lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

ADALCIN ALLAH MATSARKAKIN SARKI

Da sunan Allah mai Rahama mai jin ka

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah buwaya gagara misal

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halittar wanda aka kira shi da Ahmad a sama a kasa kuma a ka kiraye shi da Muhammad da iyalansa tsarkaka jagorori

Bayan haka hakika Adalci yana daga cikin Asalai filoli ginshikai da muslunci ya doru kansu kuma yana daga nag aba-gaba siffofin Allah na zati da bai taba rabuwa da su kamar yanda yake asali na biyu cikin Asalai guda biyar Tauhid, Adalci, Annabta Imamanci, Ma’ad

 

Asali na biyu daga asalan addini: shi ne adalcin Allah, shi yana daga siffofinsa madaukaki na tabbatuwa fi'iliya (na aiki) kamaliya, lallai shi adali ne ba azzalumi ba, bai yin zalunci cikin hukuncinsa, bai kaucewa gaskiya cikin shari'arsa, yana sakawa masu da'a, haka yana ukuba ga masu saba masa, bai dorawa bayinsa abin da basu da iko kansa, baya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta, shi tsarkakakke ne daga zalunci da aikata duk abin da yake mai munine.

Kadai dai an sanya adalci matsayin daya daga cikin asalai sakamakon abin da yake ginuwa kansa daga ka'idojin muslunci, bari dai baki dayan hukunce-hukuncen addini, idan babu shi babu wani abu da zai cika ya tabbatu daga addinai, bazai yiwu a iya gane gaskiyar Annabi ba da tsiransa alal idlak kwata-kwata.

Sannan shi adalci a luggance: yana da ma'anar ajiye abu a muhallinsa, ko kuma haddi matsakaici tsakanin takaitawa da wuce gona da iri, ma'ana shi ne hikima.

Sannan adalci a cikin isdilahi: yana da ma'anar lallai Allah Adali ne baya zaluntar kowa, bai wofinta daga wajibi, dukkanin abin da yake gangarowa daga gare shi hikima ce ta ubangijantaka adalci ne na Allantaka, sannan adalcin zamantakewa daya daga cikin mabayyyana ce daga mabayyanan adalcin Allah.

 

Natijar maganar masu imani da kasantuwar Allah Adali:

Lallai aiki bai gangarowa daga gare shi madaukaki face kan illolin manufa da hadafi, ana kiransu da agraz (hadafofi) su ne amfanunnuka da suke komawa ga halitta. Allah bai aika abin da cikinsa babu amfani ga halitta ba, ko kuma abin da cikinsa akwai cutuwa kansu, da abin da zai janyo musu azaba ranar kiyama ko kuma cikin duniya, idan ma sun kasance daga aikinsa madaukaki sai dai cewa sun biyo sakamakon zabinsu ne, bisa alkawarin narkon azabarsa, hakan ba zalunci bane daga gare shi madaukaki, bari dai mutane ke zaluntar kawukansu.

Hakika ayyukan mutum suna gangarowa ne cikin zabinsa, babu tilashi babu fawwalawa, bari dai al'amari ne tsakankanin lamurra guda biyu, shi ne cewa ayyukan suna siffantuwa da husnu da kubuhu (kyakkyawa da mummuna) a zatinsu a hankalce.

Daga cikin ayyukan mutum akwai wadanda suke da kyawu a hankalce.

Akwai kuma wadanda suke da muni a hankalce.

Allah matsarkaki ya tsarkaka daga munana duk da kasantuwarsa mai cikakken iko da dama kansu, baya aikata mummuna ba ya kuma son sa, domin cewa aikata munana da son su bai kasantuwa face daga gajiyayye gafalalle, Allah shi ne mai iko masani, gyangyadi da bacci basu daukarsa, yana yin aiki cikin hikima da hadafi, shi ne bijiro da bayi zuwa ga samun lada saboda haka yake kallafa musu, yake son da'a yake kin sabo daga bayi baki dayansu da irada da karaha na shari'a babu banbanci ta afku ne da iradar bayinsa ko kuma ba ta afku da ita ba, shi iradarsa: ita ce umarninsa madaukaki, ko kuma ta yiwu abin da aka umarta da ayi ya saba daga umarni wannan zai iya yiwuwa, iradarsa ga aikin bawa da'a ce aiki ya kasantu ko sabo to fa bata kasantuwa face da sabubba da dalilai daga cikinsu shi ne nufin shi bawan, lallai bawa yana da zabi cikin iradarsa da ayyukansa shi ba tilashi ba a hana shi ba, sai Allah ya shiryar da shi hanyoyi biyu ko dai ya kasance mai godiya ko kuma mai butulci da kafircewa, mutum bai ga komai face abin da ya yi sa'ayi gare shi.

