lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Daukakar himma

Shine cewa mutum ya kasance ma’abocin madaukakiyar himma, mai zurfafa kallo da duba, kamar yanda sarkin muminai (as) yake gayawa dansa Muhammad Hanafiyya a fagen yaki:

«اُنظر إلى أقصى القوم »

Ka wurga kallonka cikin mafi nisan mutane.

Lallai hakika wanda yake daga kallon sa zuwa saman dutse hawan dutsen zai saukaka gareshi, ba zai tsora daga wahalhalun hawan ba da tsanantuwar hanyasra, ba zai kasance mai hakuri da kadan ba tareda saukaka mai yawa, ba zai jinkirta aikin yau zuwa gobe ba, ba zai jinkirta aikin yanzu-yanzu ba zuwa anjima, lallai cikin jinkiri akwai aibu, mafi alheri kyautata shine wanda ya kasance take, dukkanin anjima tana aikin ta, dole a mai da hankali cikin tafiya ba tareda yankewa ba, ba tare da jin tsoran mai tsoratarwa, ba tare da ja bay aba sakamakon kayoyin da ke kan hanya, dole ne mutum ya shallake duk wani shinge da Katanga da karfin niyya da azama da hakuri, shi fa lokaci kamar misalin takobi gayama jinni na wuce, idan baka yanke shi shi zai yanke ka, dare da rana na aiki cikinka saboda haka kai ma ka zage danste kayi aiki.

Tura tambaya