lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bakon dakin Allah


Da sunan Allah me rahama mai jin kai

Imam Ali bn Abu Talib (a.s.) da ne ga baffan Manzon Allah (s.a.w.a.) kana kuma mai kare shi wato Abu Talib(1) (r.a), da kuma Fatima bint Asad(2), An haife shi ne a ranar Juma'a 13 ga watan Rajab shekara ta 30 bayan shekarar giwaye a dakin Ka'aba mai girma.

Hakika cikin haihuwar Amirul Muminin (a.s.) akwai abubuwan mamaki masu girman gaske wadanda dan'Adam bai taba ganin irinsu ba, kuma wadanda suke nuni da daukakan da yake da shi da kuma matsayinsa a wajen Ubangiji Madaukakin Sarki.

Shi dai Amirul Muminin (a.s.), kamar yadda dukkan bangarorin musulmi (Shi'a da Sunna) suka tabbatar, an haife shi ne a garin Makka a dakin Allah mai tsarki (wato dakin Ka'aba). Malumman tarihi sun bayyana cewa, lokacin da mahaifiyarsa Fatima bint Asad ta fara jin alamun haihuwa nan take sai ta nufo dakin Allah mai tsarki. Ko da isowarta sai ta tsaya a jikin dakin tana mai addu'a ga Allah da kuma kaskastar da kai gare Shi don Ya saukaka mata wannan haihuwa tata, inda take cewa:

"Ya Ubangiji na! Ni na kasance mai imani da kai da kuma dukkan litattafan da Ka saukar, da kuma dukkan Manzannin da Ka aiko, kuma na kasance mai gaskata maganarKa da kuma maganar kakana (Annabi) Ibrahim al-Khalil, wanda ya gina wannan daki naKa. Ya Allah! Ina rokonKa don AnnabawanKa, Manzanni da kuma Mala'ikunKa makusanta, da kuma don wannan jinjiri dake cikin cikina, da Ka saukaka min haihuwata"(3).

Gama wannan addu'a ke da wuya kenan, sai kawai wani sashi na katangan dakin Ka'aba da ake ce ma al-Mustajar ya tsage, nan take ita kuma Fatima bint Asad sai ta shiga ciki don haihuwar wannan da nata. Shiganta ke da wuya sai katangan ta koma ta rufu kamar babu wani abin da ya faru. Koda yake wannan daki yana da kofar shiga da fita, to amma don Allah Ya kare wannan baiwa taSa da kuma nuna girman jaririn da za'a haifa din, sai Ya sanya kofar ta ki buduwa, duk kuwa da irin kokarin da wasu suka yi na budewa, bata budu ba sai da har aka haifi wannan jariri kuma uwarsa ta fito da kanta bayan kwanaki uku.

Shaik Tusi (r.a) cikin littafinsa al-Amali ya ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa: Abbas bn Abdul Mutallib da Yazid bn Ka'anab sun kasance suna zaune a kusa da dakin Ka'aban, sai ga Fatima bint Asad bn Hashim ta iso gurin tana dauke da cikin Amirul Muminin (a.s.) na wata tara, a ranan kuwa ranar karshe ce na wannan ciki na ta. Ko da isowarta sai ta tsaya a jikin dakin Ka'aban, alhali kuwa tana fama da nakuda, ta daga hannunta sama tana addu'a……(tana fadin addu'ar da muka kawo a baya)(4) .

Nan da nan, kamar kyaftawa da bismillah, wannan labari mai ban mamaki na tsagewar katangan Ka'aba ya yadu ko ina cikin garin Makka. Ba da jimawa ba sai ga jama'a ciki har da Abu Talib suka taru a jikin dakin suna kokarin bude shi, don mata su shiga su kai taimako ga Fatima bint Asad wajen haihuwa. To amma duk wannan kokari nasu yaci tura, kofar taki buduwa. Daga nan sai suka san wannan lamari daga wajen Ubangiji ne, don haka sai suka saduda suka koma suna masu zuba wa wannan iko na Allah ido.

