ الله شيئاً إلاّ ابنتكِ اُمّ الحسنين لقد أعطاكِ خيراً كثيراً، إنّما مثل المرأة الصالحة في النساء كمثل الغراب الأعصم في الغربان، وهو الأبيض إحدى رجليه

48- an karbo daga baban Abdullah (a.s) cewa ya cewa da matar Sa'ad: farin ciki gareki ya Hansa'u, ko da ace Allah bai baki komai ba face uwar hasanaini to da hakika ya baki alheri mai tarin yawa, hakika misalin mace saliha misalin hankaka mai wuyar samu ne cikin hankaki, shi ne wanda kafar sa daya ta ke fara.

عن الثمالي ، عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : كان في بني إسرائيل رجل

عاقل كثير المال ، وكان له ابن يشبهه في الشمائل من زوجة عفيفة ، وكان له ابنان من زوجة غير عفيفة .

             فلّـا حضرته الوفاة قال لهم  : هذا مالي لواحد منكم . فلمّـا توفّي قال الكبير  : أنا ذلك الواحد ، وقال الأوسط  : أنا ذلك ، وقال الأصغر  : أنا ذلك . فاختصموا إلى قاضيهم ، قال  : ليس عندي في أمركم شيء ، انطلقوا إلى بني غنام الإخوة الثلاث ، فانتهوا إلى واحد منهم فرأوا شيخاً كبيراً ، فقال لهم  : ادخلوا إلى أخي فلان فهو أكبر منّي فاسألوه ، فدخلوا عليه فخرج شيخ كهل فقال  : سلو أخي الأكبر منّي ، فدخلوا على الثالث فإذا هو في المنظر أصغر ، فسألوه أوّلا عن حالهم ثمّ مبيّناً لهم فقال  : أمّا أخي الذي رأيتموه أوّلا هو الأصغر وإنّ له امرأة سوء تسوؤه وقد صبر عليها مخافة أن يبتلى ببلاء لا صبر له عليه فهرمته ، وأمّا الثاني أخي فإنّ عنده زوجة تسوؤه وتسرّه فهو متماسك الشباب ، وأمّا أنا فزوجتي تسرّني ولا تسوؤني لم يلزمني منها مكروه قط منذ صحبتني ، فشبابي معها متماسك ، وأمّا حديثكم الذي هو حديث أبيكم ، انطلقوا أوّلا وبعثروا قبره واستخرجوا عظامه وأحرقوها ثمّ عودوا لأقضي بينكم . فانصرفوا فأخذ الصبيّ سيف أبيه وأخذ الأخوان المعاول ، فلمّـا أن همّـا بذلك قال لهم الصغير  : لا تبعثروا قبر أبي وأنا أدع لكما حصّتي ، فانصرفوا إلى القاضي فقال  : يقنعكما هذا ، ائتوني بالمال ، فقال للصغير  : خذ المال ، فلو كانا ابنيه لدخلهما من الرقّة كما دخل على الصغير

49- daga sumali daga baban Jafar (a.s) ya ce: cikin Banu Isra'ila akwai wani mutum mai hankali da tarin dukiya, ya na da wani da da ke kama da shi daga dabi'un matar sa mai kame kanta, sannan kuma ya na da wasu `ya`yan  daga matar sa mara kame kai, yayin da mutuwa ta zo masa sai ya ce musu : wannan dukiyar tawa na mallakawa daya daga cikinku, sai babban dansa ya ce: ni ne wanda ya ke nufi, sai na tsakiyarsu ya ce : ni ne, karamin cikinsu shi ma ya ce: ni ne, sai suka tafi wajen alkali don raba rigima da jayayyar da ke tsakaninsu, alkali ya ce bazan iya komai ba kan al'amarinku ku je wajen banu gannam wanda suma `yan'uwa ne uku, sai suka je wajen daya daga cikinsu sai suka same shi  tsoho ya ce musu: ku shiga wajen babban yayana, suka shiga wajensa sai suka ga wani tsoho tukuf ya fito, sai shi ma ya ce musu ku shiga wajen wanda yake babban yayana, su ka tafi wajensa sai kwatsam suka ganshi saurayi sai suka fara tambayarsa halinsa da`yan'uwansa sai ya yi musu bayani yana mai cewa: amma dan'uwana da kuka fara gani to shi ne karamin cikin mu ya kasance ya na da wata mata mai munana masa ya yi hakuri da ita don gudun ka da ya gamu da bala'in da ba zai iya hakuri kansa ba sai ta tsofaitar da shi, amma dan'uwana na biyu shi ma ya kasance ya na da wata mata da take faranta masa da munana masa lokacin da ya ke cikin tashen samartakarsa, amma ni na kasance ina da wata mata da ta ke faranta mini ba ta taba munana mini ko da sau daya ba tunda ta aure ni shi ya sa samartaka ta take tare da ita har yanzu, amma labarinku wanda shi ne labarin mahaifin ku da farko ku je kabarinsa ku tone shi ku fito da kasusuwan sa ku kona sannan ku dawo wajena zan yi hukunci tsakaninku, sai take suka juya cikin sauri wani dauke da takobi wani diga  yayin da suka himmatu da tone kabarin sai karamin cikinsu ya ce: kada ku tone kabarin babana ni zan bar muku kasona sai suka juya suka tafi wajen alkali, alkalin ya ce musu hakan ya wadatar muku, kuje ku kawo mini dukiyar, da suka kawo sai ya cewa da karamin karbi wannan dukiya ta kace, da `yan 'uwanka sun kasance `ya`yan mahaifin ka da tausayinsa ya shige su kamar yadda ya shiga cikin zuciyar karamin cikin su.

