lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Akhlak din husainiyya tare da samahatus shaik husaini ansariyan

 

 

Akhlak bahasi ne mai yalwa take ne mai fadi da ya ke tattaro dukkanin falalolin hali da dabbakasu cikin rayuwar zamantakewa da zartar da su duniyar hakika wacce muke rayuwa cikinta.

Idan kana son karanta daidaikun Akhlak tsuran karatu, lallai mas’alar tana kebantuwa da falsafa da mafhuman kwakwalwa, amma idan ka nufi dabbaka wadancan mafhuman da ciro surori da shahidai kansu da jikkantuwa da su cikin gamammiyar rayuwa, lallai al'amari yana fita daga surar da ke cikin kwakwalwa zuwa gasgatuwa, daga gundarin tsura zuwa hakika, daga nazariya ya zuwa dabbakuwa, wancan falsafa ta ilimi ga Akhlak, amma tsuran falsafar Akhlak bamu nufinta, saboda bama fa'idantuwa da ita cikin rayuwarmu sai dai idan mun riketa matsayin hanyar ilimi da ta kan shiriyarta mu dabbaka haruffanta da iyakokinta cikin rayuwarmu ta yau da gobe, wancan daidaiku da mafhuman wadanda aka gaza dabbaka su a kammale face mutane kammalallu cikin mutumtakarsu.

Kammalallen mutum: shi ne wannan wanda ya ke sauyawa daga samuwarsa ta kansa zuwa taken mutumtaka; saboda ya na fita daga zatinsa zuwa gaskiya zuwa fuskar gaskiya wanda ya ke bayyanata, sai ya zama wakilin gaskiya mihwari gare ta cikin baki dayan rayuwarsa, kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya fada kan Ali ibn abu dalib a lokuta da daman gaske cikin wani hadisi:  

 

 (( علي مع الحقّ والحقّ مع علي يدور معه حيثما دار ))

Ali ya na tare da gaskiya ita ma gaskiya tana tare da shi gaskiya tana binsa duk inda ya juya.

 

Imam Ali (as) ya zama mihwarin gaskiya gaskiya tana jujjuyawa tare da shi duk inda ya juya duk inda ya sauka, misalin wannan shaida mai albarka tana daga alama mutumtaka ta farko, mafi girman mutumtaka da  bil adam ya sani tsahon zamanunnuka, cikin hakkin halifan manzon Allah (s.a.w) da wasiyinsa imami jagoran al'umma bayansa, tana bamu wasu isharorin haske, da wani yanayi na tsarkaka da take kewaye da wancan mutumtaka ta musammam, sai ta jingina wani kebantaccen haskaka da habbaka kansu da rayuwar dukkanin al'umma.

Imami bayan manzo: shi ne wannan mutumin kammalalle cikin al'ummar musulmi, shi ne tsollluwar kimar falala madaukakiya ga al'umma haka ma shi ne madaukakiyar tuta mai filfilawa  wacce al'umma ke rikarta don shiriyuwa da shiriya da haskakuwa, bazai yiwu ta kasance dayantacciya madaukakiya  bai munana ba bai munanawa wasu, wannan  yana sanya ka cikin halin dako da tsimayi ga kanka da ayyukanka kowanne lokaci, kai hatta kalmominka wajibi su kasance aunannu da mau'aunin zinare.

An rawaito wata waka daga imam Ali (as) da wannan ma'ana cikin fadin da ake danganta masa:

ويُروى عن الإمام× شعراً بهذا المعنى:

أفلحَ عبدٌ كُشف ال     ـغطاءُ عنهُ ففطن

وقرّ عيناً مَنْ رأى     أنّ البلاءَ في اللسن

فما زنَ ألفاظه         في كلّ وقتٍ ووزن

وخافَ من لسانه     غرباً حديداً فخزن(

Mafi rabauta bawa shi ne wanda aka yaye rufi daga barinsa sai ya basirantu.

Idaniyarsa ta sanyaya wanda ya ga cewa dukkanin bala'I na kan harshe.

Ya….lafuzzansa cikin kowanne lokaci ya auna su.

Ya ji tsorata daga kaifin harshensa sai ya taskace shi.

