lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

gwagwarmayar Imam Hadi da Gullatu

 

Daga cikin karkatattun kungiyoyi batattu da suka kasance a zamanin Imam Hadi (a.s) akwai Gullatu mutane da suke imani da gurbatattun akidu marasa tushe kuma sun kasance suna danganta kansa da shi'a. wadannan mutane sun kasance suna guluwi cikin Imam suna jingina masa mukamin ubangijintaka, sannan wani lokaci suna ayyana kansu matsayin wakilansa da yada da kansa, da wannan ne suka jawowa shi'a bakin suna tsakanin kungiyoyin musulmi, Imam Hadi (a.s) kai tsaye ya barranta daga wannan kungiya ya kuma zare takobin yaki kansu yayi bakin kokarinsa wajen nesantar da su daga wurinsa da korarsu bai yadda ya basu dama sun shafawa shi'anci bakin fenti ba.

Ta yiwu ace: dalilin samuwar Akidarsu kan cewa Imam Allah ne da sauran gurbatattun akidunsu marasa tushe ya samo dalili daga:

1 karamomi: tsinkaya kan gaibu da sauran abubuwa da suka sabawa al'ada da suka gansu daga Imam (a.s) da kuma su wadannan mutane sun kasa fahimta da gane wadannan mas'aloli sai suka imani da su a karkace suka cudanya karerayi da bidi'o'insu ciki suka samar da wata harka da ta kishiyantar muslunci.

2 wadannan karkatattun mutane suna su take dukkanin dabaibayi da ka'idoji da dokokin muslunci da watsi da su suna son rayuwa kan son ransu da wannan dalili suka halasta dukkanin abubuwan da muslunci ya haramta.

3 suna da kwadayin kudi da dukiyar al'umma suna son su toshe hanyoyin samun kudaden A'imma ta hanya haifar da yaki, cikin dukkanin Gullatu mutane masu hatsarin gaske masu batar da mutane zaka samu shugabanninsu mutane kamar wadannan da sunayensu zai zo a kasa:

1 Aliyu Ib Hasak Alkummi 2 Kasim Yakdini 3 Hassan Ibn Muhammad Babayi Kummi 4 Muhammad Ibn  Nusairu Fihri 5 Faris Ibn Hatim.

Alal misali akidar Aliyu Ibn Hasak ta kasance kamar haka:

A- Imam Hadi ubangiji ne mahalicci mai gudanar da duniya!

B- Ibn Hasak wani Annabi ne kuma dan aiki daga Imam domin shiryar da mutane!

C- dukkanin farillan muslunci daga Zakka, Salla, Azumi Hajji ba wajibi bane!

Imam Hadi (a.s) cikin wasikar da ya bada amsa ga tambayoyin shi'a yayi bayani kamar haka: wadannan mutane Gullatu mutane karkatattu Kafirai yayi wasiyya ga shi'a da cewa su nisanci wadannan mutane, Imam cikin amsasa ga daya ga yan shi'a dangane da Ibn Hasaka da gurbatattun akidunsa yayi rubuta kamar haka: hakika la'anannen Allah Ibn Hasaka karya yake fadi, ni bana kirga shi daga cikin masoya da mabiyana, me ya same shi ne? Allah ya la'ance shi! Na rantse da Allah ubangijin Muhammad (s.a.w) da Annabawan da suka gabata Allah bai aiko su da komai ba face bauta masa shi kadai da umarni da sallah da zakka da hajji da wilaya, sannan hakika Muhammad (s.a.w) bai kira ga wani abu ba face zuwa bautawa Allah shi kadai, mu ma magadansa bayin Allah ne bama yin shirka gareshi, idan muni masa biyayya zamu samu rahamarsa, idan muka sabawa umarninsa zamu fada cikin fushinsa da azabarsa, mu bamu da wata hujja kan Allah, Allah yake da hujja a kanmu da dukkaninmu halittunsa, ni ina barranta daga dukkanin mutumin da yake fadin irin wadannan maganganu ina neman tsarin Allah daga wadannan mugunyar kalamai, kuma ku nesanta daga wadannan mutanen  ku matsa musu ku kuntata musu, idna kuka kama daya daga cikinsu ku jefe shi da duwatsu ku kashe shi.

Kafoffin sadarwa da wakilci tsakanin Imam da shi'arsa

Yanayin matsi da tsananin da Imamai suka rayu da shi a zamanin mulkin sarakunan Abbasiyawa ya tilastawa Imamai samar da wasu hanyoyi domin dorewar sadarwar tsakaninsu da shi'arsu, wannan hanyoyi basu hanyoyi bane face wakilci da ayyana wakilai da ma'aikatansu a dukkanin sassan garuruwan musulmi, manufar wannan aiki shine tattaro Zakka da kumusi da sauran hakkokin shari'a domin mika su ga Imamai, kari kan haka shine amsa tambayoyin fikhu da akida da bayani kan al'amuran siyasa daga wurin Wakilin Imam, wadannan wakilai sun taka muhimmiyar rawa mai tasirin gaske cikin isar da sakon Imamai.

Imam Hadi (a.s) tareda kasancewarsa karkashin matsawa da sa ido daga masarauta a garin Samarra ya cigaba kan tsarin nadi da ayyana wakilai da `yan kai sako a dukkanin garuruwa da yankuna ta hanyar wadanna mutane ya samu cigaba da isar da sakonsa da hadafinsa ga al'umma.

Rashin samuwar sadarwa kai tsaye tsakanin Imam (a.s) da `yan shi'arsa ya haifar karuwar taka rawar Wakilai da gudummawarsu a mazhabance da siyasance hakan ya sanya sun samu kwarewa matuka cikin daidaita tafiyar `yan shi'a, tarihi ya bada shaida cewa Wadannan wakilai kan asasin kusurwowi da nahiyoyin garuruwa mabanbanta sun kasu zuwa kashi hudu.