 mutum shi ne wannan halittar da bai gushe ba yana jahilci cikin mafi yawan iliminsa da duniyarsa, Allah ya halicce shi daga ruhi da jiki  ya cudanya hankali cikinsa wanda ke kiransa zuwa ga da'ar ubangiji, da zuciya mai yawan umarni da munana, ya kasance cikin kowanne lokaci ya na kokawa tsakanin gaskiya da karya, tsakanin alheri da sharri, tsakanin daraja da kaskanci, wannan ma'ana na gudana cikin mata kamar yadda ta ke gudana cikin maza, cikin mata akwai nagargaru masu alheri sannan akwai na banza miyagu da dukkanin siffofi da alamomi, ya zama wajibi kowa ya dage wajen tsarkake kansa ya nemi falala da halaye nagargaru, ya zage dantse cikin tsaftace zuciya daga miyagun siffofi, sannan ya yi mata ado da kyawawan siffofi da halaye nagargaru, sannan ya yaye ta har ya samu damar kaiwa ga kololuwar kamala.

Imamai (a.s) sun yi ishara zuwa ga miyagun mataye da dabi'unsu, kamar yadda ya zo cikin kur'ani mai daraja cikin kissoshin annabawa daga matayen annabi Nuhu da Ludu (a.s)

يَا أ يُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إنَّ مِنْ أزْوَاجِكُمْ وَأوْلادِكُمْ عَدُوّاً لَكُمْ فَاحْذَرُوهُم[14]ْ   

ya ku wadanda suka yi imani hakika daga cikin matayenku da `ya`yayenku akwai wadanda suke makiyanku saboda haka sai kuyi taka tsantsan da su. 

قال الإمام الصادق ع, أغلب الأعداء للمؤمن زوجة سوء

1- Imam Sadik (a.s): galibin makiya ga mumini ita ce muguwar mata.

Mace muguwa mai muguwar zuciya da dabi'a da mai mummuna kama ta na daga makiyan mumini, mai cutar da shi dare da rana hatta ya kai ga raba shi da hankalinsa saboda abin da ta ke dauke da shi daga karancin addini da kunya.

قال النبي ص : ما رأيت ضعيفات الدين ناقصات العقول أسلب لذي لب منكن

2 - Annabi (saw) ya ce: ban taba ganin masu raunin addini da nakasar hankula mafi raba ma'abocin hankali da hankalinsa ba kamar ku mata, misalin wadannan miyagun mata da ke hana mumini yin ibada kamar yadda ya ke buri yin ibadar.

قال رسول الله ص لولا النساء لعبد الله حقا

3- Manzon Allah (saw) ya ce: ba don mata ba da an bautawa Allah hakikanin bauta.

Hakika mata tarkon Shaidan ne, ya na amfani da su wajen halakar da mumini da jawo shi zuwa ga bata da karkata daga hanyar shiriya da yawa daga rigingimu cikin al'ummu sun samo tushe ne daga mace kamar yadda tarihi ke bamu labari.

1-      saboda misalin haka ne sarkin muminai Aliyu (a.s) ya bamu labari kan karshen zamani ya na mai cewa: zai bayyana cikin karshen zamani da kusantowar kiyama, shi ne mafi sharrin zamani, mataye masu tabarruji da nuna tsiraici daga addini, masu shiga fitina, masu karkata ga sha'awa, masu gaggawa ya zuwa dandanen dadi masu halasta haramun, za su kasance masu dawwama cikin jahannama. farkon karshen zamani zai fara daga karshen annabta da cikamakinta manzon Allah Muhammadu (saw) wanda ake kiransa da sunan annabin karshen zamani, duk sanda muka nesanci zamanin annanbta mu ka kusanci ranar alkiyama sai barna ta kara bayyana aban kasa da teku sai kaga ire iren wadannan mata na bayyana, su jagoranci al'umma ga tabarbara da bata da sha'awe sha'awe da jahilci da biyewa son holewa, maganin haka magani mai tsananin wahala shi ne suturce su.

