lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kalmar Ustaz Sayyid Adil-Alawi ga daliban makarantar tadabburul kur’an

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka ya ubangiji ka bude bakina da Kalmar shiriya ka kimsa mini tsoranka.

Ubangiji mai hikima cikin littafinsa mai girma yana cewa: 

 

 ( إِنَّ هَٰذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ )

Wannan littafi yana shiryarwa zuwa abinda yafi daidaituwa

 

Ya ku yan’uwa mata muminai masu naiman gaskiya da hakika..yaku almajirai masu tsoran Allah da izinin Allah, salamu Alaikum

Magana ta tareda ku zata kasance dangane da kur’ani mai girma, hakika Allah ya halicci mutane daga rai guda daya sannan daga wannan rai ya fitar mazaje da mata, saboda haka nafsun mutum nafsu ce guda daya rak ku bude kunnuwa ku saurare ni da kyau

Wannan nafsu guda daya ruhi daya daga Allah take ta kuma sauka ne daga madaukakin mahalli zuwa wannan duniya da keta duniyoyin haske, sa’ilin da ta sauka cikin duniya mafi kaskantar kaskantattu wacce itace wannan duniyar tamu bayan kasantuwa cikin mafi kyawun tsari da zubi bayan kasantuwa daga ruhin Allah da yayi huri cikinsa daga ruhinsa, wannan ruhi na Allah wanda shi madaukakin Mala’ika ne wato Jibra’il, Allah madaukakin sarki ya halicci mutum daga wannan nafsu ta ruhi da ruhaniya malukutiya sama’iya ta Allah madaukaki, sannan ta sauka ta keta duniyoyi har takai ga kausul nuzuli ya zuwa wannan duniya kanta ne ya kamata tayi su’udi ta hau domin Allah yana ce mata ki koma zuwa ga ubangijinki saboda ita dama daga ubangiji take gareshi kuma zata koma, wannan itace nafsun mutum ya zama dole ta koma zuwa ga Allah natsarkaki ta keta duniyoyi cikin kausinta na su’udi, wadannan duniyoyi daga cikinsu akwai duniyar kabari  barzahu da duniyar tashi daga kabari da alkiyama kamar yanda lokacin da ta sauka ta sauka zuw aga duniyar hankula da ruhi da inuwa da duniyar kwayar zarra da duniyar da muke ciki, a wannan lokaci wanna nafsu ta mutum da ruhinsa babu namiji gareta ballantana mace domin mazantaka da matantaka na kasantuwa cikin gangar jiki, jiki shine yake karbar namiji da mace shi ruhi abu guda ne bai da mace bai da namiji.

Sannan dole a tarbiyantar ruhi, ubangiji mai rainon talikai shine mai yin tarbiya na farko, sannan ita tarbiyar ubangiji tana tajalli cikin annabawansa da manzanninsa da litattafansa da wasiyyansa da malamai da shahidai da zababbu da rabautattu, kadia wadannan suna suke tarbiyantar da mutane suke tarbiyantar da ruhin mutum, ma’ana tarbiyar mutum babu banbanci cikin kasantuwarsa mace ko namiji, sannan duk wanda yayi Imani dag cikinku mace ko namiji yayi aiki nagari da sannu zamu raya shi rayuwa mai kyawu kadai tana cikin kur’ani da shiryarwarsa.. sannan shirywarsa da fari tana kasantuwa ne daga rahamar Allah da jin kansa, wani lokacin kuma tana kasantuwa cikin kasha biyu duk wanda ya karbi shiriyarsa ta farko da ma’anar nuna hanya lallai Allah zai datar da shi da karbar shiriya ta biyu  ya kara masa shiriya   

 

 ( وَالَّذِينَ اهْتَدَوْا زَادَهُمْ هُدًى

 

Kuma wadanda suka shiriyu zai kara musu shiriya.

 

Kur’ani mai girma littafi ne na shiriya mai gamewa daga jinkansa daga fuskanin wannan shiriya domin Allah matsarkaki yana cewa:

 

(شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِّلنَّاسِ )

 

Watan Ramadan wanda cikinsa ya kur’ani ya sauka shiriya ga mutane.

 

Ita gamammiyar shiriya ce ga dukkanin mutane bayan haka dukkanin ya samu dacewa da rungumar wannan shiriya domin nuna hanya lallai shi zai ga wannan hanya zai kuma tafi kanta kuma Allah zai taimaka masa zai isar da shi zuwa ga bainda yake nema wanda shine saduwa da Allah matsarkaki cikin aljanna da koramu a matsugunin gaskiya wurin sarki mai ikon yi. Allah matsarkakin sarki karkashin Imam zaman (as) ta yanda shine waliyin Allah mafi girma rike hannun shiriyayye ya kara masa shiriya.

`ya`yana ina rokon Allah ya datar daku cikin abinda cikinsa akwai ilimi mai amfani da aiki nagari cikin Imani da lura cikin kur’ani mai girma wannan kur’ani littafi mai katange dukkanin litattafan sama da kasa, yana da kariya bdomin shi littafi ne na kamala da kamalar litattafai babu wani littafi bayan kur’ani da yafi shi kammaluwa, shine karshen kamala, kamar yanda manzon Allah ba a samu wani annabi bayansa ba shine cikamakin annabawa da manzanni, sannan babu wata kamala face ta Allah, zuwa ga ubangijinka ne magaryar tukewa take tukewa, manzo mafi girmama shine mudlakin kamala cikin alamul imkan , kamar yanda Allah yake kamalul mudlak kuma mudlakul kamal cikin alamul wajibul wujud ga zatinsa  

Tura tambaya