b rashin wajabcin ayyana tasbihi
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

rashin wajabcin ayyana tasbihi


Lokaci: 8-9 na safe.

Fikhu 32 14 Rabiu Awwal shekara 1442 hijiri.

Mas'ala 12: idan ya kawo zikiri daga sugra ko kubra fiye da sau daya baya wajaba kansa ayyana wajibi daga gareshi, bari abinda yafi zama ihtiyadi shine rashin wajabcin musammam idan ya ayyana shi a koma bayan na farko sakamakon tsammanin kasancewar na farko shine wajibi mudlakan, bari dia sakamakon tsammanin kasantuwar jam'in shine wajibi, sai ya kasance daga babin zabi tsakanin kawo kafa daya ko kafa uku ko biyar alal misali.

Ina cewa: magana na kasancewa kan abinda ya gabata da rassanta kanshi cikin zikirin ruku'u, lallai abinda yake wajibi daga gareshi shine kawo kafa daya, yin kafa uku yana daga mustahabbi da sunna haka yin kafa bakwai yana daga falala kamar yanda ya zo cikin hadisi mai daraja, da zai kawo fiye da kafa daya shin wajibi ne kansa ya ayyana adadin da yake wajibi daga cikinsu ko kuma kafa daya da ya fara karantawa daga ciki shine wajibi sauran kuma ya zama mustahabbi ko kuma dai yana da zabi tsakankaninsu, ko kuma zai niyyar baki dayansu a wajibi?

Akwai fuskoki cikin mas'alar: ta farko: wajabcin zabi tsakanin mafi karanci da mafi yawa, idan yayi niyyar zuwa da mafi yawa wajibi kansa ayyana niyyar wajabcinsa kamar yanda yake cikin mafi karanci.

Ta biyu: kafa itace wajibi abinda ya haura daga gareta mustahabbi ne tareda zabi kan maginar tabayun banbanta da juna tsakanin wajibi da mustahabbi a zati kamar banbantuwar nafilar Asubahi da farillar Asubahi.

Kan haka ne yake halasta yayi niyyar wajabci da kafa daya daga kowanne daga duk wanda yaso daga cikinsu na farko ne ko na tsakiya ko na karshe, hakama niyyar mustahabbi daga sauran da suka rage.

Ta uku: kamar fuska ta biyu ya zama kafa daya shine wajibi sauran da suka haura mustahabbi tareda zabar magina banbantuwa tsakankaninsu sai sai cewa baya daga tabayunil zati bari dai yana daga tabayunil Ardi daga fuskar banbantuwar hissosi da afrad dangane ga zuwa mafhumil kulli kamar dai banbantuwar Zaidu da Amru cikin mafhumin kasantuwa mutum na bai daya.

Kasantuwar hakkakuwar kulli dabi'I cikin fardi guda daya daga afradinsa umarni da shi yana wajabta abinda aka yi umarni ya zama shine dabi'I ba tareda sharadi ba wanda shine yake haduwa ya kuma kasance tareda na farko da sharadi, wannan shine abinda yake daidaita da zauna matsayarsa sakamakon karkatar wujudul dabi'I ya kuma dabbaku da dabi'atul hal kan afrad na farko ya kasance daga dabbakuwa ta dole da babu zabi cikinta da wadatarwa ta hankali sai ya zamana shine wajibi sauran abinda ya karu daga zikirin ya kasance mustahabbi.

Sai dai cewa ta yiwu wani yace ana kidaita shi daga wajibi na tilashi ko kuma tials kansa ya niyyaci zikirin farko sauran kuma da sunan mustahabbi, wannan yayi kama da abinda aka fadi cikin tasbihohi hudu cikin raka'a biyun karshe cikin salloli masu raka'a hudu tsakanin yin zikiri daya ko uku.

Amma fuska ta farko: an tafi kan faduwarta, sabida kadai hakan gasgatuwa ne cikin abubuwan da suke da samuwa da dangantaka da juna da kuma abinda yake cin gashin kansa kamar yanda yake a cikin mukaminmu saboda haka a hankalce fuskar farko tana koruwa cikin samammu masu cin gashin ka.