قال (صلى الله عليه وآله)  : إنّ النساء غيّ وعورة ، فاستروا العورة بالبيوت ، واستروا الغيّ بالسكوت

5 - Annabi (a.s) ya ce: hakika mata bata ne da al'aura, ku suturce al'aura da gida, ku suturce batansu da yin shiru.

وقد مرّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) على نسوة فوقف عليهن ، ثمّ قال  : يا معشر النساء ، ما رأيت نواقص عقول ودين أذهب بعقول ذوي الألباب منكن ، إنّي قد رأيت أنّكن أكثر أهل النار يوم القيامة ، فتقرّبن إلى الله ما استطعتن ، فقالت امرأة منهن  : يا رسول الله ، ما نقصان ديننا وعقولنا  ؟ فقال  : أمّا نقصان دينكن فبالحيض الذي يصيبكن فتمكث إحداكن ما شاء الله لا تصلّي ولا تصوم ، وأمّا نقصان عقولكن فبشهادتكن ، فإنّ شهادة المرأة نصف شهادة الرجل  

6- wata rana Manzon Allah (s.a.w) ya wuce ta gefen wasu mata sai ya tsaya kansu ya ce: ya ku taron mata ban taba gani masu tauyayyen hankula da addini da ke tafiyar da hankulan ma'abota hankula fiye da ku ba, hakika na ga ku kuka fi kowa yawa cikin wuta ranar alkiyama, ku nemi kusanci da Allah gwargwadon iyawarku, sai daya daga cikinsu ta ce: ya manzon Allah, me ye tawayar addininmu da hankalanmu? sai ya ce: amma tawayar addininku na cikin haila dayan cikinku haila na risakarta ta kame daga sallah da azumi ila masha'Allah, amma tawayar hankulanku na tare da ba da shaidarku, hakika shaidar mace rabin ta namiji ta ke.

Daga cikin munin halin mace shi ne yiwa mijinta gori da dukiyarta idan ya kasance tana da ita.

 

قال النبي ص لو أن جميع ما في الأرض من ذهب وفضة حملته المرأة الی بیت زوجها, ثم ضربت علی رأس زوجها يوما من الأيام تقول:من أنت؟ انما المال مالي,حبط عملها لوكانت من أعبد الناس الا أن تتوب وترجع وتعتذر الی زوجها.

7- Annabi (saw) ya ce: da dukkanin abin da ke cikin kasa zai kasance zinariya da azurfa da mace ke dauke da shi zuwa gidan mijinta, sannan wata rana ta buga su kan mijinta, ta na cewa mijinta kai waye? dukiya dai tawa ce, to da dukkanin ayyukanta sun baci ko da kuwa ta kasance tafi kowa ibada cikin mutane har sai ta tuba ta koma ta nemi gafarar mijinta.

قال سلمان الفارسي (رضي الله عنه)  : سمعت رسول الله (صلى الله عليه وآله) يقول  : أيّما امرأة منّت على زوجها بمالها ، فتقول  : إنّما تأكل أنت من مالي ، لو أ نّها تصدّقت بذلك المال في سبيل الله لا يقبل الله منها إلاّ أن يرضى عنها زوجها

8-salmanu alfarisi (rd) ya ce: na ji manzon Allah (saw) ya na cewa: duk wata mace da ta yiwa mijinta gori da dukiyarta, ta na mai cewa kadai dai kai ai kudina ka ke ci, da ace za tayi sadakar dukkanin wananan dukiya to ubangiji ba zai karba ba daga gareta har sai mijinta ya yafe mata.

ya zama wajibi mutum ya zabi mace wadda ta ke daga tushe nagari daga dangi masu riko da addini mai lazimtar sanya hijabi da kula da addini, ka da ya takaitu da kyawunta na zahiri, duk da cewa babu mai kin kyawun zahiri amma kada ya gafala da kyawunn badini da kamewa da addini

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أ يّها الناس ، إيّاكم وخضراء الدمن . قيل  : يا  رسول الله ، وما خضراء الدمن  ؟ قال  : المرأة الحسناء في منبت سوء .

9- Manzon Allah (saw) ya ce: ya ku mutane na haneku da furen juji, aka tamabayi manzon Allah (saw) wacce mace ce furen juji? sai ya ce: kyakkyawar mace daga mugun tushe.

