lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 5 GA WATAN RABI’U AWWAL SHEKARA 1441

Magana cikin mukami na biyu cikin mas’alar bayyanar da karatun sallah da boye shi.

Wuri: Qum mai tsarki-Muntada Jabalul Amil tareda Assayid Adil-Alawi

Lokaci: karfe 8 na safiya bahasin fikhu, karfe 9 bahasin usul.

 

Cigaba kan bahasin da ya gabata cikin mas’alar bayyanar da karatun cikin sallah da biye shi yau Magana za ta kasance cikin mukami na biyu: shi ne bayanin wuraren da ake bayyanarwa da boyewa, cikin kowacce sallah cikin kowanne mahalli daga sallah hakika harshen riwayoyi ya sassaba cikin haka.

Amma ta fuskanin wuraren sallah hakika riwayoyi sun zo cikin wannan babi da bayani karara da cewa bayyanarwa da boyewa kadai dai suna kasancewa cikin karatu ma’ana karatu fatiha da sura cikin raka’o’i biyu na farko-farkon sallah.

Ingantacciayr riwayar Zurara ta biyu tana shiryarwa zuwa ga haka kamar yanda bayani ya gabata, haka zalika riwayar Muhammad Ibn Imran da Yahaya Ibn Aksam duk da cewa riwayoyin suna da raunin ta fuskar isnadi sai dai cewa tareda haka malamai sun yi aiki da su wanda hakan na gyara raunin da suke da shi kamar yanda hakan shi ne ra’ayinmu, da ba’arin wasu riwayoyi cikin babin sallar Juma’a da sallar jam’i kamar yanda ya zo cikin ingantacciyar riwayar Halabi: idan ka yi sallah bayan limamin da kake binsa kada ka kai karatu a bayansa, babu banbanci ka ji abin da yake karantawa ne ko baka ji ba, sai dai idan sallar ta kasance cikin sallolin da ake bayyanar da karatunta. Da waninta.1

Amma sauran Azkaru da ba karatu ba kamar zikirin da ake yi cikin ruku’i da sujjada da zaman tahiya da sallama, lallai cikinsu ya halasta ka zabi bayyanarwa ko boyewa sakamakon rashin dalili kan wajabcin bayyanarwa ko boyewa cikinsu, rashin dalili dalili kan babu shi, kamar yanda asali shi ne halasci duk sanda babu dalili, bisa riko da jumla daga riwayoyi da bayani karara ya zo cikinsu kan cikakken zabi cikin bayyanarwa ko boyewa, daga cikin riwayoyin akwai: ingantacciyar riwayar Aliyu Ibn Jafar da riwayar Aliyu Ibn Yakdinu, cikin riwayar Aliyu Ibn Jafar (a.s) ya ce: na tambaye shi dangane da mutum shin zai bayyanar da zaman tahiya da tasbihi cikin ruku’i da sujjada da addu’ar cikin kunuti? Sai ya ce: idan ya ga dama ya bayyanar idan ya ga dama ya boye.

A riwaya ta biyu: na tambayi Abu Hassan (a.s) shin ya halasta mutum ya bayyanar da zaman tahiya da tasbihin cikin ruku’i da sujjada da addu’ar kunuti? Sai ya ce: idan ya so ya bayyanar idan ya so ya boye.

Zahiri daga zikrin cikin ruku’i da sujjada da zaman tahiya ya kasance daga babin buga misali bawai kebancewa ba, daga nan kuma yake gamewa da hukuncin sallama da waninta bisa alkawarinsa na ma’auni.

Amma ta fuskar ayyana sallah, lallai bayani karara bai zo ba ciki hadisai kan haka sai dai cewa Siratul mutasharri’atu wacce ta hade da zamanin A’imma Ma’asumai amincin Allah ya kara tabbata a garesu tana shiryarwa zuwa ga haka, lallai ta gudana kan bayyanar da karatu cikin sallolin asubahi da raka’a ta bibiuyun farkon magariba da Isha’i da boye karatun cikin Azuhur da La’asar.

Da wannan ne yake bayyanuwa da kuma ayyanarw maudu’i cikin riwayoyin da suka cikin littafin Alwasa’ilul Shi’a (bayyanarwa cikin wurin da bai kamata a bayyanar ba) ko kuma (boye karatu a wurin da bai dace a boye shi ba) daga misalin wannan bayani za a san cewa sallah ta kasance kan sinfi biyu: ana bayyanarwa cikin wasu ba’ari sannan ana boyewa cikin daya ba’arin, kamar yanda yake a wannan zamani karkashin koyarwar makarantar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu.

 

Mukami na uku: cikin sallar Juma’a da Azuhur din cikinta:

Hakika manya-manyan malamai sun samu sabani cikin bayyanar da karatu da boye a ranar Juma’a, amma sallah Juma’a Mashhur din malamai daga cikinsu Akaramakallahu sun tafi kan mustahabbanci bayyanar da karatunta kamar yanda da yawan daga manyan malamai sukai da’awar tsayuwar Ijma’i kan haka kamar yanda ya zo cikin littafin Alkawa’id, daga Attazkiratu da Annihayatul Ahkam da Azzikra da Albayan da Jami’ul Makasid da wasunsu, daga Muhakkikul Hilli cikin littafin Almu’utabar: (malamai basu da sabani cikin wannan mas’ala) daga Attankihu: (malamai sun yi Ijma’i kansa) ijma’i tareda rabe-rabensa daga Mankuli da Muhassali ya nusantar kansa.

