lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Addu’a makamin mumini da ita damuwa ke yayewa bakin ciki yake tafiya, shi shela ne daga hujja mudlaka ga sarki mudlaki ubangiji mai rainon talikai, rashin amsa addu’a tare da cewa Allah ya yi alkawarin amsa ta 

 (أدعوني استجب لكم)

ku kira ni zan amsa muku

 

ta yaya zamu fuskanci wannan ishkali menene hijaban da suka katange tsakaninmu da tsakanin amsa addu’a, akwai wani batun daban da yake bayyanuwa cikin addu’o’in da suka zo daga ma’asumai (as) da yadda ake yin addu’a da su ? wadannan batutuwa jigo da wasunsu sun kasance cikin tattaunawar mu ta mubahasa tare da samahatu ayatullah sayyid husaini shahrudi (dz) sai ya amsa mana yana mai cewa :

1-     Sasanni na farko amsa addu’a : bahasi kan amsa addu’a yana maudu’ai masu tarin yawa daga cikinsu shi ne abin da ke fado cikin kwakwalwar muminai da wasunsu lallai Allah matsarkaki madaukakin sarki yana cewa:

 

 (إِنَّ اللَّهَ لَا يُخْلِفُ الْمِيعَادَ)

Tabbas Allah bai saba alkawali. Suratul ra’adu aya:31

 Haka ma cikin fadinsa madaukaki :

 

 (وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ...)

 

Idan bayina suka tambaye ka game da ni tabbasi ni ina kusa ina amsa kiran mai kira idan ya kira ni. Suratu bakara aya :186

 

Shi daga bangare guda yana umarni a daya bangaren kuma yana fadin cewa lallai ni bana sa`ba alkawali a bangare na uku shi ne mu kuma mafi yawan abin da muke gani a waje shi ne cewa ba’a amsa mafi yawan addu’o’inmu, wannan ishkali yanada amsoshi masu yawa daga cikin amsoshin akwai amsar irfani wadda yake cewa :

 

 (إن تحت أي دعاء منك لبيك مني)

Tabbas kasan dukkanin wata addu’a daga gareka akwai amsawa daga gareni.

 

Sai dai cewa wannan amsa ba zata gamsar ba yawancin mutane ba zasu ce idan shi Allah yana amsa dukkanin addu’ar da mukeyi to me yasa bama ganin tasirinta a fili a sarari a zahiri? Akwai wata amsar daban cewa tabbas Allah matsarkaki madaukaki yana biyan bukata sai dai cewa kuma tare da jinkirtawa kamar yadda hakan ya zo cikin nassin du’au iftitahu

 (ولعل الذي أبطأ عني هو خيرٌ لي لعلمك بعاقبة الآمور)

ta yiwu abin da ya jinkirta daga ni ya fi zama alheri gareni sakamakon iliminka ga karshen lamurra.

 

Sai dai ita ma wannan amsar ba zata gamsar da wasu saboda wasu suna neman bukatu biyu, bukatar farko ita ce asalin bukata shi ne misali ina bukatar gida ta biyu kuma shi ne ka cika mini waccan bukata take ba tare da jinkiri ba, idan ya zama ya amsa bukatar fari tare da jinkiri sai dai cewa shi lallai bai amsa ta biyu ko kuma ni banji alamun amsawa ba, amsa ta uku shi ne abin da ya zo daga hadisai na cewa lallai ita addu’a tanada sharudda guda takwas dukkaninsu suna dawowa zuwa ga cewa lallai mutanen da suke addu’a  a daidai wannan lokaci suke kuma sabawa Allah cikin umarninsa da haninsa, ita ma dai wannan amsar ba zata gamsar da wasu ba saboda akwai wata doka cikin ilimin usul ita ce idlaki (saki babu kaidi) sannan ita ayar da ta zo da cewa Allah ya yi alkawalin amsa addu’a ta zo ne da saki babu kaidi ba ta ce ku kirani da sharadin ka da ku saba mini ba sai in amsa muku, kadai dai ya ce ku kirani wannan siga kuwa ta tattaro kowa da kowa ba tare da togaciya ba ko wariya ba, amma jawabi mai gamewa wanda ya wofinta daga waddannan ishkaloli to shi ne mu ciro kaidi da sharadi daga cikin shi kansa kur’anin Allah madaukakin sarki cikin suratu bakara aya: 40 yana cewa:

 (... وَأَوْفُوا بِعَهْدِي أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَإِيَّايَ فَارْهَبُونِ)

 

Ku cika alkawalina zan cika alkawalinku  ni kadai zaku ji tsoro.