Su wadannan jama'a a tunaninsu, Fatima bint Asad tana cikin halin wahala ne, don kuwa daman nakuda ya gaji hakan, don haka ne yasa suka kawo mata dauki. To amma ba su san cewa ita ba ta ma san me ke faruwa ba kuma ba ta ma cikin wata damuwa ko kuma jin zafin haihuwar kamar yadda suke tsammani. Don kuwa a daidai lokacin ma tana cikin nitsuwa da kwanciyar hankali ne ba tare da wata damuwa ba. Don dada fahimtar wannan lamari da kyau, bari ma mu ji abin da take fadi yayin wannan lokaci na haihuwa. Cewa take:

"Na zauna a cikin wannan guri na kimanin sa'a guda, sai ga shi na haifi dana Aliyu bn Abi Talib ba tare da wata damuwa ko zafi ba………".

To bayan faruwar wannan lamari, wato haihuwar Aliyu (a.s.), Fatima bint Asad da wannan tsarkakakken da nata sun ci gaba da zama cikin dakin har na tsawon kwanaki uku, alhali kuwa mutane suna nan makil a gurin don ba wa idanuwansa abinci da kuma mamakin wannan babbar mu'ujiza. A rana ta uku kuwa sai ga ta ta fito tare da wannan da nata, ta hanyar da ta shiga, alhali kuwa wannan jariri yana haske fuskarsa tana walkiya kamar farin wata. Fitowarta ke da wuya sai ta dubi mutanen da suka taru a wajen tace musu:

"Ya ku mutane! Hakika Allah Madaukakin Sarki Ya zabe ni da kuma daukaka ne akan sauran matayen da Ya zaba a gabannina. Lalle Ya zabi Asiya bint Muzahim, wacce ta bauta wa Allah a boye a wani guri…..sannan kuma Ya zabi Maryam bint Imrana, lokacin da Ya saukaka mata haihuwar Isa, tana mai girgiza bishiyar dabino don su zubo mata ta ci. Sannan kuma Allah Ya zabe ni da kuma daukaka ni akanta da kuma dukkan wadanda suka gabace ni daga matayen duniya, don kuwa ni na haihu a dakinSa mai tsarki, kuma na ci gaba da zama a cikinsa na tsawon kwanaki uku ina mai cin abinci da 'ya'yan itatuwan aljanna (ba tare da wata wahala ba.....(5)",har zuwa karshe.

Wannan haihuwa ta Imam Ali (a.s.) a dakin Allah al'amari ne da kusan dukkan malumman tarihi sun ruwaito shi da kuma tabbatar da ingancinsa, in banda 'yan tsiraru daga cikinsu masu kokarin kore duk wata falala da darajan Amirul Muminin (a.s.) da kuma Ahlulbaiti (a.s.) saboda dattin da zuciyarsu take da shi na gaba da kuma kiyayya ga wadannan tsarkakakkun taurari masu haskaka hanya da kuma shiryar da mutane zuwa ga hanya madaidaiciya. Kuma ko ba'a fadi ba hakan wata falala da kuma daukaka ce da babu wani da ya same ta ko kuma da zai same ta, tun daga farkon duniya har zuwa karshenta.

Bayan gama wannan jawabi, sai Annabi (s.a.w.a.), wanda daman ya kasance a wajen don tarbar wannan jariri, dan'uwansa, sannan kuma halifansa a bayansa, ya nufo inda take cikin fara'a da farin ciki don yin maraba da barka da zuwa ga Amirul Muminin (a.s.) da kuma taya mahaifiyarsa murnar sauka lafiya da kuma samun wannan tsarkakakken jariri. Koda wadannan 'yan'uwa biyu (Annabi da Imam Ali) suka hada ido, sai Imam Ali (a.s.) yayi dariya saboda da ganin Manzon Allah (s.a.w.a.), shi kuwa Manzon Allah (s.a.w.a.) sai ya dauke shi ya sumbance shi, ya gode wa Allah saboda bayyanar da wannan jariri, wanda ya san zai kasance mafi dacewa da kyawun ya zama mataimakinsa, wazirinsa kana kuma halifansa a bayansa. Wanda zai cika babban burin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da kuma na 'yan'Adam gaba daya, wato haskaka duniya da haske bayan ta cika da duhu, da kuma shiryar da al'umma zuwa ga tafarki madaidaici da babu wani wanda zai iya hakan bayan Manzon Allah (s.a.w.a.) sai shi.( ...إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٌ وَ لِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ )".... abin sani kawai, kai dai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa" (6).