Kamar yanda jumlar nassoashi suka shiryar zuwa zuwa gareshi kamar misalin ingantacciyar riwayar Zuraratu daga Abu Jafar amincin Allah ya kara tabbata a gareshi cikin hadisin Juma’a ya ce: ana yin karatunta a bayyane.2

Da ingantacciyar riwayar Umar Ibn Yazidu ya ce: yan zauna tsakanin hudubobi biyu ya bayyanar da karatu.3

Da ingantacciyar riwayar Azrami daga Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya ce: idna ka riski limami ranar Juma’a alhalin ya rigaya ya gabace da raka’ar farko to ka kara raka’a daya kanta ka bayyanar da karatu.4 da wata riwayar dai.

Fuskar kafa dalili da riwayoyin: hakika zahirin hadisan suna shiryarwa kan wajabci, sai dai cewa malamai sun dora su kan mustahabbanci bisa shaidar ijma’i da akai da’awarsa cikin kalmomin malamai kamar yanda ya gabata.

Sai dai kuma Shaik Hassan Najafi mawallafin littafin Aljawahir ya yi munakasha kan ijma’in da yake shiryarwa kan wajabci da cewa cikin bayanai manyan malamai gabanin Muhakkikul Hilli (K) ba a samu bayani karara kan mustahabbanci, lallai shi ne na farkon wanda ya fara maganar mustahabbanci, bai nesanta ba ya zama abin da malaman suke nufa shi ne mudlakin rinjaya wanda yana iya haduwa da wajabci, sai ya zama an tafi kan wajabcin bayyanarwa cikin sallar Juma’ar kishiyar boyewa da yake cikin Azuhur wanin Juma’a.

Mawallafin Aljawahir (K) ya ce: (sai dai cewa kuma ni zatona abin da ake nufi daga gareshi shi ne mudlakin rinjaya kishiyar wajabci da boyewa cikin Azuhur cikin koma bayan ranar Juma’a sakamakon rashin samun bayani karara kan mustahabbanci gabanin Muhakkikul Hilli (K) ta fuskar da zai kasane ijm’a’i, na’am an hakaito daga Misbahul Shaik da kuma ishara da ta gabata, da littafin Assara’ir da Al’isbahu da Almuntaha: cewa dukkanin wadanda ake haddato ilimi daga garesu sun yi Ijma’i cewa zai bayyanar da karatu cikin sallar Juma’a, ban yi tuntube da maganar malamai ba cikin wajabci da rashin wajabci ba, bari dai cikinj littafin Kashaful Lisam yazo cewa: akasarin malamai sun ambaci bayyanarwa cikinsu kan fuskar da zata iya daukar wajabci.5

Assayid Hakim (K) ya tafi kai yana mai cewa: a wannan lokaci akwai ishkali cikin dauke hannu daga zahirin nassoshi- da suke shiryarwa kan wajabci da kasancewar umarni da shi da wajabci-cikin wannan mukami akwai wahamin hallara- da hani kamar yanda yake cikin ilimin usul, saboda haka baya shiryarwa kan wajabci_da ya tabbatu, da ba zai tattaro ko ina ba, ka lura sosai.6

Assayidul Ku’i (K) ya tafi kai yana mai cewa: abin da mawallafin Aljawahir ya fa’idantar ya da karfi matuka, babu abin da yake wajabta kau da kan Assayid daga zuhurin wannan hadisai cikin wajabci, sakamakon rashin tabbatar da tsayuwar Ijma’i kan sabanin haka, tafiya kan wajabci duk da cewa bai kasance Magana mafi karfi ba amma dai babu kokwanto cikin kasancewarsa Ahwadu.

Kamar yanda lallai Ijma’i daga dalili lubbi ya tabbatu to sai ayi riko da kadarul mutayakkan daga gareshi wanda ya kasance a wannan mukami shi ne mudlakin rinjaya wanda yake iya haduwa da wajabci, kamar yanda zuhuri yake gabatuwa a kansa, kamar yanda hakan yake sanannen al’amari wurin Dalibai (mu muna tareda zuhuri duk inda ya juya can zamu juya) ahwadu wujuban bayyanarwa cikin sallar Juma’a kamar yanda wannan shi ne ra’ayin da muka zaba, amma ra’ayin manyan malamai da manya biyu kan Urwatu kamar yanda zai zo:


([1]).الوسائل: باب 31 من أبواب الجماعة الحديث الأوّل والحادي عشر.

([2]).الوسائل: باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

([3]).الوسائل باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الرابع.

([4]).الوسائل باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الخامس.

([5]).الجواهر: 11: 133.

([6]).المستمسك: 6: 203

 

Tura tambaya