Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
KARIJUL FIKHU 11 GA WATAN RABI'U AWWAL SHEKARA 1441 CIKIN BAHASIN MUSTAHABBANCIN BAYYANAR DA BISMILLA CIKIN AZUHUR DA LA'ASAR 21
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 11 GA WATAN RABI'U AWWAL SHEKARA 1441 CIKIN BAHASIN MUSTAHABBANCIN BAYYANAR DA BISMILLA CIKIN AZUHUR DA LA'ASAR 21

Bahasi kan mustahabbancin bayyanar da karatun bismillar fatiha da sura

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami-tare da Samahatus-Assayid Adil-Alawi (H)

Lokaci: karfe 8 na safiya bahasin fikhu karfe 9 bahasin Usul

Cigaba kan bahasin da ya gabata kan mustahabbancin bayyanar da karatun bismillar fatiha da sura cikin sallolin Azuhur da Laa'asar kamar yanda mashhur suka tafi kan haka daga cikinsu akwai Akaramakallahu Almuhakkikul Hilli (K) bisa riko da fuskokin ijma'i da siratul mutasharri'a da jumlar riwayoyi kamar yanda bayani ya gabata, Shaik Saduk da Ibn Barraj da Abu Salahul Halabi sun tafi kan wajabcin bayyanarwa bisa rikonsu da riwayoyi guda biyu: ta farko wacce Alkulaini ya rawaito ta daga hanyar Sulaimu Ibn Kaisu daga Sarkin muminai Ali (a.s) cikin wata doguwar hudubarsa da cikinta yake cewa:

 (وألزمت الناس الجهر ببسم الله الرحمن الرحيم).

Na lazimtawa mutane bayyanar da karatun bismilla.

Ta biyu itace riwayar da Shaik Saduk ya rawaito cikin littafin Alkisal da isnadinsa daga A'amash daga Jafar Ibn Muhammad (a.s)

قال: والإجهار ببسم الله الرحمن الرحيم فيالصلاة واجب).

 bayyanar da bismilla cikin sallah wajibi ne.

Assayid Hakim ya na ganin raunin isnadin wadannan riwayoyi biyu da kuma kauarcewa da malamai sukai kansu, ba za a dogara kansu sai dai cewa Assayidul Ku'i ya tafi kan ingancin isnadin riwayar Sulaimu duk da cewa ya ganin raunin isnadin riwaya ta biyu, kadai yayi munakashar dalalar hadisan guda biyi cikin fuskoki:

Ta farko gamar karina wato shaida da kuma ka'idar (lau kana labana) da ace wajabci ya tabbatu kuma mas'alar tana daga wacce ake yawan fuskantar ta da hakan ya shahara ya kuma bayyana da yaduwa, ta kaka zai buya da yanayin babu wadanda suka Ankara da lura da shi sai iya wadannan malamai guda uku Shaik Saduk da Ibn Barraj da Abu Salahul Halabi.

Magana ta biyu: cikin riwayar Sulaimu babu wani abu da ya bayyana cewa abin da ake nufi da bayyanar da bismilla cikin dukkanin salloli hatta sallolin da ake boye karatu, hakika hikaito kaziyyar ce cikin waki'a da aikin Ma'asumi  amincin Allah ya kara tabbata a gare shibabu idlaki cikinta da har za ayi riko da shi da zai game sallolin boye karatu, ta yiwu abin da ake nufi daga bayyanarwa shi ne iyakar sallolin da ake bayyanar da karatunsu, sakamakon wadanda suka gabace shi daga shugabanni da sarakunan zalunci sun barta daga asalinta kai hatta cikin sallolin da kae bayyanar da karatunsu kamar yanda hakan shi ne abin da wadanda suka sabawa mazhbar Ahlil-baiti suke kai, sia ya umarce su da bayyanarwa domin kawar da bidi'a, ka lura sosai lallai barin bayyanar da bismilla ya kasance daga Mu'awiya Allah ya dawwamar da shi cikin wuta.

Ta uku: munakashar cikin dalalar riwayar A'amash, wajabci cikinta ya zo da ma'anarsa ta lugga wanda yake nufin tabbatuwa kamar yanda yake zuwa da ma'anar korewa kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukakin Sarki:

 (فإذا وجبت جنونها)

Idan geffanta suka fadi.

Koma bayan wajabcin na isdilahi wanda yake dauke da ma'anar rinjayen aiki tare da hani barinsa, saboda riwayar bata nuni da fiye da kan mustahabbanci da mudlakin rinjaye, ka lura.

Ta hudu: lallai riwayoyin biyu suna cin karo da ingantattun riwayoyi guda na Sufwan da suke bayyane kan mustahabbanci: ta farko:

قال: صليت خلف أبي عبد الله عليه السلام أياماً فكان يقرأ في فاتحة الكتاب ببسم الله الرحمن الرحيم، فإذا كانت صلاة لا يجهر فيها بالقراءة ـ كصلاتين الظهرين ـ جهر ببسم الله الرحمن الرحيم وأخفى ما سوى ذلك) ([1]).

Ya ce: na yi sallah a bayan Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gare shihar tsahon kwanaki ya kasance yana karanta fatiha da bismilla, idna sallar ba bayyanar da karatunta misalin Azuhur da La'asar –sai ya bayyanar da karatun bismilla ya boye saura.

والثانية: قال: صليت خلف أبي عبد الله عليه السلام أيّاماً فكان إذا كانت صلاة لا يجهر فيها جهر (ببسم الله الرحمن الرحيم وكان يجهر في السورتين معاً) ([2]).