 

Misali ni da kai mun cimma yarjejeniya kan zan sayar maka wannan gidan kan wannan kudi naira kaza to idan kai baka bani kudin ba bazan baka gidan ba saboda lallai cika alkawalina ya dogara ne da cika naka, saboda haka Allah ya dau alkawalin amsa addu’a da sharadin shima mutum ya cika alkawalinsa tare da Allah, anan tambaya take fadowa shin ma wai menene alkawalin Allah madaukaki don mu samu damar cika shi, amsarta tazo a wata ayar  cikin fadinsa madaukaki cikin suratu yasin aya:60.

 

 (أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آَدَمَ أَنْ لَا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ)

 

Ashe banyi alkawali gareku ba ya bil adama da kada ku bautawa shaidan lallai shi makiyi ne gareku mabayyani.

 

Daga tattarowa wadannan ayoyi guda uku zamu fitar da natijar cewa lallai shi Allah madaukaki tun farko lamari lokacin da ya dau alkawalin amsa addu’a bai dau alkawalin ba tare da musanye da mayin amsawar ba, musanyen da mayin shi ne mutum ya kame daga bautawa shaidan da binsa, tabbas wadannan riwayoyin tafsiri ne da Karin bayani  ga wadannan ayoyin.

 

Sasanni na biyu: ladubban addu’a

Ya zo cikin kur’ani fadinsa madaukaki cikin suratu a’araf aya:55

 

  (ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ)

 

Ku kirayi ubangijin ubangijinku kuna halin `kan`kan da kai da tsoro tabbas shi bai son masu ketare iyaka.

 

 A cikin aya ta biyu 205 kuma ya ce:

 

(وَاذْكُرْ رَبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآَصَالِ وَلَا تَكُنْ مِنَ الْغَافِلِينَ)

 

Ka kirayi ubangijika cikin ranka tare da `kan`kan da kai da tsoro da kuma koma bayan bayyane da safiya da maraice ka da ka kasance daga gafalallu.

 

Ma’ana cikin sauti na nutsuwa `kasa-`kasa  ba da daga sauti ba. Imam sadik (as) yana bayyna fuskar wannan batu na kur’ani da bayanansa: da cewa sababin daga sauti da murya dayan biyun al’amura biyu ne, na farko dai imam dai wanda na kake kira yna da matukar nesa daga gareni  sai nake kokarin daukaka sauti na da murya ta don ya ji murya ta, na biyu kuma lallai shi yana kusa da ni sai dai kuma baibai ne bai ji sosai sai ya zama na larurantu da `daga sauti na da murya ta, sai dai kuma shi Allah matsarkaki madaukaki yana cewa

 (نَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ الْوَرِيدِ)

mu muka fi kusa zuwa gareshi daga jijiyar wuya.

 

Wannan dangane da kusancin ji kenan Allah bawai kadai mai ji bane kawai bari dai shi mai yawan ji ne shi ne mafi jin masu ji idan ya kasance akwai suldani da fasilar hijabi gwargwadon kamu guda sai kai kasance kana `daga sautinka a gabansa sai ya kasance addu’a da kira da munana ladabi muna fitar da natija cikin kur’ani cewa doka ta asali da ke jagaba shi ne addu’a da kira su kasance cikin sauti `kasa-`kasa, sai dai cewa akwai wasu wurare da yake zama larura sai mutum ya yi `daga murya da sautinsa daga ciki shi ne akwai wanda bai da sanin addu’a misalign du’a’u kumail to a irin wannan wuri zaka `daga sautinka bawai don addu’ar ba sai don koyar da shi suma suyi addu’ar kamar yadda ka ke fa`di to a wannan wuri kenan ansamu karo da juna tsakanin abubuwa biyu, shi ne tsakanin kiyaye ladabin addu’a da kiyaye sautina da kuma tsakanin `daga sautina domin wadanda na ke koyarwa su karanta tare da ni.

da yawa-yawan ma’abota ilimi suna `daga sautinsu domin koyarda mutane, tunda bukata ta biyu tafi muhimmanci daga ta farko to lallai shi ya sanya wasu ba’arin sharuddansa saboda fa’ida mafi girma, ita addu’a tana kasance a bayyana a wurare biyar a iya sanina da ilimina na farko shi ne cikin alkunuti da addu’ar imam husaini (as) a ranar Arafat hakika imam ya `daga sautinsa lokacin da ya yi wannan addu’a ranar Arafat, wuri na uku shi ne yin addu’a ga mutum da bai mallaki gida ko kuma gidansa `karami ne  ya zo cikin riwayoyi da cewa ya nemi gida daga Allah tare da `daga sautinsa gabanin addu’ar da bayanta ya ce:   

  اللهم صل على محمد وآل محمد

Ya Allah kayi salati ga Muhammad da iyalansa.

