lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami

Ya Allah ka fitar da ni daga duhhan wahami, ka karrama ni da hasken fahimta, ya Allah ka bude mana kofofin rahamar ka, ka rarraba mana taskokin ilumummuka da rahamar ka ya mafi jinkan masu jin kai.

Ka sani shi dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami tana iya tukewa zuwa ga galabar wahami da samun ikonsa kan hankali, wannan yana daga cikin mafi hatsari da halaka, lallai yanda lamarin yake mutum zai zama yana daukar abin da ba ilimi ba a matsayin ilimi, wanda hakan na biye da kufaifayen ilimi, ya tsammaci cewa shi yana kyawunta aiki.

Ta yiwu wanda yake da ba’arin wasu daga ilimummuka da mushahada ya jarrabtu da wahamai da hiyalai da kurafat da karairayi, sababin hakan yana komawa zuwa ga kasantuwar mutum bai yi amfani da karfin hankalinsa ba da mustawar da ya dace yayi amfani da shi, har wahami ya wayi gari yana mai galaba kan hankalinsa, bai buya ba mabiya wahami duk da kasantuwarsu cikin surar mutane sai suna da tanadin riskar ayarin cikakkun mutane da zukata masu furuci masu riskar gundarin abubuwa, tare da haka su basu tsallake madaukakan tsanuka ba cikin martabobin nafsun dan Adam, da kuma kaiwa ga tsololuwar kamala tare da wahamai.

Bayanin haka: shi ne cewa shi mutum cikin zirinsa na zahiri da tsarin hallittarsa a zahirinsa da badini yana dauke da gundarin girma, yana sassabawa a siffance da cikin zatinsa daga sauran halittu ma’abota jikkuna, sakamakon wannan tsarkakken jauhari da ya kasance cikinsa ya fifitu daga halittu marasa baki da tsirrai da daskararrun abubuwa. Dama sauran halittu ma’abota jiki ya fifitu da karamci da falala da daraja, hakika Allah ya karrama dan Adam da karamomi, daga cikin mafi girmansu da kyawunsu shi ne hankali, shi hankali shi fitilace mai haskaka cikin maslakai da hanyoyin rayuwar mutum.

Wannan itace marainiyar zinariya kwaya daya rak ma’ana nafsu din mutum da ta sauko daga daukaka daga madaukaka, hakika ta fifita daga waninta cikin kausin nuzuli da su’udi da abubuwa guda biyu:

1- hankalta da riska mafahim da ma’anoni mujarradai da kulliyat, da riskar hakika kamar yanda suke.

2-Kubutuwa da fitar da iradar hankali daga datti da shubuha cikin janyo abubuwan da suka dace da kuma abubuwan da suke dadadawa nafsu, ana kiran wadannan da sha’awa, kamar yanda cikinsu maunazorori suka afku. Su kuma ana kiransu da fushi, dan Adam cikin zubinsa Allah ya bashi hankali, bisa la’akarin da kasantuwarsa mutum, kuma ya bashi nafsu mai Magana da karfi na fushi da sha’awa bisa la’akari da janibin dabbantakarsa, lallai a ilimin mandik anyi ta’arifinsa da cewa shi dabbace mai Magana duk da cewa anyi ta’arifinsa a irfani da rayayye mai jin radadi.

Kebantaccen jauhari da yake cikin mutum wanda ake ta’arifinsa cikin isdilahin addinai a matsayin ruhi. Sannan akai ta’arifinsa a falsafa da nafsul nadika, wacce take mallakar karfin idrakil kulli. Ita tana daga tabbatattun abubuwa, da kuma idrakat na juzu’iyya wanda su suna iya canjawa, mutum yana iya kaiwa ga nafsul insaniyya ba ta hanyar tsanukan waje ba, sai dai cewa ta biyu samun yana kasancewa ta hanyar tsanukan da kayan aiki na waje da karfin jiki.      

Cikin wannan siyaki wasu ba'arin malaman falsafa suke cewa: ita nafsu tana iya riskar kulliyat da zatinta sannan tana riskar juzu'iyat da kayan aikin ta. Sannan shi mutum yana da janibin bukatuwa da tsirrai daga karfinsa na cimaka da girmau da haifau  janibin da yayi tarayya da sauran dabbobi, sakamakon kasantuwarsa jiki mai girma mai motsi da iradarsa, hakama yana tattare da janibinsa na mutum kamar misalin riskar kulliyat da juzu'iyat , shi jiki ne mai girma yana motsi da irada kuma mai magana, sai ya zamanto ya tattaro janibin bukatuwarsa da tsirrai sakamakon cimakau da girmau da kuma dabbantaka da `yan Adamtaka, kai hatta madawwamiyar rayuwa.