Ta biyu: ya ce: na yi sallah a bayan Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gare shitsahon kwanaki ya kasance cikin sallar da ba bayyanar da karatunta sai ya bayyana bismilla ya kasance ya bayyanar da bismillar surori biyu a tare.

Fuskar kafa hujja: zahirin riwayoyin Imam amincin Allah ya kara tabbata a gare shiduk da kasancewar yana aikata haka sakamakon mustahabbanci da shaidar cewa da wajibi ne da babu bukatar ambatonsa a kebance, lallai zai kasance misalin ya ce ( na yi sallah bayansa (a.s) ya kasance yana ruku'i da sujjada, ka lura.

Ra'ayinmu shi ne watsi da dukkanin hadisan guda biyu sakamakon raunin isnadinsu da munakashar da ta kasance cikin dalalarsu da kauarcewar da malamai suka daga aiki da su, sai ya zamanto mustahabbanci bayyanar da bismilla ya wanzu ba tare da wani dalili da yake jayayya da shi ba a cikin sallolin da ba a bayyanar da karatunsu, kamar yanda hadisai da suka gangaro cikin wannan babin suka nuni a kai kamar yanda suka gabata, amma raunin d ayake cikinsu hakika malamai sunyi aiki cikinsu wanda haka na gyara raunin kamar yanda wannan shi ne ra'ayinmu.

Tanbihi:

Na farko: shin hukunci da mustahabbancin bayyanar da bismilla cikin sallolin Azuhur da La'asar ya kebantu da limami cikin sallarsa ta jam'i koma bayan mai sallah shi kadai? Ko kuma ya shafe su duka kamar yanda hakan shi ne ra'ayin da mashhur suka zaba shi kuma Ibn Junaidu ya tafi kan kebantar hukuncin da limami bisa riko da ingantattun riwayoyin Sufwan biyu da suka gabata, lallai a bayyane suka kan sallar jam'i bayan Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata a gareshi, sai dai cewa anyi ishkali kansa: da farko dai abin da yake zahiri daga Sufwan hikaya ce daga Imam (a.s) ta fuskar cewa shi yake sallah ba daga cewa yana limamin jam'i ba, ka lura.

Na biyu: bai tabbatu ba cewa Sufwan ya bi Imam (a.s) sallah, bari dai zai iya yiwuwa ya riske shi bayan ya rigaya ya fara sallarsa shi kadai sai yayi sallah a bayansa a lokacin ya rigaya ya fara sallarsa tun kafin zuwan Sufwan, bawai sun fara tare da shi ba yaji lokacin da yake bayyanar da karatun bismilla yana halin sallar jam'i, ka lura.

Koma dai ya ta kasance ba zai a iya kafa hujja da riwayoyin ba cikin kebantar da hukuncin da iya limami da iktisasi da takyidi, bari dia hukuncin ya tattaro hatta mai sallah shi kadai.

Daga Ibn Idris Alhilli cikin littafinsa Assara'ir juz 1 sh 218 kebantuwar hukuncin da raka'o'in biyun farko bisa riko da kebantarwa dalilai da sallar Azuhur da La'asar wadanda kira'a ta ayyanu cikinsu, kuma kira'ar bata ayyanuwa face cikin raka'o'in biyun fari, lallai cikin biyun karshe mai sallah yana da zabi cikin yin tasbihatul arba'a ko kuma karanta fatiha.

Na biyu: sakamakon samuwar ilmul ijmali da ya tafi kan yin ihtiyadul wujubi da kebantuwar hukunci da raka'o'in biyun fari koma bayan na karshe.

Fuska cikin ihtiyadin da ka'idar ishtigalu shi ne cewa babu sabani cikin ingancin sallar wanda bai bayyanar da bismillah ba, sai dia cewa cikinm ingancin bayyanar da bismilla cikin raka'o'in biyun karshe  akwai sabani akwai wadanda suka tafi kan rashin halascin bayyanar da bismilla, ka lura.

Anyi ishkali kan dukkanin fuskoki biyun: da farko: hakika jumla daga nassoshi da suka cikin babin babu kaidi cikinsu da raka'o'in biyun farko, aiki da idlaki sai ya ayyanu, a dora dayar kan mustahabbanci koma bayan kaidi sakamakon kasantuwar kaidi cikin masu kore juna ba masu tabbatarwa.

Na biyu: da wadannan idlakai za dauke hannu daga ka'idar ihtiyadi, lallai ita tana daga usulul amali da dalili ga wanda bai da dalili.

Na uku: lallai ka'idar ta ginu kan rashin halascin bayyanarwa cikin raka'o'in biyun karshe bisa kasantuwar makoma cikin shakka cikin sharadi da juzu'i itace ka'idar ihtiyadi-kamar yanda yake a ilmul usul-sai dai cewa fuska ta hananniya ce ta farko kuma mahallin ishkali(Almustamsak juz 6 sh 206)

 Saboda haka cikin littafin Almu’utabar ya ce: (wasu ba’arin malamai da suka zo daga bayan ajin farko sun ce: duk inda cikinsa karatu bai ayyanu ba a bayyanar da karatu cikinsa ko da kuwa an karanta, shi kebantarwa ne daga abin da malamai suka nassantar kansa riwayoyi suka shiryar kansa..)

Zamu cigaba da wannan bahasi da yardarm Allah ta’ala 

([1]).الوسائل: باب 11 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث: الأوّل.

([2]).الوسائل: باب 21 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث: الأوّل.

Tura tambaya