Kai hatta don neman yalwatawa yana iya fadin: (ya Allah ka azurta ni da gida mayalwaci ) ka `daga sautinka gwargwadon yadda ya samu dama kamar yadda ya zo cikin lafazin riwayar, na hudu idan mutum ya zama yana daga masu jagaban sallar jam’i mustahabbi ne ya jiyar masu binsa salla sautin addu’arsa idan ya sauka sujjada yan nufin addu’a bawai kasantuwarta addu’a ba akankin kanta a’a kasantuwar tana gangarowa daga limamin sallar jama’a to sai ya bayyanar da karatunta  da hukuncinta na addu’a wacce ake cikin sallar dare saboda dama mustahabbi ne bayyana addu’a cikin sallar dare domin wanda zai farka ya farka, idan ka nufi rama sallar darenka idan kaga cewa iyalanka suna ganinka to kada kayi sallar a bayya ne ka yi ta a boye tare da mustahabbancin yinta a bayyane muhimmi shi ne kai mai kiwo ne wanda nauyi yake kansa abin tambaya kan abin da aka bashi kiwo da kulawa, idan iyalinka suka ganka kana rama sallar darenka zasu zamu kasalallu cikin sallarsu kuma kai ne sababin faruwar hakan, wuri na biyar shi ne cikin yin salati ga muhammad da iyalansa  wanda ya wayi gari da wannan yanayi shi da`di kan kasantuwarsa addu’a wani take sannan ne cikinta shi ne `daga sauti, ta yiwu wasu ishkaloli su bayyana lokacin da muke karanta addu’o’i daga a’imma ma’asumai (as) daga ciki shi ne shin zamu karanta kamar yadda ma’asumi yake karantawa ba tare da da`di ko ragi ba, ko kuma dai muna da `yanci cikin wannan al’amari cikin kara wasu jumloli ko maimaita su  a wasu lokuta a wasu wurare?

Amsa kan abin da ya zo daga wurin a’imma (as) lallai mu zamu takaitu daga abin da ya zo daga ma’asumai (as) ka da mu kara komai kai ka da kuma mu tauye komai daga ciki, babu matsala idan ya zama akwai wani abu da ya yi cikas kamar misalin karancin lokaci da makamancinsa, amma kari lallai cikinsa akwai hani dalili kan haka sune wasu dalilai na hankali da na nakali. Amma dalili na nakali shi ne abin da ya zo cikin wasu ba’arin hadisai cewa wani mutum ya cewa imam sadik (as) lallai a karshenb zamani fitina mai girma zata kasance mutum zai nutse cikinta sai imam ya bashi amsa da na’am babu mai tsira daga wannan fitina sai wanda ya nemi taimako da addu’ar mai nutsewa  sannan imam ya koyar da wannan mutum addu’ar, wannan ita ce addu’ar kamar haka:

 (بسمِ اللهِ الرّحمنِ الرحيمِ يا مُقلّبَ القلوبِ ثبت قلبي على دينك)

 

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai ya mai jujjuya zukata ka tabbatar da zuciyata kan addininka.

 

Marawaicin wannan yana da tsanantawa cikin tabbatarwa a nakalin hadisi sai ya nemi imam sadik (as) ya jiyar da shi daga gareshi sai ya ce:

 

 (يا مُقلّبَ القلوبِ والابصار ثبت قلبي على دينك)

 

Ya mai jujjuya zukata da idanuwa ka tabbatar da zuciata a kan addininka.

Sai imam (as) ya amsa masa da cewa:

 (لا أقل أن ما قلت خطأ ولكن كما قلتُ قل)

 

Ni bana cewa abin da ka fada kuskure ne sai dai cewa ka fadi

Ma’anar riwayar shi ne akwai wata kalma bamu ce kuskure bace ko kuma cikinta akwai kuskure  sai dai cewa matukar dai ba ta zo daga imam ba tare da ingancinta ya zama dole mu bi yadda ya fada, wasu ba’ari suna addu’a suna fadin

 

 (يا مثبت القلوب ثبت قلوبنا على دينك)

 

Ya mai jujjuya zukata tabbatar da zukatanmu a kan addininka.

mu muna cewa lallai mu muna lazimtar riko da nassi amma idan na nufi a amsawa wannan addu’a dangane da`yan’uwa na sai in ce musu ku karanta wannan addu’a kuma in koya musu.