 (أحياء عند ربهم يرزقون)

Su rayayyu ne suna azurta daga ubangijinsu.

Rayuwar ubangiji tana tajalli cikinsa kamar yanda sunayensa da siffofinsa girmansa ya girmama suke tajalli cikinsa, daga nan mutum ya zamanto rayayye mai imani da Allah, rayuwar Allah kadai dai shi ne iliminsa da kudurarsa, lallai shi masanin komai ne kuma mai iko kan komai ne, sannan dukkanin wanda ya kasance kwatankwacinsa haka to ya kasance rayayye cikin zatinsa da siffarsa da ayyukansa.

Sannan asalan tsirrai karfi guda uku: cimakau girmau haifau, ita cimakau tana da abubuwa guda hudu da ta kebantu da su: jawau turau kamau nikau, sannan haifau tana da karfi  guda biyu: samau rarrabau, abin da ake nufi da na farko shi ne tana sanya yankunan abinci su zamanto masu ikon karbar surar kwayar halitta, sannan ta biyu tana sanya su masu iko kan karbar wata surar daban.

Amma janibin rayuwar dabbanci, lallai ita tana tarayya da mutum cikin karfi goma sannanu, daga cikinsu akwai na zahiri, sune ganau jiyau kamsau dandanau tabau, biyar daga cikinsu kuma na badini sune: na farko shi ne shi ne hissi mushtarak wanda ake kira da (bindasiyya) wanda yake riskar surori na zahiri domin ya dauko ya kaisu zuwa mataskatar hiyali da karfi na hiyali, hiyali wanda yake taskace surori da gadinsu shi ne mataskatar hissi mushtarak , sai kuma karfi na wahami wanda yake kiyaye hissi na juzu'i, sai na biyar wato karfi mai tasarrufi wanda yake tattara dukkanin ababen da aka riska aka taskace su, sannan ya sadarsu da sashensu tare da sashe domin fitar da hukunci daga gare su, idan tushen hukunci ya kasance daga wahami, sai a kira shi da hiyali, idan kuma ya kasance daga karfi na hankali sai a kira shi da tunani,

Gudummawar tunani cikin rayuwar mutum:

Sannan ka sani shi hankaltar mafhumai kulli da riskar tabbatattun abubuwa wanda yake tajalli cikin nafsul nadik, kadai dai yana samuwa ne daga hanyar datacaccen tunani da ingantaccen ra'ayi, sannan shi datacaccen tunani yana kasantuwa cikin ilimi mai amfani, shi ilimi bai kasantuwa face da lafiyayyen hankali, bawai cikin sauki ake keta hijaban wahami da suke hana gano tabbatattun abubuwa da gasgatattun ilimummuka da fannoni masu kyawu ba, face da hankali da ilimi da ma'arifa, lallai karfi na wahamai suma suna riskar abubuwa na zahiri da wanda bana zahiri ba, wadanda suka kasance cikin na zahiri, hukunci juzu'i na gangarowa daga garesu, sai dai cewa kawai wani lokaci a mukamin dauki ba dadi da fafatawa da hankali sai ka samu yayi galaba kansa ya zauna kan karagar ilimi ya karbe ragamar tafiyar da lamurra a hannunsa, sai ya rattaba kufaifayin ilimi kan hukuncinsa, sai ya dinga sawwalawa da kayatar da karya da rigar gaskiya, wannan duka na daga sawwale-sawwalen nafsu cikin mutum, shi wahami yana amfanarwa cikin dabbobi domin tseratar da akuya daga harin kura, amma cikin mutum yana cutar da shi musammam ma lokacin jidalinsa d adauki ba dadi tare da hankali da abubuwa na hankali, sakamakon su wahamai gangar jiki ne na samuwa, suna daga karfi na badini cikin mutum kamar yanda bayani ya gabata, idan suka karbi ragamar mulki sai su kasance sun mamaye ko ina sun hana hankali sakat da taka rawarsa, shi wahami bai imani da hankali ba bai sallama mishi ba, bai mika wuya ga hukuncinsa a ko ina, kai hatta a ba'arin muhallai wahami kan kasancewa shugaba hatta tare da samuwar jahilci da wauta da gabunta, daga cikin abin da yake gajiyar da hankali da yin galaba kan hukunce-hukuncensa, kamar misalin mutum da yake tsoran kwana tare da gawa ciki daki daya, adaidai lokacin da yana da yakini da hankalinsa cewa gawa bata cutarwa bata kuma amfanarwa, gawar bata bakin komai face daskararren abu daga sauran daskararrun abubuwa kamar misalin bangon da yake kishingide jikinsa ko kuma misalin tabarmar da yake zaune kanta, sai dai cewa tare da hakan yana jin tsoro sakamakon ya ajiye aiki da hankali ya mika wuya ga wahami.