 

rabautaccen bawa: shi ne wannan da aka dage masa labule daga barin gaban idanuwansa da basirarsa. Sai ya gano cewa aibobin dake tattare da harshe sunfi kisa da hatsari daga sukan da mashi ke yiwa mutum, saboda haka nema ya auna harshensa bai magana face tare da ambaton Allah matsarkakiko kuma da abin da zai taimake shi ya amfanar da sh, ya taskace shi tsakanin saman bakinsa da kasansa cikin koma bayan wadannan muhallai karantattu.

Wannan hadisi yana da tsawaita bayani cikin mukamin tarbiyya  ga imam husaini (as) zamu da magana kan wannan hadisi nan gaba lokacin bayani kan nafsu dinsa tsarkakka da izinin Allah, sai dai cewa gabanin tsallakawa ya kai dan'uwana mai karamci, na nakashceka wannan al'amari da ya karanta wanda ya ke bayyana girman shugaban samarin aljanna, da zurfafar girmamawarsa ga ma'abota ilimi da adabi

 

تيُقال: إنّ أعرابياً جاء الحسين بن علي× وقال: يابن رسول الله  قد ضمنتُ دية كاملة وعجزت عن أدائها، فقلت في نفسي: أسأل أكرم الناس، وما رأيت أكرم من أهل بيت رسول الله|.

فقال الإمام الحسين×: (( يا أخا العرب، أسألك عن ثلاث مسائل، فإن أجبت عن واحدة أعطيتك ثلث المال، وإن أجبت عن اثنتين أعطيتك ثلثي المال، وإن أجبت عن الكلّ أعطيتك الكلّ )).

فقال الأعرابي: يابن رسول الله، أمثلك يسأل مثلي وأنت من أهل بيت العلم والشرف؟!

فقال الحسين×: (( بلى، سمعتُ جدّي رسول الله| يقول: المعروف بقدر المعرفة )).

فقال الأعرابي: سلْ عمّا بدا لك، فإن أجبتُ وإلاّ تعلّمتُ منك، ولا قوّة إلاّ بالله.

فقال الإمام: (( أيُّ الأعمالِ أفضلُ؟

Ance wani balaraben kauye ya je wajen imam husaini ibn Ali (as) sai ya ce: ya dan manzon Allah (sa.w) hakika ni na laminci wata kammalalliyardiyya sai dai cewa kuma na gaza bayarwa, sai cikin zuciyata na c: zan roki mafi karamcin mutane, banga wani mutum mafi karamci ba daga Ahlil-baiti rasulillah. Sai imam husaini (as) ya kai dan'uwa balarabe, zan tambayeka tambayoyi guda uku, idan ka amsa daya daga cikinsu zan baka daya bisa ukun kudin, idan ka amsa biyu daga ciki zan baka biyu cikin uku idan kuma ka amsa duka zan baka dukkanin kudin.

Sai wannan balaraben akuyen ya ce: ya dan manzon Allah (s.a.w) yanzu mutum irinka ne zai tambayi mutum irina kai kana daga Ahlin gidan ilimi da daukaka?

Sai imam husaini (as) ya ce eh, naji kakana manzon Allah (s.a.w) yana cewa: kyauta tana ta dogara da gwargwadon ma'arifa, sai wannan balaraben kauyen ya ce yi tambayar da kake son yi, idan na iya amsa ta kaga na koyi ilimi daga gareka babu karfi sai da Allah.

Sai imam ya ce: wanne ayyukan suka fi falala?

 

فقال الأعرابي: الإيمان بالله.

فقال الإمام: (( فَما النَّجاةُ منَ المهلَكة؟ )).

فقال الأعرابي: الثقة بالله

Sai balaraben kauye ya ce: imani da Allah.

Sai imam ya ce: mene ne tsira daga halaka?

Sai balaraben kauye ya ce; yarda da Allah

فقال الإمام: (( فَما يُزيَّنُ الرَّجُلَ؟ )).

فقال الأعرابي: علم معه حلم.

فقال الإمام: (( فَإنْ أخْطأهُ ذلِكَ؟ )).