Amma dalilin nakali shine matukar muna ganin cewa lallai shi imam (as) ya yi kari cikin ba’arin wurare da fadin:

 (إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)

Lallai kai mai iko ne kan komai.

 

Da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama

Sai dai cewa cikin addu’armu ga hujja (af) tare da gangarowar addu’ar daga fiye da imami daya mun sami cewa imam a karshenta bai fadi lafazin (da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama haka ma bai fadi (lallai kai mai iko ne kan komai) ba, tare da kau da ido daga dalili nakali na farko dalili na hankali zai bayyana ya tallafa mana ya ce kai idan ka karanta shin kana ganin lallai shi imam ya manta karanta wadannan jumloli da ka karanta kenan (Allah ya tsare) har kai ka tuna ko kuma kai ka gano abin da imam ya gaza ganowa kenan, dukkanin amsoshin za su a’ a kenan, daga wadannan bayanai sai ya zamanto ya ayyanu da cewa lokacin da ni nake kara wasu jumloli ko dai ina jin kaina na fifita kan imam ko kuma dai shi imam din ya manta ko ya yi rowa karin hakan kanmu, dukkanin wadannan surori ababen wurgi ne, sai ya ayyanu da cewa ka da muyi kari kai, misali cikin du’au kumail imam yana cewa 

 (يا نور يا قدوس)

Ya haske ya tsarkakakke

Idan kai ka karanta karo guda sai wani mutum ya zo ya maimaita, zamu ce asa mai ya sa kai kake maimaitawa? Maimaici dai zai iya zama ko dai mafi kyawu ko daidai ko mafi munana, sai mu ce menene laziminsa. Idan ya ce mana daidai yake da bainda ya zo a rubuce a addu’ar sai mu ce masa shin kana bata lokacinka da lokacin wasu ga abin da daidai da abin da ke rubuce wannan shirme ne bai da wani amfan, babu abin da ya rage masa face ya ce mana shi karin a kankin kansa abu ne mai kyawu mujarradin fadin cewa kari yanada kyawu to fa ya munanawa imam (as) domin zai zama kenan shi ya fadi abin da yafi na imam kyawu kenana, ta yiwu mai maimita irin wannan yanki daga addu’ar kumail ya bamu amsa da cewa ashe halarto da zuciya bai daga cikin addu’a, sai mu ce masa babu matsala daga maimaitawa idan wani abu ya afku misalin `karar `kararrawa ko dai abin da ya yi kama da haka da yake zama sababi na gigitar tunani da dauke hankali sai dai cewa mu bama tare da kai da cewa kai tsawo shekara da shekaru  kana maimaita jumla daya kadai ra, idan haka neto da sai ya zama   kana tare da halarto zuciya awani wurin daban daga ragowar wuraren, me yasa sai wannan waje kake rasa hallarar zuciyarka  kuma hakan bai faru bagtatan ba ba zato babu tsammani bari dai kai dai kana ganin maimaicin shi yafi kyawu, kamar yadda babban malami abu ali sina yake cewa lallai ita bagtatan kwatsam bata fiya afkua a galibin lokuta wannan doka ce mai gamewa.

Ta yiwu wani ya ce wannan nuk`dar ita ce kollluwar kimar addu’a ma’ana lallai ita addu’a ba dukkanin ta take kai daya bai daya ba daidai ba kamar yadda ake cewa cikin ilimin balaga tabbas shi kur’ani duk da cewa dukkaninsa mu’ujiza ne sai dai cewa fadin Allah cikin suratu masad aya: 1

 (تَبَّتْ يَدَا أَبِي لَهَبٍ وَتَبَّ )

Hannun abu lahabi sun ta`be shima ya ta`be.

 

Ba daidai yake da fadinsa ba cikin suratu hudu aya:44

 

  (وَقِيلَ يَا أَرْضُ ابْلَعِي مَاءَكِ وَيَا سَمَاءُ أَقْلِعِي وَغِيضَ المَاءُ وَقُضِيَ الأمرُ وَاستَوَتْ على الجُودِي وقِيلَ بُعدًا للقَومِ الظَّالمِينَ)

Aka ce ya ke kasa ki ha`diye ruwanki yak e sama ki kame, kuma aka `kafar da ruwan aka hukunta lamarin ta daidaita a kan judiyyu aka ce nesa ga mutane azzalumai.

 

Cikin balaga suna cewa wannan balagarta tafi girmama daga balagar waccan ayar, ingantacce ne cewa dukkanin wadannan addu’o’i daga suke sai dai cewa ba’arin wasu nukdodi suna wani fifiko da yake isar da su zuwa ga kololuwa, saboda kiyaye wannan fifiko aka maimaita su a wasu wurare kebantattu  daga addu’a, sannan ana fa’idantua cikin dokokin ilimin balaga cikin tabbatar fadinsa.

