lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bayani kan Ayatullah saiyid Adil Alawi



Da sunan Allah me rahama me jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah ma daukakin sarki uban gijin talikai, mahaliccin sammai da kassai, wanda ya bai wa dan Adam baiwar rubutu da karatu saboda ya ciyar da wannan niima ta baiwa da Allah ya basa na ga mutanen gobe.

Tare da jinjinawa ga fiyayyen Halitta annabi Muhammad (saw) wanda aka sauko masa da cikakkiyar Addini wato Addinin musulunci.

Da kuma iyalan gidan sa tsarkaka wan da Allah kore su da ga duk wani mummunar aiki kuma ya tsarkake su tsarkakewa

Lallai marubucin da yayi amfani da baiwar sa ta Ilimi da kyawawan bayanai zai yi matukar tasiri kan masu sauraronsa musamman ma idan ya hada da koyarwa irin na Alquani me girma da hadisan manzon tsira da kuma na iyalan gidan sa (saw) tare da hanyoyin koyarwa irin na manya manyan malaman addini.

Ayatullah Saiyid Adil Alawi yayi matukan samun nasara gun fanni daban daban na koyarwar Addinin musulunci.

Daya daga cikin baiwar da Allah ya basa shine kaifin Alqalami. Wanda ya wallafa littattafai da dama cikin harshe biyu wato Larabci da kuma Farisanci

Bayan baiwar kaifin Alqalami da Allah ya basa, yana da basir Magana, kuma yana amfani da wannan baiwar da Allah ya basa wurin Karen mutuncin dan adam, kuma yana yaqi da duk wani abun me muni da ke gurbanta Al’uma

Wasu niimomin da Allah ya ma wannan bawan san shine ya basa daman koyarwa a hauza ta qum, tun daga mataki na muqaddima har zuwa bahsul kharij

Wani baiwar da Allah yayi ma wannan bawan san shine ya basa karbuwa a cikin jamaa, wanda mutane da dama suna zuwa domin binshi sallar jam’i (ذلک فضل الله یؤتیه من یشاء)

Abinda zaku gani nan gaba wasu magan ganu ne da ga cikin bayanan da yayi cikin harcehn farisanci a wani taron da akayi a kasar Iran duk da cewa asalin yaren sa larabci ne, amma cikin ikon Allah yakan iya yin bayani cikin wannan harchen (farisanci)

Wannan malamin yana da sabbin mahanga ilimin falsafa, yana da aqida kan cewa zatin Allah da sifofinsa da kuma iyyukan sa tsarkakane

Amma shi kuma shaidan duka wadannan abubuwa guda uku (zatin sa, siffofinsa da kuma ayyukansa) sunkasance munanan kuma abin qi,

Wadannan abu guda uku a dan adam in sukayi kyau zai zamo na kirki amma in sukayi muni zai zamo na banza,sabida haka shi dan adam in yayi aiki na kwarai zai iya samun matsayi babba a gun Allah, in kuma ya kasance na banza zai kasance kaskancacce cikin kaskantattu.

Za’a iya samun cikakkun bayanai kan wannan maudi acikin tarun karantarwar wannan babban malamin.

Daga karshe muna rokon Allah (swa) ya qara wa malam nasara da basira kan hidindimu da yake wa Ilimi.


Tura tambaya