فقال الأعرابي: مال معه مروءة.

فقال الإمام: (( فَإنْ أخْطأهُ ذلِك؟ )).

فقال الأعرابي: فقرٌ معه صبر.

فقال الإمام: (( فَإنْ أخْطأهُ ذلِكَ؟

فقال الأعرابي: فصاعقة تنزل عليه من السماء فتحرقه ؛ فإنّه أهلٌ لذلك

Sai imam ya ce: wanne abu ne yake kyawunta `da namiji?

Sai balaraben kauye ya ce: ilimi wanda yake tare da hakuri.

Sai imam ya ce: idan hakan bai samu ba  fa?

Sai balaraben kauye ya ce: kudi wanda yake tare da muru'a.

Sai imam ya ce: idan hakan bai samu ba fa?

 Sai balaraben kauye ya ce: talauci wanda yake tare da hakuri.

Sai imam ya ce: idan hakan bai samu ba fa?

Sai balaraben kauye ya ce: tsawa daga sama zata sauko kansa ta kona shi, lallai shi hya cancanci hakan.

فضحك الإمام الحسين× ورمى إليه بصرّة فيها ألف دينار، وأعطاه خاتمه وفيه فصٌّ قيمته مئتا درهم، وقال: (( يا أعرابِيّ، أعْطِ الذَّهبَ إلى غُرَمائِك، واصْرِفِ الخاتَمَ في نفَقَتِكَ )).

فأخذه الأعرابي وانصرف وهو يقول: ( اللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُ )

Sai imam husaini (as) ya yi dariya ya jefawa wannan balaraben kauye wata jaka wanda cikin akwai dinare dubu, sannan ya bashi zobensa da yake da dutse wanda kimarsa ta kai dirhami dari biyu ya ce: ya kai wannan balaben kauye ka bada zinaren ga masu binka bashi, sannan ka yi amfani da hatimin cikin bukatarka, balaraben kauye ya karba ya dauka ya juya ya tafi yana halin fadin: Allah ne mafi sanin inda yake ajiye sakonsa.

Shin ka taba jin irin wannan darasi na ilimi da aiki, da wannan madaukakiyar dabi'a c, wadannan madaukaka dabi'u da halaye, da wannan uslubin tarbiyya?

Imami mai girma (as) tun farko ya san adabi daga wancan balaraben kauye, ya kiradadi kaifin basira dake cikinsa da kyawun tarbiyya, sai dai cewa ya nufi koyar da mutanen da ke kewaye da shi ko kuma al'umma da wadanda za su bayansa da wannan saukakken uslubin tattaunawa da yake yaye bayyanuwar imam (as) da zurfin karamcinsa da tawali'unsa ga al'ummarsa musammam wanda ya zo masa da bukata, sai ya fitar da abinda yake tattare da shi daga kaifin basiara da ilimi, sannan ya bashi abinda ya nema daga gare shi daga kudi da tarkacen duniya.

ba za ace cikin mu'amalar da imam ya yiwa wannan mutumin ba akwai wulakanci ba, Allah ya tsari imam (as) daga haka; shi ne wanda kan wannan babi yake cewa:   

 (( صاحبُ الحاجَةِ لَمْ يُكرِمْ وجْهَهُ عَنْ سُؤالِكَ، فَأكرِمْ وَجْهَكَ عَنْ رَدِّهِ ))

Ma'abocin bukata bai karrama fuskarsa daga rokonka, saboda haka kai ka karrama fuskarka daga barin korarsa.

Da wannan uslubi da wannan hanya ya karrama balaraben kauye matukar karamci lokacin da ya bayyanar da falalarsa da iliminsa a fili tsakankanin mutane, kissarsa da maganarsa ta zama daga sunna da ilimin da imam husaini (as) ya bari, ya isar masa alfahari daga wata nahiyar lallai wannan mutumin ya karbi kudi bisa cancantarsa, saboda amsa tambayoyi ukun da ya yi, wannan wani darasi ne daga imam da cewa lallai mu ajiye dukkanin al'amuranmu na sakafa da ilimi inda suka dace da ajiyewa, domin a girmama kowanne mutum gwargwadon iliminsa da mustawarsa ta sakafa da imani da ruhi.