Amsa shi ne wannan magana bata inganta ba shin kai ka shiriya ka kai ga gano wani ffifiko cikin wannan addu’a da abin da imami ma’asumi (as) bai kai ga gano shi ba, irin wannan magana ana samunta cikin jaridu ya kan faruwa sai a dauke shi a sanya can tsakiya a rubuta da manyan rubuta gwara-gwara sai ace wannan magaryar tukewar tattaunawar tana da kuma matukar muhimmanci, da ace haka cikin abin da yake maimaitawa akwai wani fifiko da sarkin muminai Ali ibn abu dalib (as) da kansa ya maiamiata gabaninka, idan ka ce ai shi ma da mutanensa rashin halarta zuciya yana afkuwa da su a wannan nukda, amsa tawaya cikinku ku dinnan me yasa bakwa mai da kanku da irin yanayin da sarkin muminai Ali (as) zai gamsu da addu’arku alhalin shi dama ya sanya wannan addu’a ne ga mutane gama gari lallai kai kake wannan maimaici ka sabawa hanyar da sarkin muminai Ali (as) ya koyar saboda haka kayi watsi da abin da shaidan ya ke umartarka ka sallamawa hanyar sarkin muminai (as) ta yiwu mai yin haka ya bawa kansa uzuri ya ce sarkin muminai Ali (as) kowanne lokaci ya kasance cikin halin halartar zuciya da `damfaruwa da Allah madaukaki yana kuma cewa:

 (لو كُشف لي الغطاء لما ازدت يقينا)

Da za a yaye mini rufi da ba zan karu da wani yakini ba.

Sai mu ce masa lallai sarkin muminai Ali (as) ya koyar da sahabinsa kumaili ibn ziyad addu’ar ne domin ta gangaro zuwa garemu sannan ba zai yiwu ace shi imam ya gafalu daga yima kumaili ibn ziyad wasicci maimaita wannan jumloli ba da kuke maimaita su.

Zai iya cewa ni ban shar’anta ba ban kuma danganta hakan ya zuwa ga wani ma’asumi ba har da zai zama haramun, sai dai cewa mu muna cea dalili na nakali da ambatonsa ya gabata shi ne shifa marawaicin bai danganta karin ba zuwa ga ma’asumi amma tare da hakan ma’asumi ya hana shi kari cikin addu’a, ko da kuwa babu niyyar shar’antawa to fa wannan aiki da kake yi zai zama kudurcewa ne da cewa abu ne da ya fifita kan aikin ma’asumi (as) ba da ban haka da baka aikata ba.

Amma dalili na uku wanda shi ne yake wajabta rinjayarwa amma bai wajabta lazimta  shi ne cewa lallai tun da can sun kasance suna cewa

.

 (فَأَمَّا مَنْ ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَهُوَ فِي عِيشَةٍ راضِيَةٍ في جنة عالية وأَمّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأمّه هَاوِيةٌ)

Amma wanda ma’aunansa sukai nauyi to shi yana cikin rayuwa yardadda cikin aljanna madaukakiya*amma wadanda ma’aunansa sukai rashin nauyi to uwarsa hawiya ce.

Sunce lallai shi mizani yanada tafuka guda biyu a da amma bayan zuwan mizanin kimiyyar zamani sai suka ce tafi guda gareshi. Bayan haka sun tafi ziyartar sarkin muminai Ali (as) sai suka samu

 (السلام عليك يا ميزان الأعمال)

Amincin Allah ya tabbata gareka ya mizanin ayyuka.

Sai ya bayyana cewa Ali (as) shi ne mizanin ayyuka dukkanin wanda galibin ayyukansa suka kamanceceniya da shi to shi ne wanda mizaninsa ya nauyaya har zuwa lokacin da sabani zai kasance a wannan lokaci ne mahallin

 

 (وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ. فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ. وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ. نَارٌ حَامِيَةٌ

Amma duk wamda ma’aunansa suka saukaka sukai rashin nauyi uwarsa hawiya ce* me ya sanar da kai ita* ita wuta ce mai tsananin zafi.

Saboda haka maimaita kalaman ma’asumi aiki sabanin aikin da ma’asumi ya yi wanda zai tanadar mana da hasara, saboda haka abin da ya fi zama abin so shi ne ka da mu sanyawa kanmu wannan hasara matukar dai sarkin muminai Ali (as) shi ne ma’aunin ayyuka

 

Mustafa gazi da’amiyyu

Tura tambaya