Daga nan sai mahaifinsa Abu Talib ya gayyaci mutane don halartar walimar murnar wannan ni'ima da Allah Yayi masa da kuma dukkan halittun duniya.
 


____________

(1)- Aihinin sunan Abu Talib (r.a) shi ne Abdul Manaf, to amma an fi saninsa da wannan suna na Abu Talib hakan kuwa lakabi ne ake masa da babban dansa mai suna Talib. Shi dai Abu Talib baffa yake wa Manzon Allah (s.a.w.a.) don shi dan'uwa ne shakiki wa Abdullahi baban Annabi (s.a.w.a.). Kuma shi ne yaci gaba da kulawa da Annabi (s.a.w.a.) har zuwa girmansa bayan rasuwar mahaifinsa Abdullahi da kuma kakansa Abdul Mutallib. Lalle tarihi ya tabbatar mana da irin tsananin kauna da soyayya da kuma kulawan da Abu Talib yake nuna wa Ma'aiki (s.a.w.a) sama da yadda yake nuna wa 'ya'yansa. Haka nan kuma bayan girmansa da kuma lokacin da aka aiko shi a matsayin Annabi, ya ci gaba da kare shi, bayan yayi imani da shi, har lokacin da Allah Ya karbi ransa, ta koma ga rahamar Ubangiji. To saboda irin wannan kulawa nasa da kuma kariyar da yake bai wa Annabi (s.a.w.a.) da kuma Musulunci ne ma yasa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira shekarar da ya rasu da suna "shekarar bakin ciki".

(2)- Fatima bint Asad bn Hashim (r.a) itace mahaifiyar Imam Ali (a.s.), kuma an ruwaito cewa ita ce Bahashimiya ta farko da ta auri wani Bahashime gaba da baya, kuma itace mahaifiyar sauran 'ya'yan Abu Talib (r.a) , sannan kuma a hannunta ne Annabi (s.a.w.a.) ya girma tana mai tsananin sonsa da kaunarsa kamar yadda mijinta yake masa. Don haka ne ma Annabi (s.a.w.a.) yake ambatonta da cewa ita ce mahaifiyarsa. An ruwaito cewa tana daga cikin musulman farko, kana kuma wacce take da imani mai girman gaske, kana kuma ta yi hijira tare da shi zuwa Madina. Sannan kuma an ruwaito cewa lokacin da ta rasu, Annabi (s.a.w.a.) yayi mata likkafani da rigarsa, sannan kuma lokacin da aka zo tona kabarinta, shi da kansa ya tona ainihin ramin da za'a kwantar da ita a ciki, sannan kuma bayan ya gama ya kwanta a ciki yana cewa: "Ya Allah Ka gafarta wa mahaifiyata Fatima bint Asad kuma Ka fadada makomarta". An ruwaito cewa, sahabbai (wasu sun ce Umar bn Khattab ne) sun tambayi Annabi (s.a.w.a.) cewa me yasa ya aikata hakan don kuwa ba su taba ganin ya aikata hakan ga wani ba, sai yace musu; wannan mace ta kasance uwata ce bayan rasuwar ainihin mahaifiyata, kuna na rufe ta ne da riga ta, don ta kasance mata garkuwa ranar lahira, kana kuma na kwanta cikin kabarinta ne, don Allah Ya dada fadada mata shi da kuma hana kasa matse ta, don kuwa ta kasance mafi kyautata min cikin bayin Allah bayan Abu Talib".

(3)- Kashful Ghummah na al-Arbili, juzu'i na 1, fasali kan Imam Ali (a.s.).

(4)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 9.

(5)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 9.

(6)- Surar Ra'ad 13: 7.

Mawallafi: Muhammad Auwal Bauchi
Source: www.alwilayahnews.net 

Tura tambaya