والمرأة السيّئة تشيب الرجل قبل أوانه ، ولمثل هذا كان النبيّ ـ  يدلّ على الاستمرار  ـ يقول في دعائه  : « اللهمّ إنّي أعوذ بك من ولد يكون عليّ ربّاً ـ  أي فوقي وحاكماً عليّ بمنزلة الربّ  ـ ومن مال يكون عليّ ضياعاً ـ  لا يعرف الإنسان كيف يتصرّف به حتّى يضيع عليه  ـ ومن زوجة تشيبني قبل أوان شيبي

             وهذا ما نشاهده ، فإنّ أكثر الشيب من الهمّ والغم ، فإنّ الهم يجلب الهرم ، والهمّ يكون تارةً من خلال الدَّيْن ، فإنّ الدَّيْن همّ ولو درهم ، واُخرى يكون من زوجة السوء وأولاد السوء ، فاسأل من كان شايباً قبل أوانه  ؟ لتقف على ما ندّعيه

10- mace muguwa na tsofaitar da mutum gabanin tsufan sa, kan misalin haka ne Manzon Allah ya yi ta ishara cikin addu'ar sa ( Allah ina neman tsarinka daga da `da zai kasance mini ubangiji – ma'ana zai dinga iko kaina kamar matsayin ubangijina, da dukiya da za ta zame mini bata – wacce mutum zai rasa yadda zai amfana da ita har ta bace daga ganinsa, da mata da za ta sani yin furfura kafin lokacin yin furfurata, wannan ne abin da mu ke gani yau hakika mafi yawan furfura na faruwa ne daga  yawan damuwa da bakin ciki, lalle yawan damuwa na jawo saurin tsufa, damuwa wasu lokuta na kasance sakamkon bashi da ake bin mutum, hakika bashi abin damuwa ne ko da kuwa dirhami daya ne, wasu lokuta kan kasancewa  daga muguwar mata da miyagun `ya`yaye, ka tambayi wanda ya yi furfura ya tsufa gabanin lokacinsu, da sannu zaka samu amsar abin da muke da'awa.

sannan samuwar `ya`ya cikin duniyar aure na daga ginshikan abubuwa wajen kasantuwar iyali da farin cikin su, ta nan ne muka sami karfafar auren mace mai haihuwa, da kuma wurgi da bakararriya wadda ba ta haihuwa.

قال النبي ص ذروا الحسناء عقيم وعليكم باسوداء الولود, فاني مكاثر بكم الأمم حتی بالسقط.

11-Annabi (a.s) ya ce: ku yi watsi da auren kyakkyawa bakararriya mara haihuwa, ku auri bakar fata idan ta kasance mai haihuwa, hakika ni zanyi wa al'ummomi alfahari da ku hatta da wanda akayi barin sa.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : ذروا الحسناء العقيم وعليكم بالسوداء الولود ، فإنّي مكاثر بكم الاُمم حتّى بالسقط

12- Annabi (a.s) : mummunar mace mai haihuwa ta fi alheri daga kyakkyawa mara haihuwa.

وقال ص اعلموا أن المرأة السوداء اذا كانت ولودا أحب من الحسناء عاقر.

13- Manzon Allah (saw) : ku sani cewa bakar mace mai haihuwa ta fi soyuwa gareni daga kyakkyawa mara haihuwa.

عن أمير المؤمنين ع , قال:سمعت رسول الله ص, يقول: أيما امرأة هجرت زوجها وهي ظالمة حشرت يوم القيامة مع فرعون وهامان وقارون في الدرك الأسفل من النار, الا أن تتوب أو ترجع.

14 - daga sarkin muminai Aliyu (a.s) ya ce : naji Manzon Allah (saw) ya na cewa : dukkanin matar da ta kauracewa mijinta tana halin zaluntar sa za'a tashe ta ranar kiyama tare da Fir'auna da Hamana da Karuna cikin karkashin wuta, har sai idan ta tuba ko kuma ta koma wajen mijinta.

Daga cikn miyagun dabi'u cikin ba'arin wasu mata shi ne dorawa mazajensu nauyin da ba za su iya dauka ba cikin abin da ya fi karfin ikonsa daga kayayyakin abinci da tufafin sawa ko dai wani abu daban

قال النبي ص: أيما امرأة أدخلت علی زوجها فی أمر النفقة وكلفته ما لا يطيقه,  لا يقبل منها صرفا ولا عدلا.

 15-Annabi (a.s) ya ce: dukkanin matar da ta dorawa mijinta abin da ya fi karfin sa cikin al'amari ciyarwa, Allah bazai karbi kyawawan ayyukanta ba face ta tuba ta janye ta dora masa wanda zai iya akwai wasu siffofin daban na miyagun mata.

 16 Annabi (saw) : yanzu bana baku labari da mafi sharrin matayen ku ba ? sai suka ce: na'am ya Manzon Allah bamu labari,  ya ce :mafi sharrin matayenku ita ce kaskantarta wajen danginda, mai nuna girma da darajar kanta wajen mijinta, bakararriya mara haihuwa mai kulle gaba wadda ba taka tsantsan da aikata miyagun ayyuka, mai tabarruji idan mijinta ya faku daga barinta, mai kame kai idan ya na tare da da ita  wadda ba ta jin maganar sa ba ta yi masa biyayya, idan ya kadaita da ita ya nemeta sai tayi masa taurin kai irin taurin kan taguwar da ba a taba daura mata igiya ba yayin da ake yunkurin hawa kanta, ba ta karbar uzurin sa  ba ta yafe masa laifin da ya yi mata .