Misalin wannan shi ne abin da muke gani cewa kowa da kowa ya sancewa shi mutum matalauci ne  cikin zatinsa, bai da amfanawar ballantana cutarwa, bai da karfi babu dabara face da Allah madaukaki, sai dai cewa sakamakon wahami sai muke neman biyan bukatarmu daga gare shi, ko kuma mu sanya shi a mahallin ubangijintaka da Allantaka sakamakon wahaminmu mu fitar shi daga haddinsa na mutum da dabba, hakan kuskure ne matukar bai kasance shingagge da shingen Allah ba da iliminsa daga ubangiji mai hikima ba.

Wahami wani lokacin kan sanya mutum cikin fursun dinsa daddaure da sasarinsa shi ne abin da ake kira da shaidan mai tsaurin kai, kadai dai zaka iya saninsa daga kufaifayinsa da waswasinsa da sawwale-sawwalensa.

Wazifofin da suka hau kan hankali:

Daga cikin wazifofin hankali shi ne ma'abocin hankali ya ciratu daga riskarsa ga juzu'an abubuwa na zahiri ya zuwa mafhumai kulli, daga nan ne zai fara kaiwa ga kamsasar kamshim hakika, kamar misalin wanda yake hango kyalkyalin haske daga nesa. Kamar misalin dambar farawa da hattamawa da karshe, shi ilimi shi ne jarin hankali.

Sannan ka sani tsakanin nukdodi biyu daga bangarori biyu wato farawa da hattamawa shi ne samun ma'arifa, hanya daya rak wanda kuma itace tsani shi ne kaiwa ga ma'arifa, lallai ita ma'arifa ita ce misalin karfaffar igiya da waya da zata sadar tsakanin mai ilimi da ilimi da abin da ake son a sani, babu banbanci cikin kasantuwa a nukdar farawa ne ko hattamawa, duk sa'ailin da muka taka gaba zuwa ga abin da muke son sani a dunkule shima sai ya karo gaban kadan gare mu a dunkule, lallai zamu kara cika da ma'arifa da shi, mu san shi cikin kebantattunsa da juzu'ansa, to hakama idan muka nesantu daga nukda ma'arifarmu sai ta karantu iliminmu ya zama kamar misalin digo ne kan littafi ko kamar digon ruwa cikin kogi, daga cikin abubuwa da suke banbanta ilimi da ma'arifa shi ne cewa shi ilimi shi ne riskar kulliyat shi kuma ma'arifa riskar juzu'iyat.

Nukda day ace kawai ta yawaitu ne sakamakon jahiltar da jahilai sukai kanta da neman sanin su da tambayoyinsu kan hakikaninta da mahiyarta da abubuwan da suka kasantar da ita da juzu'anta

Ma'anonin hankali:

Sannan shi ilimi da ma'arifa kamar yanda ya gabata suna daga abubuwa guda da daya da suke da dab banbantuwa a kankin kansu ma'abota martabobi, wannan na daga abin da ya haifar da sassabawar mutane cikin hankulan su da mariskan su da tunanunnukan su da ra'ayoyin su, haka lamarin yake cikin hankali, mutane ba kudin goro suke ba, bai bai daya suke ba cikin hankulan su da ababen da hankalin su yake riska kai hatta cikin ma'arifofin su.

Hankali yana da ma'anoni daban-daban ta fuskanin daban-daban

Hankali a luggance: yana daga igiyar da ake yiwa rakumi dabaibayi da ita a kafa yayin da ake durkusar da shi kasa wanda hakan yana nuni da daure shi tamau ta yanda ba zai iya kwacewa ba.