Na'am idan ya kasance mafi karanci ana la'akari da da sharadin la kamar yanda yake cikin kasaru da itmami, wannan da farko kenan: yana shiga kasan masu banbantuwa da juna bawai mafi karancin da mafi yawa masu dangantaka da juna ba, na biyu bata kasance fuskar da ake tsammani a wannan mukami sannan abinda yake bayyana daga nassoshi wannan babi kamar cikin fadinsa aminci ya tabbata a gareshi (idan daya cikin ukun ta tawaya lallai kashi daya daga sallarsa ya samu tawaya, idan biyu suka tawaya lallai ya rasa biyun ukun sallarsa, idan baiyi tasbihi ba to lallai baida sallah) kamar yanda ya zo cikin riwayar sallah a gida kamar yanda ya gabata, haka zalika abinda ya zo daga sababi da dalilin sanya tasbihi cikin ruku'u kamar yanda yake cikin riwayar Akabatu haka zalika abinda ya zo cikin mustahabbancin tsawaita ruku'u (Alwasa'il babi 6 daga abwabil ruku'i) shine fuska ta uku kamar yanda Almusannif ya ambata kuma tarkizin halin al'adar ma'abota shari'a yake nuni kai.

Amma abind aka hakaito daga zikira da cewa wajibi shine fuska ta farko sai dia cewa da zamu samu kishiyarta yanke sai muyi riko da ita matukar dai fuskar bata bayyana ba, sai dai idan abinda ya kasance a halin samun shubuha cikin dabbakawa, sai a lura sosai.

Sannan Almusannif ya tafi kan yin ihtiyadi ta hanyar rashin ayyana wajibi daga zikiri idan ya zabi fiye d adaya musammam ma idan ya ayyana wajibi cikin wanin na farko.

Dalili cikin hakan shine tsammanin kasancewa na farko matsayin wajibi kamar yanda ya zo cikin littafin Azzikra, ko kuma ya kasance daga baki dayan adadi zikirin daga babin zabi tsakanin mafi yawa da mafi karanci, a wannan lokacin babu wajabcin ayyanawa, kadai dai ayyana tana wajaba kansa idan wajibi ya kasance guda daya amma ba a kankin kansa ba yana da zabi cikin dabbaka shi wannan kuma bai tabbatu a mukaminmu.

Ra'ayin da muka zaba shine abinda Almusannif ya zaba.

Mas'ala 13: a halin larura da karancin lokaci yana halasta a takaita da yin tasbihatus sugra kafa daya (subhanallahi)

Ina cewa cikin cigaba kan gabar data gabata reshe kanta daga abinda ya gabata ya wadatar yin tasbihatul Kubra kafa guda sugra kafa uku ga wanda yake cikin zabi amma a halin larura da kuntatar lokaci lallai ya halasta a gareshi ya wadatu da yin sugra kafa daya tana isar masa (subhanallahi) kafa daya wannan shine abinda Mashhur suka tafi akai, kamar yanda Muhakkikul Awwal ya kafa dalili cikin littafin Almu'utabar da cewa kansa fatawar Malamai ta kasance, a cikin littafin Almuntaha ya danganta zuwa ga ittafaki ya tafi kan wajabcin tasbihi cikin ruku'u, a karshen maganarsa yace: (wadatuwa da kafa daya a halin larura shine abinda aka fa'idantu da shi daga ijma'i)

A zahiri wannan ijma'I yana daga ijma'ul madaraki ko kuma akwai tsammanin madarakiyya bisa riko da riwayoyi biyu a wannan mukami.

الأولى: صحيحة معاوية بن عمار عن أبي عبد الله عليه السلام قال: قلت له أدنى ما يجزى المريض في التسبيح في الركوع والسجود؟ قال: تسبيحة واحدة (الوسائل: باب 4 من أبواب الركوع الحديث 8).

Ta farko itace Sahihatu Mu'awiyatu Ibn Ammar daga Abu Abdullah (a.s) yace: nace masa menene mafi karancin abinda yake isarwa mara lafiya cikin tasbihi a ruku'u da sujjada? Sai yace tasbihi kada daya.

والثانية: مرسلة الصدوق قدس سره في الهداية قال: قال الصادق عليه السلام: سبّح في ركوعك ثلاثاً تقول سبحان ربي العظيم وبحمده  ـ إلى أن قال مفان قلت سبحان لله سبحان الله سبحان أجزاك، وتسبيحة واحدة تجزى للمعتلّ والمريض والمستعجل (المستدرك: باب 16 من أبواب الركوع الحديث 1 ـ الهداية: 136)

Ta biyu: Mursalatu Saduk (k.s) cikin littafin Ahidaya yace: Assadik (a.s) yace kayi tasbihi kafa uku cikin ruku'unka kace (subhana rabbiyal Azim wa bihamdihi.


Tura tambaya