lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

masu tarbiyya ga al'umma

 mai tarbiya na farko cikin duniyar halitta da dabi'a da abin da yake kunshe bayanta shi ne Allah matsarkaki, hakika shi ne ubangijin talikai, hakika kalmar رب da abubuwan da aka tsago daga gare ta sun zo cikin kur'ani har kusan wurare (980) kur'ani ya tattaro mutanen farko da wanda za su zo daga baya hakika shi kur'ani ya tattara dukkanin abinda ke cikin littafan sama da addinan ubangiji, shi littafi ne mai gadi kan littafan sama  da kasa, shi ya tattara dukkanin iliman magabata da wanda za su zo daga baya, sannan an tattara abin da ke cikin kur'ani cikin surar fatiha, surar ta fara da fadinsa madaukaki:

الحَمْدُ للهِ رَبِّ العَالَمِينَ[1] 

 (godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai)

sai ya siffanta kansa da ubangijintaka, hakika shi ne mai tarbiya na farko ga dukkanin duniyoyi madaukaka da akasinsu, da abubuwa mujarradai marasa jiki da masu jiki, saboda kare dokokin sabubba wanda ke jagorantar wannan duniya sai Allah ya sanya

فَالمُدَبِّرَاتِ أمْر[2]ا

   sa'annan su kasance masu shirya gudanar da al'amari.

 ta kasance sanadin samuwar abubuwa da dokokin tarbiya ke jagorantarsu dukkanin wannan kadai ya kasance bisa rahamarsa duniya da lahira.

 Sannan tarbiya ta yi tajalli da dauko iliman ubangiji cikin annabawa (as) hakika su annabawa sune mabayyanar tarbiyyar ubangiji hakika ya aiko su don tarbiyar mutane da shiriyar dasu da tsayar da adalci da daidaito hakika annabi ya kasance mabayyanar ubangijintakar ubangiji, bauta zinare ne wanda zurfafarsa ubangijntaka, annabi muhammadu ya kasance cikamakin annabawa shugaban manzanni bawan Allah manzonsa .

sannan bayan annabawa wasiyyai da imamai (as) sun kasance kan tafarkinsu da hanyarsu da shiriyarsu, sun kasance mabayyanar tarbiyar ubangiji da annabi, an daura nauyin tarbiyyar mutane da shiryar da su a wuyayensu, sannan kuma bayansu nauyin ya koma kan malamai domin sune magada annabawa da wasiyyai cikin iliminsu da dabi'unsu da dukkanin matsayin da suke da shi, hakika su anayi musu hukunci da magadan da aka dora musu nauyin tarbiyyar mutane bayan sun tsarkake kawunansu da badininsu da ilimantuwa sannan sai su fito ya zuwa ga mutane  zuwa ga abin da zai rayasu su rungumi daukar nauyin tarbiyantarda su tarbiyya ingantacciya ta gargaru.

da hukuncin malamai nagargaru  iyaye maza da mata sune suke tarbiyya cikin iyali da dangi kamar yadda malamai suke tarbiyya a fagen makarantu da fagagen koyarwa, haka al'amarin ya ke cikin ragowar fagagen rayuwa, haka ma cikin ragowar mutane dole a samu wani mai tarbiyantarwa da koyarwar saboda hakan na daga sunnar ubangiji kuma ba za ka taba samun sauyi ko canji cikin sunnar ubangiji

wadannan da muka kawo dukkaninsu mabayyana ne na ubangijin talikai a mukamin tarbiyya, abin da sukayi tarayya ciki shi ne tarbiyya amma sukan banbanta a bangaren fadadawarta da tsukewa bisa la'akari da fadin duniyar da take cikin kowanne dayansu.

misali cikin ilimin mandiki mas'alolin nazari dole su tuke ga badihiyat (sanannun abubuwa ) ma'ana zatin abubuwa saboda shi zatin abu bai bukata kawo dalili kansa,ba don hakan ba da ya lazimta maimaici da tasalsul wanda gurbatattu ne a mahalinsu, saboda haka iliman nazari na tukewa ya zuwa mukaddimar badihiyya na zati  haka al'amarin ya ke cikin tarbiya da mai yinta  hakika ita ma tana tukewa ga tarbiya ta zati wacce ta ke tarbiyya ce ta ubangiji da ta bubbugo daga rububiyarsa girmansa ya girmama, iyaye masu tarbiyya ne da suke komawa ga malamai cikin tarbiyantar da kawukansu, su kuma malamai na koma ga annabawa da imamai (as) wanda ke dauke da tarbiyyar zati hakika su kuma imamai (as) suna komawa ga Allah ubangijin talikai domin shi ne mai tarbiyya na farko, sai tarbiyyarsa ta halitta cikin halittu da ta shari'a su yi tajalli cikin halittunsa, haka cikin annabawa malamai da iyaye, tarbiyya da ke bijira wadda a ke tsiwirwirarta a wannan lokaci na tukewa ya zuwa tarbiyyar ta zati tabbatacciya  sai a lura

 

Tura tambaya