Kamar yanda ya zo cikin littafin Mufradat Ragib: {Akalu} ana kiransa da matsayin wani karfi da yake tukewa don karbar ilimi, ana kiran ilimin da nutum ke fa'idantuwa da shi da wancan da hankali, saboda haka nema sarkin muminai Ali (a.s) ya ce:

 (العقل عقلان مطبوع ومسموع ـ ولا ينفع مسموع إذا لم يكن مطبوع)

Hankali kashi biyu ne akwai wanda ake tantancewa da shi, da kuma wanda ake ji da shi-wanda ake ji bai da wani amfani idan bai tare da na tantancewa ba.

 kan na farko ma'ana hankalin tantancewa manzon Allah (s.a.w) ya yi ishara da fadinsa:

(ما خلق الله خلقاً أكرم عليه من العقل).

Allah bai halicci wata halitta ba mafi karamci daga hankali ba.

Sannan kan na biyu ma'ana wanda ake ji ya yi ishara da fadinsa:

 (ما كسب أحد شيئاً أفضل من عقل يهديه إلى هدىً أو يردّه عن ردى).

Wani mutum bai tsiwirwiri wani abu ba mafi falalan daga hankali yana shiriyarwa zuwa shiriya ko kuma ya kubutar da shi daga halaka.

Wannan da ma'ana ta biyu shi ne ma'anar fadin sa madaukaki:

﴿وَتِلْكَ الأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ﴾

Wadancan misalai nada muke buga su babu masu hankaltar su sai masu ilimi.

Haka ya cikin suratul Ankabut:

 ﴿وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنْكَبُوتِ﴾.

Lallai mafi raunin gidaje shi ne gidan gizo-gizo.

Dukkanin wuraren da Allah yake zargin kafirai da rashin hankali to ishara ce zuwa kan na biyun bana farko ba:

﴿وَمَثَلُ الَّذِينَ كَفَرُوا كَمَثَلِ الَّذِي يَنْعِقُ﴾

Misalin wadanda suka kafirce kamar misalin wanda yake yin me!me! ne.

Zuwa fadinsa madukaki:

 ﴿صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لا يَعْقِلُونَ﴾

Baibaye kurmaye makafi su basa hankalta.

Kafirai yanada hankalin dabi'a wanda da shi ne Allah ya kallafa masa wazifa da kuma shi zai masa hisabi, koma bayan hankalin ji wanda shi ilimi ne mai amfani ga wanda ya san shi ya kuma yi aiki da shi, sannan duk wurin da aka dage alkalami sakamakon rashin hankali da yake da shi to ishara ce zuwa ga farko.

Asalin hankali a luggance shinhe kamewa da damkewa, kamar dabaibaye rakumi da dabaibayi, ana cewa mace ta daure gashinta ko ace ya yiwa bakinsa takunmkumi (akkala lisanahu kaffahu) ko (akkalatil mar'atu sha'araha) dss…

Hankali a isdilahance suna da ma'anoni masu banbanci da juna gwagwadon sassabawar isdilahohi, hankali a cikin isdilahin ilimin fikihu da usul ya saba da ma'anar hankali a isdilahin ilimin falsafa da mandik, haka dai kamar yanda ya zo cikin tafsirai da madaukakan hadisai.

Ya zo cikin hikima muta'aliya: da gundarin jauhari wanda yake cikin gangarowar ayyukan mutum karkashin zabin sa wanda sababin sa ne mutum yake bukatar karfin kayan aiki na zahiri da na badini da hawasul Ashara kamar yanda bayani ya gabata a muhallinsa.

Wurin ba'arin Arifai sun yi bayanin hankali a matsayin haske na ruhi wanda da sababinsa nafsu ke samun idraki da riskantattu, an ce da hankali a ke riskar kulliyat abin da yake kara kyawuntar tunani da zurfafar sa da kyawuntar tafiyarwa da gudanarwa, da istinbadi da da neman alfanu da tunkude cutuwa ga kankin kan mutum da sauran jama'a cikin al'amura na madiya da ma'anawiya, da tantance zance daga daidaituwa da kuskurewa hakama daga gaskiya da karya da bata da shiriya, da tanadin don karbar ilimummukan nazari da tafiyar da sana'o'i da cigabantar da su da habbaka su da dai makamantan haka.