Haka na nufin idan miji ya aikata kuskure to ya nemi afuwa, kamar yadda ya kamata ta karbi uzurin sa ta yi masa afuwa, kada ta ki yin hakan ta kafe kan hakkinta ta na mai neman yi masa ukuba kan laifin sa da miyagun dabi'unta.

 من كتاب روضة الواعظين ، قال الصادق (عليه السلام)  : شكا رجل إلى أمير  المؤمنين (عليه السلام) نساءه ، فقام خطيباً فقال  : معاشر الناس ، لا تطيعوا النساء على كلّ حال ، ولا تأمنوهن على مال ، ولا تذروهن يدبّرن أمر العيال ، فإنّهنّ إن تُركن وما أردن أوردن المهالك ، وعدون أمر المالك ، فإنّا وجدناهن لا ورع لهن عند حاجتهن ولا صبر لهن عند شهوتهن ، البذخ لهن لازم وإن كبرن ، والعجب بهن لاحق وإن عجزن ، لا يشكرون الكثير إذا منعن القليل ، ينسين الخير ويحفظن الشرّ ، يتهافتن بالبهتان ، ويتمادين بالطغيان ، ويتصدّين للشيطان ، فداروهنّ على كلّ حال ، وأحسنوا لهن المقال لعلّهن يحسن الفعال

17- daga littafin Raudatul Wa'izin, Imam sadik (a.s) ya ce: wani mutum ya kai kukan matar sa wajen sarkin muminai Aliyu (a.s) sai Imam ya mike ya na huduba ya ku taron mutane ka da biyewa matanku cikin kowanne hali, ka da ku aminta da su kan dukiyarku, ka da ku kyalesu su zamanto su ke tafiyar da al'amuran iyali, hakika idan aka kyale su da abin da suke so za su fada halaka, hakika mun same su ba sa yin tsantsaeni cikin bukatarsu, basu da hakuri yayin sha'awarsu, idan sun girma alfahari na zamar musu lazimi, idan sun tsufa sai jiji da kai ya riske su, basa yin godiya kan mai yawa idan an hanasu dan kadan  suna manta alheri su kiyaye sharri, suna daga murya da kage  suna kafewa da dagawa, suna karkata zuwa ga Shaidan. saboda haka ku bi su a hankula cikin kowanne hali, ku kyawunta musu kalami ta yiwu su kyawunta aiki.

Abin ban mamaki cikin wadannan kalamai na Imam Ali (a.s) hakika Imam ya ba da labarin hakikanin yadda mata suke mafi yawancin mata sun tattara wadannan siffofi da halaye, namiji mai hankali da lura ya zama wajibi ya san yaya yakamata ya yi mu'amala da matar sa sannan abubuwa da zamu fa'idantu cikin kalaman Imam (a.s) su ne kamar haka:

1- rashin biyewa mace cikin kowanne irin abu da kowanne hali (ka da ku biyewa mata cikin kowanne irin hali.

2- ka da a mika al'amarin kudi hannunta, ka da a aminta da ita kan dukiya, saboda da zarar ta san cewa mjinta na da kudi take za ta fara kawo bukatun ababen da take kwadayi da sha'awa marasa daraja da kima da ma'ana wadanda sayensu bai zama dole ba a rayuwance dukkanin mutum mai hankali ishara ta ishe shi (ka da ku aminata da su kan kudadenku)

3- ka da a bari su zamanto su ke tafiyar da sha'anin gida : hakika mai gida  aka sani da gudanar da al'amuran gida, shi ne wanda ke tsaye kan iyali, hakika mazaje sune masu tsayuwa kan mata, ya zama wajibi ga namiji ya tafiyar da sha'anin iyali cikin hankali da hikima  idan ba haka to hakika mace tauyayyace, nakasashe bai iya bayar da kamala, saboda wanda bai abu ta kaka zai kyautarsa, hankalin da ke shugabanci cikin iyali shi ne hankalin namiji mumini salihi, idan ba haka ba, da mace za ta kasance saliha mumina shi kuma mijinta fasiki fajiri, to irin wannan lokaci ba za'a mika al'amarin iyali ga hannusa ba, domi hakika zai kai su ya zuwa kwazazzabon bata da halaka   kamar yadda hakan ya ke bayyane amma idan ya kasance mutumin kirki mumini mai hankali to hakika babu shakka shi ne wanda zai tafiyar da gida, ba zai bar matarsa ta tafiyar da al'amarin gidansa ba  ( ka da a kyalesu da tafiyar da gida, dalilin haka shi ne ( idan aka kyalesu da dukkanin abinda su ke so za su gangara mahalaka )  hakika mace da dabi'arta da yanayin halittatra ta na da yawan karkata ga ababen dadi da sha'awe sha'awe da wuce iyaka, dalili kan haka shi ne hakika su basa yin taka tsantsan cikin bukatunsu basu da hakuri kan sha'awarsu, ya isheka hujja ka jarrabasu ka gani, hakka duk wanda ya jarraba haka zai yi nadama.

