lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

NAU'UKAN HAJJI DA WASU BA'ARIN SIRRIKANSU

 

                                                                                                                               

A fili ya ke kamar yadda fikihun muslunci ya karkasa hajji zuwa kashi uku:

1- Hajji Ifradi: shine hajjin da ya wajaba kan mazauna garin Makka da gefenta da daura da ita har ya zuwa mil 48 haka ga wanda bai samu dacewa da umarar tamattu'i ba cikin lokacin ta ko kuma wani abu ya hana shi kammala hajjin tamattu'i, to a irin wannan hali sai ya canja daga hajjin tamattu'i zuwa hajjin Ifradi.

 

2- hajjin Kirani:  aikin hajji ne da yake wajaba kan mutanen Makka, za su riki abin hadaya tun daga mikatinsu.

 

3-  hajiin Tamattu'i: shine hajjin da ya wajaba kan wadanda suka nesanci makka da mil 48 shi ne mafi falala daga nau'o'in hajji a tarihinsa na komawa ga hajjin Manzon Allah(saw) wanda aka fi sani da hajjin bankwana wanda ya yi shi kasrhen rayuwar sa mai daraja bayan saukar fadin Allah madaukaki:

(وَأَذِّن فِي آلنَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوکَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ )[1]

Ka yi yekuwa cikin mutane don ibadar hajji za su zo maka suna masu tafiya da kafafunsu kan dukkanin dankwararren doki za su zo daga dukkanin rango mai nisa.

فخرج النبيّ في معشر المسلمين ... فخطب النبيّ

الأعظم  6 في المروة ، وأشبک بين أصابعه وقال : «دخلت العمرة في الحجّ كأصابع يدي بعضها في بعض[2]

 

Sai Annabi ya fito cikin taron musulmi ya yi huduba cikin Marwa sai ya hade yatsunsa biyu ya ce: na shigar da umara cikin hajji kamar misalin yatsun hannu na sashen su cikin sashe

Sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: yanzu zamu fito aikin hajji alhalin gashin kawukanmu na digar daruwa? Sai Manzon Allah ya ce masa kai ba zaka taba imani da ita ba bayanta har abada. Shi wannan mai fadin haka shi ne wanda ya haramta mutu'atul hajji bayan wafatin manzon Allah lokacin da ya samu halifanci bayan Abubakar.

الكافي بسنده عن معاوية بن عمّار قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : «الحجّ ثلاثة أصناف : حجّ مفرد وقران وتمتّع بالعمرة إلى الحجّ ، وبها أمر رسول الله6 والفضل فيها، ولا نأمر الناس إلّا بها».

Daga littafin alkafi mai daraja da isnadin sa daga Mu'awiyatu dan Ammar ya ce: na ji baban Abdullah (as) ya na cewa: lalle hajji sinfi uku ne: hajjin Ifradi da hajjin Kirani da hajjin da ake umara cikin sa gabanin tsayuwar Arafat da shi ne manzon Allah(saw) ya yi umarni sannan dukkanin falala na cikin shi, ba ma umartar mutane face shi.

وقال  7: «التمتّع أفضل الحجّ وبه نزل القرآن وجرت السنّة ».

Wani wajen kuma ya ce: hajjin Tamattu'i  shi ne mafi falala, shi kur'ani ya saukar sunna ta tafi kai.

وعن صفوان قال : قلت لأبي عبدالله 7 ان بعض الناس يقول جرد الحجّ وبعض الناس يقول أقرن وسُق ، وبعض الناس يقول تمتّع بالعمرة إلى الحجّ ، فقال : «لو حججت ألف عام لم أقرنها إلّا متمتّعاً».[3]

An karbo daga SUfwanu ya ce: na cewa baban Abdullah lalle ba'arin mutane suna cewa a kwabe hajji ayi ta zalla, wasu kuma na cewa ayi hajjin Kirani a kora hadaya, wasu kuma suna cewa ayi Tamattu'i da umara ya zuwa hajji (Hajjin Tamattu'i), sai Imam ya ce: da zan yi hajji sau dubu da bazan yi Kirani ba, hajjin Tamattu'i kadai zan yi.

وقال الامام الرضا 7 في سرّ حجّ التمتّع : «إنّما اُمروا بالتمتّع إلى الحجّ لأنّه تخفيف من ربّكم ورحمة ، لا يسلم الناس في إحرامهم ولا يطول ذلک عليهم ، فيدخل عليهم الفساد، وأن يكون الحجّ والعمرة واجبين جميعاً، فلا تعطّل العمرة ، وتبطل ولا يكون الحجّ مفرداً من العمرة ، ويكون بينهما فصل وتميز، وأن لا يكون الطواف بالبيت محظوراً، لأن المحرم إذا طاف بالبيت أحلّ إلّا لعلّة ، فلو لا التمتّع لم يكن للحاج أن يطوف ، لأنّه إن طاف أحلّ وأفسد إحرامه[4]

Imam Rida (as) cikin sirrin hajjin tamattu'i yana cewa: kadai dai an umarce su da hajjin tamattu'I saboda shi sauki ne da rahama daga ubangijinku, bai sallama mutane cikin ihramin su bai tsawaitawa kan su ta yadda barna za ta shiga kan su, da kuma kasantuwar hajji da umara wajibai baki dayan su, ka da ka bata umararka ta gurbata, ka da hajji ya kasance hajji ba tare da umara ba sai ya kasance tsakanin umara da hajji akwai wata fasila da banbanta, don gudun ka da dawafi ya kasance abin hani, saboda wanda ya daura harami idan ya yi dawafi zai warware haramin sa ne sai dai idan wata larura ta bijiro, ba da bon tamattu'I ba da mai hajji ba zai yi dawafi ba, saboda idan ya yi dawafi ya gama sannan kuma harami ya baci.