Kashe-kashen hankali:

Sannan ka sani nafsun mutum tana da hankula guda biyu: hankalin nazari shi ne wanda ya ta'allaka da abin da za a iya sani, sai kuma hankalin aiki wanda ya ta'allaka da aiki da abin da za a aikata.

Kamar yanda nafsu take da martabobi da matakai da ake nadewa masu tari yawa kuma tana da martaba d atake ayyanuwa a kebance da kebantaccen suna tsakanin ayyanannu.

Hankalin nazari yanada martabobi hudu:

Na farko: tanadi domin neman hankaltau na farko ta hanyar mariskai biyar wanda ake kira da (akalul hayulani).

Na biyu; tana tanadi domin samun nazariyoyin hankali daga hankaltau da sanannu na fari-fari saki babu kaidi nbabu banbanci cikin kasantuwar su daga hanyar mariskai ko kuma tunani, shi ne abin da ake kira da (al'akalu bil malaka).

Na uku: tanadi domin halarto da nazariyoyi da aka tsiwirwira cikin kowanne lokaci ya so wadanda ake kira da (ala'akalu bil fi'ili).

Na hudu: canji abin da yake da tanadi da karfi nan gaba zuwa nan take, ma'ana karar da tanadi da nan gaba da halarto da tsiwirwirarrun ilimummuka da mushahada, wanda ake kiransa da (akalul mustafad)

A wani fadin cikin jumla shi ne cewa: shi hankali nazari ko dai cikin martabar nan take tsantsa ko kuma cikin martabar tanadi da zia karba nan gaba, shi ne ko dai nna kusa ko tsakatsaki ko na nesa, na farko: akalul mustafad, na biyu: akalul fi'il, na uku: akalul malaka, na hudu: akalul hayulani.

Amma martabobin hankalin aiki to guda hudu ne:

Na farko: tsarkake zahiri da amfani da ladubba cikin dabbaka koyarwar muslunci da hukunce-hukunce addini da shari'a, wadanda ake kiransu da: attajaliyatu.

Na biyu: tsarkake badini daga munanan dabi'u da siffofi marasa kyawu, wanda ake kira da: takliyatu, sai dai cewa abin da ya shahara kamar kuma yanda yake shi ne ra'ayinmu ita takliyatu cikin mukamin hankalin aiki tana gabatuwa kan ragowar martabobin.

Na uku: yiwa zuciya ado da falaloli da kamaloli da kyawawan dabi'u, shi ne abin da ake kira da : tahalli.

Na hudu: kaiwa zuwa ga mukamin fana'i cikin zatin Allah da wanzuwa tare da shi, sai ya zamanto iradarka ta kare ta narke cikin iradar Allah matsarkaki, babu abin da kake so face abin da Allah yake so, sai ka narke ka kare cikin hasken sa da kyawawan sunayen sa da madaukakan siffofin sa masu tajalli cikin shimfidaddiyar samuwa ta hakika, matsayi cikin kausul nuzuli zuwa duniyar nasutu cikin halittar Allah cikin littafin sa kur'ani mai girma cikin mafi daukakar halittun Allah Muhammad (s.a.w) da iyalan sa tsarkaka.

Babu kokwanto cewa ya zama dole cikin kashafin tabbatattun abubuwa da shuhudinsu da sanin juzu'ai da samun ilimi kan kulliyat dole ace hankali ya kasance jagora wanda shi ne tsantsar hankalin tsaftatacce daga dukkanin datti cikin kagar samuwar mutum cikin rayuwarsa tare da dukkanin sasanninta da fagagenta, lallai yanda lamarin yake shi ne da hasken hankali da kasantuiwa tare da shi launukan tabbatattun abubuwa ke banbancewa a fara jin kasmhin dandankewa daga gareta, ruhi ya kyawunta ya kammala da saninta har ta kai ga tsololuwar kamaloli kofar kausi biyu ko mafi kusa daga haka.          

اللهم أرزقنا عقلاً کاملاً ولبّاً راجحاً وقلباً زکيّاً وعزّاً باقیاً وأدباً بارعاً وعملاً کثيراً وإجعله لنا ولاتجعله علينا برحمتک يا أرحم الراحمين.

Ya Allah ka azurtamu da kammalallen hankali da tunani mai rinjaye da zuciya tsarkakka da izza madawwamiya da adabi mai kyawu da aiki mai kyawu, sannan ka sanya shi garemu ka da ka sanya shi kanmu da rahamarka ya

Tura tambaya