lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU

An hakaito cewa a wata rana wani yaro matashi ya ji rashin gamsuwa da yanda rayuwarsa take gudana da dukkanin abin da yake kewaye da shi, sai ya fara tunanin yanda zai canja yanayinsa, sai ya tafi wajen malaminsa ya yi masa bayanin halin da yake ciki da shawarar da ya yanke, sai wannan malami na sa ya yi masa nasiha da ya dibi gishiri cikin tafi hannu ya zuba cikin kofin ruwa sannan ya sha, yayin da wannan matashi ya dawo gida sai ya zartar da nasihar da malamin ya bashi, a wayewar gari sai ya koma wajen malamin ya tambaye shi yaya ya ji dandanon wannan ruwan gishirin? Sai matashin ya ce: kai gaskiya ya yi dandanon gishiri sosai raurau na ma kasa sha kwata-kwata, sai malamin ya yi murmushi sannan ya nemi daya daga dalibansa da ya dibi tafi hannu daga gishiri shima ya zuba cikin kogi, wannan saurayi da dalibin suka tafi bakin kogi tare wannan dalibi ya zuba wannan gishiri cikin kogin, sai malamin ya nemi  ya sha daga ruwan kogin , sai ya mika hannunsa ya debo ya sha, sai wannan malami ya tambaye shi yaya ya ji dandanon ruwan, sai ya ce gaskiya ya yi dadi matuka gashi kuma kamshi na tashi, sai ya kara tambayarsa shin kaji dandanon dukiya, sai matashin ya girgiza kansa yana mai korewa, a wannan lokaci sai malamin ya waiwaye shi cikin damuwa yace masa, lallai wahalhalu da radadin rayuwa suna kama da tacaccen gishiri , adadin radade radade da wahalhalu cikin rayuwa suna dai ke wanzuwa basu canjawa, sai dai cewa mu bama fahimtar dandanon wahalhalu bisa gwargwadon yalwar da muke sanya radadi, idan muka sanya dukkanin himmarmu muka bashi muhimmanci fiye da wanda ta cancanta  sai ya karu ya mamayi dukkanin rayuwarmu , idan bamu himmartu da shi muka gafala muka shagaltu da tunani cikin abubuwan da muka samu nasara bama zamu taba jin radadin ba, saboda haka lokacin da kake jin radadi da wahala abin da yafi kamata da kai shine ka fadada tunaninka cikin abubuwa ka da ka zama misalin kofi ka yi kokari ka zama misalin kogi mai gudana

Tura tambaya