Sannan dole ayi cikkaken shiri da tanadi don hajji da guzuri da abin hawa da makamantansu daga share fage da shimfida zuwa ga hajji daga ciki akwai passport (katin izinin shige da fice)

 

قال الامام الصادق  7 لعيسى بن منصور: «يا عيسى اني اُحبُّ أن يراک الله عزّوجلّ فيما بين الحجّ إلى الحجّ وأن تتهيّأ للحجّ » . [5]

Imam Sadik (as) ya cewa Isa dan Mansur: ya Isa lalle ni ina kaunar ace Allah ya ganka cikin tsakankanin hajji zuwa hajji da kuma ace kayi shiri don hajji.

Daga wannan mafara ma daraja hadisi ya zo:

عن الامام الصادق  7: «لو أنّ أحدكم اذا ربح الربح أخذ منه شيء فعزله فقال : هذا للحجّ ، وإذا ربح أخذ منه وقال هذا للحجّ ، جاء أبّان الحجّ وقد إجتمعت له نفقة ، عزم الله فخرج ، ولكن أحدكم يربح الربح فينفقه فاذا جاء ابّان الحجّ ـ أي وقت الحجّ ـ أراد أن يخرج ذلک من رأس ماله فيشق عليه » . [6]

An karbo daga Imam Sadik (as):  da ace dayanku zai samu wata riba sai ya dibi wani kaso daga cikin ribar ya ce wannan kason na aikin hajji ne, haka ya kara samun wata ribar ya kara diban wani kaso ya aje don zuwa hajji, lalle lokacin aikin hajji zai zo masa yana da halin abin da zai je, zai shirya ya daura niyyar zuwa hajji domin Allah ya fita, sai dai cewa dayanku yana cin riba sai ya ciyar da ribar baki daya ba tare da ya aje wani abu daga ciki ba, ya yin da lokacin zuwa hajji ya gabato sai ya yi yunkurin cire abin da zai je hajji daga jarin sa uwar kudin da ya ke juyawa sai hakan ya tsananata gare shi ya gaza fitarwa.

Duk wanda ya ke da tunanin zuwa hajji zai tanadi guzuri da abin da zai kaishi hajjin tsawon shekara lalle babu shakka da kokwanto zaka same shi yana rayuwa cikin ma'anawiyya da mahajjaci ke rayuwa cikinta lokacin aikin hajji, Allah zai sanya albarka cikin rayuwar sa da dukiyar sa.

Daga cikin mabayyanin al'amari lalle shi karbabben hajji na kasancewa daga kudaden halal.

Idan wani mutum ya tsiwirwiri kudaden haramun ya tara su ya je hajji, idan ya ce: labbaika sai mala'iku su amsa masa da la labbaika wala sa'adaika ba a amsa kiranka ba, amma idan ya kasance daga kudaden halal idan ya ce labbaika sai a amsa masa da labbaika wa sa'adaika.

Lalle Allah matsarkaki ya na karbar aiki daga masu takawa, lalle shi kyakkyawan aiki na daga kyakkayawan mutum, duk wanda kudaden sa su kasance daga halal lalle hajjin sa ya kasance tsaftatacce karbabbe idan kuma sabanin haka ne to hajjin sa zai kasance wurgagge ya kuma wayi gari ukuba ga ma'abocinsa.

Sannan abin da yake farilla tun farko shi ne mutum ya  tanadi guzuri daga mafi kyawun abin da ke gareshi daga guzuri.

كان الامام علي بن الحسين  7 اذا سافر إلى مكّة للحجّ أو العمرة تزوّد من أطيب الزاد من اللوز والسكّر والسويق والحمّص والُمحلّى[7]

Imam Aliyu Ibn Husaini (as) ya kasance idan zai tafiya zuwa makka domin hajji da umara sai ya tanadi guzuri daga mafi kyawun guzuri daga gyadar luz da sukari da sawiku da waken himsi (chickpeas) da …….

Kai hatta mutumin da yi yi guzuri cikin guzuri ba a kidaya shi daga matafiyi

قال رسول الله 6: «ما من نفقة أحبّ إلى الله عزّوجلّ من نفقة قصدٍ ـأي الانفاق باقتصادـ، ويبغض الإسراف إلّا في الحجّ والعمرة.[8]

Manzon Allah (saw) ya ce: babu wata ciyarwa da tafi soyuwa ga Allah daga da matsakaiciyar ciyarwa, lalle Allah ya na kin wuce gona da iri face cikin hajji da umara.

Abin da ya fi zama farilla shi ne ciyarwar ta kasance mafi kyawunta da falala da tsaftata cikin tafarkin Allah kamar misalin hajji da umara da jihadi da makamantansu…..

 


[1] Hajji:27

[2] Wasa'ilul shi'a:juz 8 sh 151

[3] Alkafi:juz 4 sh 292

[4] Wasa'ilul shi'a:11 sh 232

[5] Alkafi: juz 4 sh 281

[6] Alkafi: 4 sh 280

[7] Alfakihu: juz 3 sh 382

[8]  Alfakihu: adireshin da ya gabata.

Tura tambaya