4 - tabarujji lazim ne gare su: hakika su suna kaunar rayuwar nuna ado su sayi abin da ran su ke so su sanya abin da suke so su ci abin da suke so ba tare da lissafi abin da suka kashe ba, ko da kuwa sun tsufa haka suke basa canjawa, idan kana son tabbatar da haka tambayi matarka lokacin da ta ke kokarin zuwa taron biki da makamancinsa tare da cewar ba ta san masu taron ba, zaka ka ga yadda suke sanya kayayyaki zamani nau'i nau'i daga takalma tufafi da sauransu ya zuwa masha'Allah.

5- jiji da kai da da ruduwa na riskar su: hakika su suna da ruduwa da jiji da kawukansu, wannan jiji da kai na riskarsu har tsufansu. babban masanin adabi harshen larabci malam shauki daifu ya na cewa: ta yaudaru da fadin cewa ke kyakkyawa ce    yabon mawaka ya rudar da ita.

6- basu da godiya : duk da kasantuwar godiya na daga dabi'ar da aka halicci dan adam da ita, sai dai abin ban mamaki ya yi karanci kaga mace na godewa mijinta ko da kuwa abin da ya ke ba ta na da yawa za ta dinga tunanin cewa ai tilashinka ne ka bata ko da ranka bai so  ko da ma sunyi godiyar ya isheka ace wata rana ka hana ta kadan nan ne fa za ka ga abin mamaki wani lokacin ka ga mijin na debe tsammani daga rayuwar aure, tare da cewa a baya ya bata dayawa amma don kawai ya hana kadan saboda wani yanayi da ya samu kansa ciki sai ka ga tana butulcewa dukkanin abin da ya yi mata a baya na daga alheri, hatta wasu lokuta za ka ji suna cewa : na zauna da kai shekaru da yawa amma mai ka tsinana mini, ni banga wani alheri cikin zamana da kai ba.

7- suna manta alheri: tsawon rayuwa aure kana ta yi mata hidima ba dare ba rana saboda aikata fadin Allah madaukaki:

وَعَاشِرُوهُنَّ بِالمَعْرُوفِ 

  ku yi zamantakayya da su da ma'arufi

  فَإمْسَاكٌ بِمَعْرُوف

ku rike da alheri.

  idan suka samu dan rashin jituwa da juna sai ta manta dukkanin alheri ta dinga tuna da dukkanin sharri, ta fito da takardar da ta ke rubuta laifukanka tsawon aurenku, take mijin zai gigice da fusata shaidan ya samu dama kansa ya fara tunanin sakinta da rabuwa da ita, misalin wannan mata ba ta amfanar da kai sai cutarwa, a gaskiya wannan shi ne hakikanin dabi'ar mata, mafi yawancinsu haka suke, baka da wata hanya da ta wuce kyautata zamantakewa da mu'amalarka da ita da mafi kyawu don cetar rayuwarta daga afkawa tsanantacciyar rayuwa

8- basu kunyar karya da kage: basu taka tsantsan daga karya da kage nan take za ka ga sun aikata haka matukar bukatarsu da abin da suke kwadayi ya hukunta yin hakan .

9- kafewa kan dagawa – saboda biyan bukatar su da sha'awe sha'awen su sai ka ga suna dagawa kan mazajen su, su kafe kan haka tsawon kwanaki watanni kai har shekaru ta ki sassautowa daga kan kalmarta ta karya ba saboda dagawa da takabburanci, ka ga ta kauracewa mijinta don zalunci da dagawa, hakika ranar kiyama za a tashesu tare da Fir'aunan Hamana da Karuna cikin karkashin wuta,  har sai ta tuba ta koma wajen sa ya yafe mata .

10 - suna karkata ga shaidan : hakika suna karkatar da fuskokin su zuwa shaidani, sai zamanto tarayyar shaidan, daga cikin mata akwai  hadiman Allah kamar yadda bayanin hakan ya gabata cikin darajantattun mata, daga cikin su kuma akwai hadiman shaidan da tarkon sa na halakar da mazaje, tare da wannan yanayi mai tsananin wuya babu wata dabara da ta ragewa maza face binsu a hankula da tafiyar da su cikin dabara da hikima da tausasa musu harshe me yiwuwa su canja daga munana zuwa salihai, Allah ne abin neman taimako, babu tsimi babu dabara face ga Allah madaukaki ma'abocin girma. 

Wannan ne gwargwadon abin da zamu iya kawowa kenan cikin zargin mata daga riwayoyi masu daraja, hakika mata basu taru duka sun zama bai daya ba cikinsu akwai nagari akwai miyagu, hadisan da suka gabata game da rashin amanar mata suna Magana ne kan wasu daga cikin su, tarihi ya shaida mana mata da suka kasance masu rikon amana da alkawali ga mazajen su .

أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَنَّهُ قَالَ: خَمْسٌ مِنْ خَمْسَةٍ مُحَالٌ النَّصِيحَةُ مِنَ الْحَاسِدِ مُحَالٌ وَ الشَّفَقَةُ مِنَ الْعَدُوِّ مُحَالٌ وَ الْحُرْمَةُ مِنَ الْفَاسِقِ مُحَالٌ وَ الْوَفَاءُ مِنَ الْمَرْأَةِ مُحَالٌ وَ الْهَيْبَةُ مِنَ الْفَقِيرِ مُحَال[15]ٌ

18- daga baban Abdullah (a.s) ya ce: abubuwa biyar daga mutane biyar basu yiwuwa har abada: nasiha daga mai hassada, tausayi daga makiyi, kiyaye alfarma daga fasiki, cika alkawali daga mace, kwarjini daga talaka.

19- namiji na neman tsari daga shaidan kamar yadda yake neman tsari daga sharrin miyagun mata.

 Manzon Allah (saw) ya ce : ku yi musu wa'azi da kyakkyawa tun kafin su yi maku umarni da mummuna, ku nemi tsarin Allah daga masharrantan su, sannan ku kasance cikin taka tsantsan daga nagarinsu.

    عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: لَا تُشَاوِرْهُنَّ فِي النَّجْوَى وَ لَا تُطِيعُوهُنَّ فِي ذِي قَرَابَةٍ إِنَّ الْمَرْأَةَ إِذَا كَبِرَتْ ذَهَبَ خَيْرُ شَطْرَيْهَا وَ بَقِيَ شَرُّهُمَا ذَهَبَ جَمَالُه

20-  daga baban jafar (a.s) ya ce : ka da ku shawarci mata cikin ganawarku ta sirri, ka da ku biye musu cikin al'amarin dan'uwanku hakika idan mace ta girma sai alherin gefanta biyu su ta fi sharrinsu su wanzu : kyawunta ya tafi.

 في نهج أمير المؤمنين (عليه السلام)  : المرأة عقرب حلوة اللسبة

21- Nahjul Balaga daga sarkin muminai Aliyu (a.s): mace kunama ce mai dadin harbi.

وقال (عليه السلام) بعد حرب الجمل في ذمّ النساء ـ  ويريد تلك المرأة التي خرجت عليه وأمثالها  ـ  : معاشر الناس ، إنّ النساء نواقص الإيمان نواقص الحظوط نواقص العقول ، فأمّا نقصان إيمانهن فقعودهن عن الصلاة والصيام في أيام حيضهن ، وأمّا نقصان عقولهن فشهادة امرأتين منهن كشهادة الرجل الواحد ، وأمّا نقصان حظوظهن فمواريثهن على الأنصاف من مواريث الرجال ، فاتّقوا شرار النساء وكونوا من خيارهن على حذر ، ولا تطيعوهنّ في المعروف حتّى لا يطمعن في المنكر([176])

 

22- bayani yakin Jamal Imam (a.s) cikin zargin mata ya na nufin waccan mata da ta fito yakar sa : ya ce ya ku mutane, hakika mata suna da tawayar imani da rabo da tawayar hankali, amma tauyewar imanin su  barin su sallah da azumin kwanakin al'adar su, amma tauyewar hankula kasantuwar shaida mata guda biyu matsayin shaidar namiji daya, amma tauyewar rabon su kasantuwar gadon su rabin na namji idan an kasafta, kuji tsoron masharrantan mata, ku kasance cikin lura da taka tsantsan daga salihan su, ka da ku biye musu cikin kyakkyawa don gudun kada suyi kwadayi cikin munkari, Allah matsarkaki na zargin mata kan kaidin su  acikin annabin Yusuf (a.s) daga bakin sarkin Misra, Allah matsarkaki ya ce:

إنَّهُ مِنْ كَيْدِكُنَّ إنَّ كَيْدَكُنَّ عَظِيم[16] 

  hakika kaidin kune lalle kaidinku na da girma

Dubi yadda kaidin su ke da girma dangane da mazaje, amma kaidin shaidan dangane da maza sai ya zamanto mai rauni , saboda Allah shi mai karfi da ke tallafawa muminai (suka shirya makirci , Allah ya yi musu sakamako da makircin su, Allah ne mafi Alherin masu sakawa makirci . saboda haka kaidin Allah na da karfi, kaidin shaidan rarrauna ne.