 

Yin kyauta gwargwadon ma'arifa:

Wannan ma wani labara ne da riwaya daban daga imam husaini (as) ta yiwu ta zama daga mafi kyawun da kammala daga riwayar da ta ambatinta ya gabata, zan nakalto maka ita ya kai aboki mai karatu mai girma don karkayi zaton cewa kissa daya rak riwaya da ba ta da ta biyu.

.

روي أنّ أعرابياً من البادية قصد الإمام الحسين× فسلَّم عليه فرَّد عليه السّلام وقال: (( يا أعرابِيُّ، فيمَ قَصَدْتَنا؟

قال: قصدتك في دية مسلّمة إلى أهلها.

قال×: (( أقَصدْتَ أحَداً قَبْلي؟ )).

قال: قصدت عتبة بن أبي سفيان فأعطاني خمسين ديناراً فرددتها عليه، وقلت له: لأقصدنَّ مَنْ هو خير منك وأكرم

An rawaito cewa wani balarabe daga kauye ya  je wajen imam husaini (as) sai yayi masa sallama sai imam ya amsa masa sallama ya ce: ya kai wannan balaraben kauye mene ne ya kawo ka wajenmu? Sai ya ce: na zo wajneka ne cika wata diyya da za mika zuwa ga ahlinta.

Sai imam (as) ya ce masa; shin kace wajen wani gabani na?

Ya ce: na wajen utuba ibn abu sufyanu sai ya bani dinare hamsin sai na mayar masa, nace masa: zan tafi wajen wanda yafi alheri daga gare ka.

قال عتبة: ومَنْ هو خير منّي

وأكرم لا أُمَّ لك؟

فقلت: إمّا الحسين بن عليّ، وإمّا عبد الله بن جعفر ( ابن أبي طالب )، وقد أتيتك بدءاً لتقيم بها عمود ظهري، وتردّني إلى أهلي.

فقال الحسين×: (( والذي فَلَقَ الحبَّةَ، وبْرَأ النَّسَمَةَ، وَتَجَلّى بالعظَمَةِ، ما في مِلْكِ ابْنِ بنتِ نبيّكَ إلاّ مئِتا دينارِ فأعطِهِ إيّاه يا غلامُ، وإنّي أسْألُكَ عن ثلاثِ خِصالٍ إنْ أنتَ أجبتَني عنْها أتْمَمتُها خَمْسَمئةَ دينارٍ )).

فقال الأعرابي: أكلّ ذلك احتياجاً إلى علمي، أنتم أهل بيت النُبُوَّة، ومعدن الرسالة، ومختلف الملائكة؟!

فقال الإمام الحسين×: (( لا، ولكنْ سَمِعتُ جدّي رسول الله| يقول: أعطوا المعروفَ بقَدَرِ المعْرِفَة )).

فقال الأعرابي: فسلْ، ولا حول ولا قوةّ إلاّ بالله

فقال الإمام الحسين×: (( ما أنْجى مِنَ الهَلَكَةِ؟

Sai utuba ya ce: wane ne mafi alheri daga gare ni yafi karamci daga gare ni ya kai mutumin wofi?

Sai nace masa: imam husaini ibn Ali (as) ko kuma Abdullahi ibn Jafar ibn abi dalib, hakika na zo maka domin ka mikar da kashin gadon bayana, ka komar dani wajen iyalina.

Sai imam husaini ya ce: na rantse da wanda ya kagi kwaya ya kirkiri mutum ya yi tajalli da girma, babu abinda ke karkashin ikon `dan `yar annbainka face dinare dari biyu zan mikawa hadimina idan ka amsa ka masa mini abubuwa dabi'u uku zan cika ya zama dinare dari biyar! Sai balaraben kauye ya ce: shin dukkanin wannan bukatuwa ne zuwa ga ilimina, ai kune ahlin gidan annabi ma'adanin sako, masaukin mala'iku?

Sai imam husaini (as) ya ce:  a a sai dai cewa na ji manzon Allah yana cewa ku bada kyauta kan gwargwadon ma'arifa, sai balaraben kauye ya ce: yi tambayar, lallai babu tsimi babu dabara sai da Allah.

