lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 24 MUHARRAM CIKIN MAS'ALAR HALASCIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA MUDLAKAN CIKIN SALLOLIN NAFILA KO DA KUWA YA KAI GA KARANTA RABI

Wuri: Qum mai tsarki cibaiyar Muntada Jabalul Amil Islami tareda-Smahatus Assayid Adil-Alawi.

Lokaci: karfe 8 na safiya.

Cigaba kan bahasinmu da ya gabata cikin mas'alar halascin yin uduli daga Sura zuwa wata mudlakan cikin sallolin nafilfili ko d kuwa ya kai ga karanta rabin sura da ya fara da ita da farko ko ma ya kai ga tsallake rabi, hakika manya-manyan malamai sun samu sabani cikin wannan mas'ala  a cikin Mustanad ya zabi hani kan maganar haramcin yanke nafilfili, da kuma halasci kan magana kan halascin yanke nafilfili sakamakon mas'alar yanke nafilfili mas'ala ce da malamai ke da sabani cikinta, wanda ya tafi kan halascin yankewa ya fadi abinda muke bahasi cikin kan halascin uduli mudlakan, wanda ya tafi kan hana yanke nafilfili ya fadi rashin halascin cikin wannan mukami na halascin uduli da rashinsa ko da kuwa ya kai ga karanta rabin surar ko ma ya keta rabi da dai abinda ya karu kan haka.

Fuska kan wannan ra'ayi: amma wanda ya haramta yanke nafilfili bisa riko da umumi da idlakin hadisai da ska zo cikin wannan babi da suke shiryarwa kan hana yankewa bayan keta rabin sura ko kuma hana yankewar iya cikin suratul Iklas da Fatiha mudlakan, kadai dai ya hana hakan ne daga dogaro da fuskar hani daga cigaba cikin sallah da cewa ka da ku gurbata ayyukanku babu banbanci cikin farilla ne ko nafila duk wanda ya rigaya ya fara to wajibi ya cika, ko kuma daga fuskar tabbatar da laifi da hani da cikin janyewa da uduli zuw aga wata sura da makamancin haka daga fuskoki da suke wajabta tabbatar da hani cikin nafilfili kan rashin halascin yankewa mudlakan.

Anyi ishkali kan wannan magana: lallai shi hanin bai da wata laka da mas'alar haramcin yankewa cikin nafilfili bari dai zahirin hadisan hani daga janyewa da uduli cikin halin kai wag a ga karanta rabin sura shi ne ayyanuwa cigaba da karanta surar da aya fara da ita sakamakon gasgatar misaltawa da ita da sauke nauyin da ya wajaba a kansa daga karanta sura, da zai janye yayi uduli zuwa wata surar da hakan ya lazimya misaltawa bayan misaltawa yin hakan kuma baya halasta, ka lura.

Ance: kadai dai mas'alar hani tana ginuwa kan uduli da kanyewa da kuma halasci cikin nafilfili kan mas'lar wajabcin karanta sura da rashin wajabcinsa cikin nafila, idan aka tafi kan wajabci sura to fa lallai zai zama an fadi halascin janyewa da uduli idan ya kai ga karanta rabin sura, idan kuma aka zabi rashin wajabcin sura cikinta, lallai cikin mukamin zai zama an zabi halascin uduli mudlakan ko da kuwa ya kai ga rabin sura.

Anyi ishkali kan wannan magana: kamar yanda yake cikin abinda ya gabata da kasantuwar abinda muke cikinsa daga hani bai da wata alaka da mas'alar wajabcin sura da rashinsa cikin nafila, saboda wasu suka zabi haramcin uduli da janyewa cikin sallolin farilla cikin yanayin da sura ba ta wajabta ciki kamar yanda yake cikin mara lafiya da wanda yake cikin halin gaggawa da sauri kamar yanda ya gabata.

Kadai ishkali yana gangara cikin tsallakawarsa ga nafila cikin rashin halascin uduli bayan shallake rabin sura ta fuskar kasantuwar jigo cikin dalilin hani shi ne Ijma'i, shi kuma yanda daga dalili Lubbi (dalili da bai kasance daga lafuzza ba) sai cikinsa a debe iya gwargwadon abinda ake da yakini kansa wanda shi ne hana uduli da janyea cikin sallolin farilla, ta yiwu daga cikin dalilan fatawar Akaramakallahu Almuhakkikul Hilli (K) cikin halascin uduli ciki nafilfili mudlakan  ko da kuwa ya kai ga rabin sura, ka lura da ishkali, ijma'in bai hado da nafilfil su zasu wanzu karkashin idlakai da suke shiryarwa  kan halascin uduli ko kuma yayin shakka, rashin dalili zai samu komawa ga riko da Asalar halasci, ka lura.

Lallai idan Mustanad ya kasance cikin hani daga uduli dogara da dalilai na lafazi daga riwayoyi cikin wannan babi kamar misalin Mursalatul Zikra ko kuma abinda ya zo cikin Fikhul Ridawi, lallai riwayar mudlaka ce ta hado da farilla da nafilfili, haka zalika cikin wanda ya zabi kansacewa idan ba a kai ga kaiwa ga karanta kashi biyu cikin uku ba kamar yanda ya zo cikin riwaya muwassakar Ubaidu kamar yanda bayani ya gabata lallai ta zo da idlaki da yake tattaro farilla da nafila, ka lura zahiri shi ne karkatar idlaki ya zuwa ga farilla kamar halasci uduli da rashinsa gabanin kaiwa ga kaso biyu cikin ukun sura ma'anarsa shi ne misaltawa cikin misaltawa, da kuma neman tabbatar da abinda ya rigaya ya tabbata kuma lallai babu dalili kan misaltawa ta biyu bayan sauke wajibi da misaltar farko, lallai  sauke umarni ko dai ya kasance cikin da'a ko kuma cikin sabo misaltawa ko dai cirewa da kuma rashin maudu'i, zabar rashin halasci gabanin kai ga kaso biyu cikin ukun sura bisa sassabawar maganganu da ra'ayoyi  ko kuma rashin halasci bayan kai wa daga babin misaltawa bayan an misalta a farko kan hakan ne hadisan babin zasu kasance suna duba ya zuwa sallar da ake karanta sura guda cikinta domin ya zama anyi hukunci da halasacin sauyata da wani misaltawar daban ko kuma rashin halasci, wannan yana gasgatuwa ne kadai cikin farilla bisa gini kan haramcin karanta kur'ani cikinta bisa riko da idlaki da zuhurin fadinsa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi

قوله عليه السلام إلّا تقرء في المكتوبة بأقل من سورة ولا أكثر[1].

Cikin sallolin farilla ka da karanta fiye da sura daya ko kasa da sura.

Bisa hani cikinsa zai kasance ko dai na hani na haramci ko dai na tsarkaka a wannan lokaci zai ya zama makaruhi ne karanta kur'ani a farilla.

amma salolin nafila bai tabbatu ba cikinsu ko da kuwa da mustahabbancin sura daya iyakantacciya da haddi, sabida abinda akai hani daga karanta kur'ani cikin sallar hani ne na haramci ko na tsarkaka bisa sassabawar maganganu biyu da ye kebantu da wanin nafila, abinda ya zama wazifa ta take daga gareta shi ne abinda ya zo da shi daga sura, bai kasance daga babin misaltawa da wujudul Awwal daga sura da har uduli daga barinta zai kasance daga babin sauya misaltawa bayan an rigaya an misalta abinda ya wajabta, bari dai baki dayan abinda ya zo da shi daga sura a kankin kansa misdaki ne daga masadik din misaltawa da wannan shaida ce wadancan mudlakan hadisai za su karkata zuwa ga hani kan uduli cikin sallolin farilla idan ya kai ga karanta rabin sura ko kaso biyu cikin ukunta baso hadowa da sallolin nafila, sai Asalar halasci ta tsayu yayin shakka cikinsu da kuma rashin dalilai kai, ka lura, lallai karkta yana gushewa da mafi kanrantar lura mudlakai sun wanzu dama itace mas'alarmu a wannan mukami.

Ra'ayinmu kamar yanda Akaramakallahu Almuhakkikul Hilli da mashur suka karkatu zuwa gareshi daga halascin udulu daga sura zuwa wata surar cikin sallolin nafila mudlakan ko da kuwa ya kai ga karanta rabin surar.

Duk da cewa ihtiyadi istihbabi domin mu kubuta daga sabawa wanda ya zabi hani ko kuma kasantuwar ihtiyadin fuska mai kyawu a kowanne hali a hankalci da shari'ance matukar dai bai wajabta tsanani da wahala da wasiwasi ba cikin kawo sura da aki udulu gareta da kasancewa da niyyar neman kusanci mudlakan.

Mas'ala ta 19: ya halasta cikin larura ayi uduli bayan kaiwa ga karanta rabin sura kai hatta cikin Fatiha da suratul Iklas kamar idan ya kasance ya manta ba'arin surar. Ko kuma ya ji tsoran fitar lokaci idna ya cigaba da karanta surar, ko kuma dai sakamakon wani dalili da ya hana cigaban.

Ina cewa magana zata kasance bisa cigaba kan bahasin da ya gabata  daga far'antawa kan asali, lallai bayan Akaramakallahu ya yayi fatawa kan halascin uduli matukar dai bai ka ga rabin sura bada kuma hani kan uduli idna ya kai ga rabinta ko ya haura rabi, kadai dai hakan ya kasance lokacin da mutum yake da zabi amma cikin halin larura lallai a bayyane yake cewa yana daga Alhukumul sanawi canjuwar hukunci yayi larura, lallai duk yayin da Allah ya haramta wani abu zaka samu ya halasta cikin halin larura da izinin Allah matsarkaki da hukumul sanawi, lallai cikin larura abubuwa da suke haramun suna halasta, idan bai iya samun damar kammala ba a bayan haura rabi cikin sura da ya fara karantawa ko dai sakamakon wani dalili na dabi'a kamar idan ya manta ba'arin sura, ko kuma sakamakon sababi na shari'a kamar idan ya ji tsoran fitar lokaci idna ya cigaba da karanta ta, to a wannan hali mudlakan ya halasta ko da kuwa cikin Ftaiha da suratul Iklas ne idna da su ya fara duk da cewa bai halasta yin uduli cikinsu ba mudlakan face cikin sallar juma'a ko Azuhur din ranar juma'a ya halasti yin uduli ya zuwa suratul juma' da munafikun kamar yanda bayani dalla-dalla kan hakan ya gabata, wannan shi ne abinda ya sarraha ya bayyana karara ciki da waninsu, abinda yake fara fadowa cikin kwakwalwa daga nassoshi shi ne hana kebantuwarsa da fuskar yiwuwar kammala sura, tareda hani na hankali da shari'a lallai umarni a misaltawa zasu fadi lallai kuma yana daga rasa maudu'I ko kuma kamar yanda ake cewa (salibatu bin tifa'il maudu'i) uduli sai ya wanzu mudlakan kan asalar halasci cikin wanin fuskar yiwuwar kammala sura.

Sannan abin nufi daga halasci shi ne gamammiyar ma'ana  wacce ke kishiyar haramci da ke haduwa da zama tareda wajibi da mustahabbi da makaruhi.

[1] الوسائل: باب 4 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

 

Tura tambaya