lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

falsafar humanism (mutumtaka) ka'ida ce ta mazhabar Almaniyanci

Mazhabar duniyanci ko kuma muce Almaniyanci (secularism) raba addini da siyasa wacce take la'akari da cewa lallai shi addini ya iyakantu da iya alaka mutum da ubagijinsa tana mai yanke dukkanin wata dangantaka addini da rayuwar zamantakewa da wancan hujja da suka ambata-sannan daga cikin falsafar mutumtaka akwai ka'idar tunani da take da ita, ya yin da Almaniyawa suke magana kan wannan isdilahi na mutumtaka to fa suna dora masu dukkanin kimomi masu kyawu wadanda suke dangantawa mutum girmama da asali. Bayan kwarara kiristanci kasashen turai cikin sannu-sannu kiristanci ya zama addini halastacce a hukumance ga kasashen turai, sannan matsugunin fafaroma ya wayi wani samfuri da babbar masarauta da take gogayya da masarautun kasahen turai zai ma yiwu ace ita ce kasance mafi iko da karfi daga gaesu a wasu ba'arin lokuta, bari dai fadar fafaroma ta kasance tana bada kariya ga turai da abin data mallaka daga karfi da tanadi, koma yaya dai, cibiyar kiristanci da ta ke misaltuwa cikin batikan da fafaroma ta samu damar assasa babbar masarauta da ta rike linzami da sitiyarin al'amurra cikin galibin fagagen rayuwa, wannan masarauta ta kasance tana aikata zalinci da nuna fin karfi a wata fuskar kuma tana ba da himma cikin yada tunanunnuka da ra'ayoyi da suke sabawa da hankali bari ta kasance tana sabani da ilimi da duk wani abu na hankali a bayyane, wanda wannan mummunan yana yi mai ban takaici daga karshe ya kai ga yin tawayen mutane masu tarin yawa kan kiristanci da majami'a, masana adabi da mawaka sun kasance cikin sahun wadanda sukai wannan tawaye daga cikin mafi shahara daga cikinsu shi ne (Dante Alighieri) wanda galibi ake kiransa da cewa shi ne wanda ya assasa falsafar mutumtaka (humanism) wannan kungiya ta yan tawaye sun kasance suna kudurcewa lallai mutum buktuwarsa ga duniya tafi bukatuwarsa da lahira, haka bukatarsa da wannan duniya da hukuma ta kan doran kasa tafi bukatarsa da duniyar badini ta boye, haka ma bukatuwarsa `yan'uwansa mutane tafi bukatarsa ga ubangiji wanda wadannan akidu na su sun hannun riga da abin damajami'a take kai daga larurar karbar hukumar Allah kan mutum cikin doran kasa; wancan ce kasance dambar farawa dangane falsafar mutumtaka (humanism) a yammacin turai, daga cikin asalai na farko-farko da falsafar mutumtaka take kira zuwa gare su shi ne cewa lallai mutum shi ne mihwari shi ne kuma asalin dukkanin kimomi, sai wannan akida ta zurfafu da shakali mau zurfi ya zama ya zama dole ayi la'akari da komai cikin hidimar addini ayi shi kuma domin hidimta masa don biyan bukatun mutum da burace-buracensa.

Haka dai bisa jingina da wannan tunani sai mutum ya wayi gari yana mai nesanta daga hidimar addini bari dai addini ke cikin hidimtawa mutum, kan wannan tunani ya zama dole ga addini ya tsara kansa da daidaita shi tare da bukatun mutum kuma dole ya tafi tare da sha'awe-sha'awen mutum da abubuwan da yake tsinkaye.

Wannan falsafa ta mutumtaka karkashin asalanta ta samu damar fantsama da yin rassa ya zuwa wasu adadin rassa fadi da tashi ta cigaba da yaduwa da ba zuwa cikin nahiyoyi daban-daban daga kasashen turai da wannan mutane suka nesantu daga majami'un kiristanci suka wayi gari suna tsarkake zatin mutum maimakon bautar Allah, kewayawa ta karkare ta tuke da su ya zuwa fadin cewa lallai mutum ya kamata gare shi ya iyakance kimomi haka kuma lallai bai wajaba kan addini ya yi katsalandan cikin sha'anin mutum da rayuwarsa ba, to da haka ne a raba addini da rayuwar mutum.

Haka muke gani bisa abin dafalsafar mutumtaka ta doru a kai to lallai bukatun mutum da sha'awe-sha'awensa sune ma'aunin gane daidan kimomi, idan wata kungiya tana kwadayi cikin riko da addini to tana da dama yin ayyukan addininta da koyarwarsa amma cikin dakunan ibada tare da dukkanin `yanci sai dai ba ta damar bijiro da addini ko tattauna bahasosin addinin cikin fagen rayuwar zamantakewa da muhimman sha'anunnuka a suka kebanci al'umma.


Tura tambaya