رَسُولَ اللَّهِ ص قَالَ: ثَلَاثَةٌ هُنَّ أُمُّ الْفَوَاقِرِ سُلْطَانٌ إِنْ أَحْسَنْتَ إِلَيْهِ لَمْ يَشْكُرْ وَ إِنْ أَسَأْتَ إِلَيْهِ لَمْ يَغْفِرْ وَ جَارٌ عَيْنُهُ تَرْعَاكَ وَ قَلْبُهُ يَنْعَاكَ إِنْ رَأَى حَسَنَةً دَفَنَهَا وَ لَمْ يُفْشِهَا وَ إِنْ رَأَى سَيِّئَةً أَظْهَرَهَا وَ أَذَاعَهَا وَ زَوْجَةٌ إِنْ شَهِدْتَ لَمْ تَقَرَّ عَيْنُكَ بِهَا وَ إِنْ غِبْتَ لَمْ تَطْمَئِنَّ إِلَيْهَا

23- an karbo daga Imam Sadik (a.s) daga babannin sa (a.s) Manzon Allah (saw) ya ce: abubuwa uku sune uwar makirci : basarake wanda idan ka kyautata masa ba zai  godiya kai ba , idan ka munana masa bai maka gafara , mokoci wanda idanun sa na gadinka zuciyar sa na fatan mutuwarka, idan ya ga wani abu mai kyawu daga gareka sai ya binne shi ba zai bari a gani ba, idan ko ya ga mummuna sai ya bayyana ya yada, mata wacce ganinta bai sanyaya maka ido, idan kai tafiya zuciyarka ba ta samun nutsuwa da ita.

Daga cikin wasiyyar Manzon Allah (saw) ga Imam Ali (a.s): abubuwa hudu masu karya gadon baya: shugaban da ke sabawa Allah kuma ake biyayye ga umarninsa, matar da mijinta ke kiyaye mata amana ita kuma ta ke ha'intar sa, talaucin da ma'abocinsa yarasa maganinsa, mugun makwabci cikin gidan da ka ke zaune.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله) لزيد بن ثابت  : يا زيد ، تزوّجت  ؟ قال  : قلت  : لا ، قال  : تزوّج تستعف مع عفّتك ، ولا تتزوّجن خمساً . قال زيد ، من هنّ يا رسول الله  ؟ فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : لا تتزوجن شهبرة ولا لهبرة ولا تهبرة ولا هيدرة ولا لغوتاً .

             قال زيد  : يا رسول الله ، ما عرفت ممّـا قلت شيئاً وإنّي باُخريهن لجاهل . فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ألستم عرباً  ؟ أمّا الشهبرة فالزرقاء البذيّة ، وأمّا اللهبرة فالطويلة المهزولة ، وأمّا النهبرة فالقصيرة الذميمة ، وأمّا الهيدرة فالعجوزة المدبرة ، وأمّا اللغوت فذات الولد من غيرك

24- Manzon Allah (saw) ya cewa Zaidu dan Sabit: ya Zaidu shin ka yi aure ? Zaidu ya ce a'a, sai Manzon Allah (saw) ya ce: masa ka yi aure za ka kare kamewa kan kamewar ka, kada ka auri daga nau'in mata biyar, zaidu ya ce su waye wadannan mata biyar ya Manzon Allah?  sai Manzon Allah (saw) ya ce: kada ka auri shahabara da lahabara da haidara da tahabara da laguta, sai Zaidu ya ce : ban san komai ba cikin abin da ka fada, lalle ni na jahilci kowacce daya daga cikinsu,  Manzon Allah (saw) ya ce: shin ku ba larabawa ba ne ? amma shahabara itace koriyar mace mai yawan kalaman alfasha, amma lahabara itace ramammiya mai dogon wuya, amma tahabara itace gajeriya mummuna, amma haidara ita ce tsohuwa, amma laguta itace matar da ta ke dauke da dan da ba naka ba.

قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص إِيَّاكُمْ وَ تَزَوُّجَ الْحَمْقَاءِ فَإِنَّ صُحْبَتَهَا ضَيَاعٌ وَ وُلْدُهَا ضیاعٌ

 25- Manzon Allah (saw) na haneku da wawiya hakika zama da ita tozartuwa ce, danta asara.

وقال (عليه السلام)  : شرّ نسائكم الجفّة الفرتع البافوق الفحاش ، وهو القتات ، والجفّة من النساء القليلة الحياء ، والفرتع العابسة

26- Manzon Allah (saw) na hane ku da mace tsagera mara kunya da mai turbune fuska.

Wannan sune jumla siffofin miyagun mata sai ayi kokari  aga an guje musu don gudun fadawa kaidinsu, Allah shi ne abin neman taimako.


[1] Biharul anwar m 100 sh 217

[2] Masdarin da ya gabata

[3] Furkan:74

[4] Attahrim:5

[5]Amali dusi m 1 sh 379

[6] Biharul anwar m 100 sh 234

[7]Masdarin da ya gabta

 

[8] Biharul anwar m 100 sh337

[9] Mandarin da ya gabata

[10] Masdarin da ya gabata sh 338

 

[12] Nahjul-Balaga m 3 sh 305

[13] Biharul anwar m 100 sh 239

[14] Attagabun:14

[15] Biharul-Anwar m 100 sh 225

[16] Yusuf:2

Tura tambaya