Sai imam husaini(as) wanne abu ne yafi tseratarwa daga halaka?

فقال: التوكّل على الله.

فقال×: (( ما أرْوَحُ للِمُهمِّ؟ )).

فقال: الثّقة بالنفس

Sai balaraben kauye ya ce:dogara da Allah.

Sai imam (as) ya ce: wanne abu nea yafi hutu ga muhimmi?

Sai ya ce: yarda da kai.

فقال×: (( أيُّ شيءٍ خيرٌ للعبدِ في حياتهِ؟ )).

قال: عقل يزينه حلم.

فقال×: (( فَإنْ خانهُ ذلكَ؟ )).

فقال: مال يزينه سخاء وسعة.

فقال×: (( فإنْ أخْطأهُ ذلك؟ )).

قال: الموت والفناء خير له من الحياة والبقاء.

قال الراوي: فناوله الحسين خاتمه وقال: (( بعهُ بمئة دينارٍ )). وناوله سيفه، وقال: (( بعْهُ بمئتي دينارٍ، واذهبْ فقدْ أتْممتُ لكَ خمسمئة دينارٍ

Sai ya ce: wanne abu ne yafi zama alheri ga bawa cikin rayuwarsa?

Sai ya ce: hankali wanda hakuri ke kayata shi,

Sai ya ce: idan hakan bai samu ba fa?

Sai ya ce: dukiya da kyauta da yalwatuwake kayata ta.

Sai ya ce: idan hakan bai samu ba fa?

Sai ya ce: mutuwa da karewa sun fi zama alheri gare shi daga rayuwa da wanzuwa.

Mai riwaya ya ce: sai imam husaini (as) ya bashi hatiminsa ya ce: ka sai da shi dinare dari biyu ya mika masa takobinsa ya ce: ka saida ita da dinare dari biyu, ka tafi tabbas na cika maka dinare dari biyar.

Sai wannan balarabe ya sabi waka yana cewa:

 

فأنشأ الأعرابي يقول:

قلقتُ وما هاجني مقلقُ     وما بي سقامٌ ولا موبقُ

ولكن طربتُ لآلِ الرَّسول     ففاجأني الشعرُ والمنطقُ

فأنتَ الهمامُ وبدرُ الظلام     ومُعطي الأنامَ إذا أملقوا

أبوكَ الذي فازَ بالمكرمات     فقصَّرَ عن وصفهِ السبُّقُ

وأنتَ سبقتَ إلى الطيّبات        فأنتَ الجوادُ وما تلحقُ

بكم فتحَ اللهُ بابَ الهدى     وبابُ الضلالِ بكم مغلَقُ(

Na damu alhalin wani abu mai sanya damuwa bai zakke mini ba kuma banda ciwo babu wani mai halakarwa gareni.

Sai dai cewana yi shauki ga iyalan manzo sai waka da furuci suka zomi bagtatan.

Kai watan ke haskaka ne cikin duhun dare kai ne mai baiwa mutane kyauta idan suka bukatu.

Babanka shi ne wanda ya rabauta da karamci wadanda suka gabata sukai kasa agwiwa cikin siffanta sh.

Kai ne wand aka gabata zuwa kyawawa kai ingarma ne ba iya riskarka.

Daku Allah ya bude kofar shiriya da ku kuma ya rufe kofar bata.

Wadannan darasussuka ya kama a yada su duniya domin hanyar Ahlil-baiti ta zama sananniya.

Akwai wata riwaya da take kusa da wannan wacce liatattafan tarihi da falaloli suka rawaito su ban kawo su ba sakamakon wadatuwa da wannan darasi na tarbiyya.

Lallai darussan Akhlak suna da kyawunta da kayatarwa musammam ma idan aka danganta su ga imam husaini (as) cikin girmama ilimi da himmatuwa da sakafa, da mutunta mai neman ilimi tare da dukkanin kaskantar a kai da dadadawa da bayyanuwa bas u da misali, amincin Allah gareka ya Abu Abdullah husaini almazlum.

Tura tambaya