lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

darussan yakini cikin sanin asalan addini

Hakika annabi (s.a.w) ya bayyanarwa al’umma yankakkiyar hakika cikin munasabobi daban-daban da cewa lallai shi ba basarake bane da yake rike da mulki karkashin karfin zatin kansa da zai sanya shugabantar al’umma cikin dukkanin wanda yake so a bayansa, kamar yadda sarakuna ke yi ta yadda suke nada masu jiran gadon mulkinsu a zamaninsu, bari shi annabi da yake karbo sarautarsa da mulkinsa da shiryarwarsa daga Allah tsarki ya tabbatar masa, lallai shi girmansa ya girma ya sanya annabta gare shi ya kuma cikata da hattama da shi, lallai shi ke daukar mas’uliyar isar da sakon Allah zuwa ga baki dayan mutane domin ya shiryar dasu zuwa ga gaskiya da fitar da su daga duffai zuwa ga haske.

Halifanci bayansana hannunsa al’amarinta kuma daga Allah yake yana sanyata inda ya so.

Mu ba zamu ce kamar yadda Umar bn khaddab ya ce ba:  

: أنّ بیعة أبي بكر كانت فلتة وقی الله المسلمین شرّها فمن عاد لمثلها فاقتلوه.

ولا نقول كما قال بعض الانصار یوم السقیفة: منّا أمیر ومنكم أمیر

Lallai bai’ar Abubakar ta kasance kwatsam babu zato babu tsammani Allah dai ya kiyaye musulmi sharrinta duk wanda ya maimaita misalinta ku kashe shi.

Kuma mu ba za mu ce misaln abin da wasu ba’arin Ansar suka ce ba ranar sakifa: a zabi sarki daga cikin mu kuma ku zabi sarki daga cikinku.

Ba kuma zamu fadi abin da Abu Sufyanu ya fada ba cikin halifancin Usmanu:

تداولها یا بني أمیة تداول الولدان بالكرة فو الله ما من جنة ولا نار

Ku jujjuyata ya banu umayya kamar yadda yara ke jujjuya kwallo wallahi na rantse da Allah babu wata alljanna ko wuta.

Ba za kuma mu fadi misalin kalmar da Abubakar ya fada ba cikin rashin lafiyarsa wacce cikin ya mutu :

 

أمّا إني لا آسي الّا علی ثلاث: وودت یوم السقیفة قذفت الأمر في عنق الرجلین ـ عمر وأبوعبیدة ـ فكان أمیراً وكنت وزیرا

Amma lallai ni bana takaici da bakin ciki sai cikin abubuwa uku: nayi burin ace ranar sakifa na wurga al’amarin cikin wuyan mutane biyu – Umar da Abu Ubaida ya kasance sarki ni kuma na kasance wazirinsa.

Kadai dai  mu muna cewa kamar yadda annabi mafi girma (s.a.w) ya ce:

«إنّي تارك فیكم الثقلین كتاب الله وعترتي أهل بیتي» «أهل بیتي كسفینة نوح من ركبها نجی ومن تخلف عنها غرق وهوی»

Mutanen gidana kamar misalin jirgin annabi Nuhu ne duk wanda ya hau ya tsira duk wanda ya juya baya yaki hawa ya nutse ya halaka.

Lallai ni ina barin nauyaya biyu cikinku littafin Allah da tsatsona Ahlil-baiti.

 

«ومن كنت مولاه فعلي هذا مولاه اللهمّ وآل من والاه وعاد من عاداه وانصر من نصره واخذل من خذله

Dukkanin wanda nake shugaban shi Ali shugaban shi ne ya Allah ka jibanci lamarin wanda ya jibance shi ka ki wanda ya kishi ka taimaki wanda ya taimake shi ko tozarta wanda ya nemi tozarta shi.

Lallai mu zamu taimaki sarkin muminai halifan manzon Allah waliyin Allah shugaban musulmai Ali bn Abu dalib zakin Allah mai galaba amincin Allah ya kara tabbata gareshi. Ba kuma zamu kasance  kamar wadanda suka juya bayansu mu bar taimakon gaskiya ba, lallai ita gaskiya tana tare da Ali Ali na tare da gaskiya

Tura tambaya