Nahiya ta farko: itace Bagdada, Mada'in, Iraki (Kufa).

Nahiya ta biyu: sun hado da Basara, Ahwaz.

Nahiya ta uku:  Qum, Hamadan.

Nahiya ta hudu: Hijaz,Yaman, Masar,.

Kowacce nahiya daga cikinsu an nada mata Wakili guda daya mai cin gashin kansa dukkanin masu yada ayyukan nahiya na karkashin kulawarsa kuma shi yake nada su, dukkanin ayyukan Imam Hadi (a.s) na gudana ne ta hannun wadannan Wakilai, zamu iya gani cikin abinda aka nakalto a shekara 232 a cikin wasikarsa zuwa ga Aliyu Ibn Bilal wanda yake wakiltarsa a inda yake wato Bagdad, ya rubuta cewa: na nada Aliyu Ibn Rashid mayin Aliyu Ibn Husaini Ibn Abdu Rabbihi[1] na mika wannan nauyi gareshi hakika yanada cancanta kan wannan mukami babu wani da yafi shi cancanta kan wannan mukami, nasan cewa kana cikin babban nahiya, kan hakane nake son cikin wannan wasika in sanar dakai wannan maudu'I, sabida wajibi ayi amsa biyayya a mika hakkokin shari'a zuwa gareshi sannan ku sanar da mabiyanmu cewa an umarcesu suyi masa biyayya domin ya samu damar sauke wazifar da take kansa.[2]

Imam Hadi (a.s) a wata wasika daban da ya rubuta zuwa ga daya daga cikin Wakilansa mai suna Ayuba Ibn Nuhu:

Malam Ayuba Ibn Nuhu! Ka kauracewa jayayya tareda Abu Ali dukkanin ku biyun an dora muku sauke wazifofi saboda haka ku mai da hankali cikin ganin kun sauke abinda yake wuyanku, ta hakane kadai zaku sauke nauyi da yake kanku ba tare da bukatar shawarata ba.

Malam Ayuba Ibn Nuhu! Kan asasin wannan umarnin kada ka karbi komai daga hannun mutane Bagdada da Mada'in kada ka baiwa kowa izini zuwa wajena, idan wani ya kawo maka hakkokin shari'a daga wajen garin da aka nadaka ka umarce shi ya mayar dasu wurin wakilin da aka nada a garinsa.

Malam Abu Aliyu! kaima Ina baka umarni ina maka wasicci ka zartar da umarni da na yi kan Ayuba Ibn Nuhu.[3]

Haka Imam cikin wasikar da ya baiwa Abu Aliyu Ibn Rashida ya aika ta zuwa ga mabiyansa na garuruwan Bagdada, Mada'in Iraki, cikinta ya rubuta cewa: ni na zabi Abu Aliyu Ibn Rashid mayin Husaini Ibn Abdu Rabbihi da wakilansa, lallai shi a wajena matsayinsa daya da Husaini Ibn Abdu Rabbi, na mika dukkanin ayyukan wakilan da suka gabace shi zuwa hannunsa nay i masa izini kan karbar hakkokin shari'a, hakika shi mutum ne da ya cancanta , na zabeka domin gudanar da lamurra, kai kuma Allah yayi maka rahama idan zaka bada hakkoki ka je wajensa , kada ka sake alakarka da shi ta samu matsala, ka karkade duk wani wasiwasi daga kwakwaklwarka da zai haifar da sabani tsakaninka da shi, kuyi gaggauwa cikin biyayyar Allah cikin tsarkake dukiyoyinku, ku kauracewa zubar da jinin junanku, ku karfafi juna kan kyawawan ayyuka da tak'wa, ku kasance masu tsantseni domin Allah ya sanyaku cikin jinkansa da rahamarsa.[4]

Aliyu Ibn Jafar  ya kasance daya daga cikin Wakilan Imam Hadi (a.s) shi mutumin garin (Haminiya) daya daga cikin kauyukan da suke gefan garin Bagdada wata rana yan leken asirin Sarki Mutawakkil sun kai tsegumin ayyukansa, sai Mutawakkil ya sanya aka kama shi aka jefa shi cikin Kurkuku, bayan gama dogon zama da yayi a Kurkuku sai aka sake shi, karkashin umarni Imam Hadi (a.s) sai ya koma garin Makka ya zauna a can.[5]

Cikin adadin jerin Wakilan Imam Hadi (a.s) ya kamata ace mun ambaci sunan Ibrahim Ibn Muhammad Hamdani, hakika Imam (a.s) cikin wasikarsa zuwa gareshi ya rubuta: hakkokin shari'a da ka aiki sun iso gareni Allah ya karbi aikinka Allah ya yarda da shi'armu ya sanya su kusa damu a duniya da lahira

A bayyana yake cewa wannan wasika tana nuni da ishara kan cewa Imam Hadi (a.s) da kansa ne ya nasabta Ibarahim ya dora masa nauyin kula lamurran kudi sannan akwai tsammanin ya zama ya dora masa wasu wazifofin

[1] Allah ya karbi ran Aliyu Ibn Husaini Ibn Abu Rabbihi a shekara ta 229 a garin makka, bayan mutuwarsa sai Imam ya nada  wani a gurbinsa

[2] Iktiyaru ma'arifatil Rijal sh 510

[3] Iktiyaru ma'arifati Rijal sh 514 hadisi na 992

[4] Iktiyaru ma'arofati Rijal sh 531-514

[5] Iktiyaru ma'arifati Rijal sh 607, ISbatul wasiyya mas'udi


Tura tambaya