Allah matsarkaki mai ludufi ne gabayinsa, ya haliccesu domin ya kallafa musu da'arsa da bautarsa, ya kallafata kansu domin sanya su kan hanyar samun lada da farin ciki da rabauta na har abada, ya sanya su kan wannan hanya domin tabbatuwar ladan ta hanyar cancantuwa, lallai shi madaukaki ya kawar da illolin mukallafai cikin abin da suke bukatuwa zuwa gare shi da kudura da tsanuka da aiko manzanni da saukar da litattafai, ya kuma umarce su zuwa ga abin da yinsa gyara ne gare su, kamar yadda ya hane su daga abin da aikata shi zai cutar da su, duk wanda ya saba hakika sabawar ta zo daga fuskaninsa ne ba daga tsarki ya tabbatar masa ba madaukaki.

Ludufi na da ma'anar abin da ake samun hadafin Allah madaukaki dashi wajibi kansa a hankalce, sabo ba tauye hadafi ta hanyar barin abin da yake da hannu cikin samunsa abu ne mai muni kuma ya tsarkaku daga aikata abu mai muni, shi ne tsantsar kamala kamala tsantsa.

Ludufi yana da ma'anar abin da ke kusanta bawa zuwa ga da'ar ubnagijinsa da kuma shi bawa yake nesantar aikata sabo ba da yanayin tilasawa ba da fin karfi, bari dai mukallafi na kasancewa koda babu shi zai iya da'a zai kuma iya barin sabo, lallai hakan wajibi kan Allah sai dai cewa bisa abin da yake hukunta samuwarsa da tausayinsa.

Mafi alherin dalili kan adalcin ubangiji bari dai dalili kan baki dayan asalan addini: shi ne lafiyayyar fidira (tsarin halitta) lallai hanalin fidira mai lafiya yana riskar lallai cewa azzalumi da maha'inci ya cancanci a tuhuma da yi masa ukuba, sannan kuma lallai adali ya cancanci a bashi lada, Allah yana sakawa mai kyautatawa kan kyautatawarsa, hakama yana sakawa mai miyagun ayyuka kan miyagun ayyukansa, kamar yadda tsarki ya tabbatar masa madaukaki yake karfafa kan adalcinsa cikin littafinsa mai girma:     

(وَمَا ظَـلَمْنَاهُمْ وَلَكِنْ كَانُوا هُمُ الظَّالِمِينَ ).

Bamu zalunce su ba sai dai cewa su ne suka kasance  Azzalumai.[1]

ubangiji yana zargin Azzalumai ta kaka kuma tsarki ya tabbatar masa madaukaki shi kuma zai kasance Azzalumi:

(يُدْخِلُ مَنْ يَشَاءُ فِي رَحْمَـتِهِ وَالظَّالِمِينَ أعَدَّ لَهُمْ عَذَابآ ألِيمآ)  .

Yana shigar da wanda ya so cikin rahamarsa ya yiwa Azzalumai tanadin azaba mai radadi gare su.[2]

(وَقِيلَ بُعْدآ لِلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ ) .

A kace nesa-nesa ga mutane Azzalumai[3]

Ta kaka zai umarce mu da yin adalci cikin jama'a alhalin shi kuma bai siffantu da shi:

 (إنَّ اللهَ يَأمُرُ بِالعَدْلِ ).

Lallai Allah yana umarni da adalci.[4]

Shi tsarkakakke ne daga dukkanin abin kunya da tawaya, hakika an tambayi shugabanmu Sarkin Muminai dangane da tauhidi da adalci kamar yadda ya zo cikin littafin Nahjul Balaga-sai ya ce:

«التوحيد أن لا تتوهّمه ، والعدل أن لا تتّهمه ».

Tauhidi shi ne kada kai wahamin ubangiji, adalci shi ne kada ka tuhume shi.

Me yafi kyawu daga abin da Sarkin Muminai (as) ya fada hakika ya takaita zance ya kuma sanya balaga cikin saukewa.

Muna imani da cewa lallai ayyukansa baki dayansu na kan hikima suna dacewa da adalci, daga cikin adalcinsa da kyautatawarsa ga halittunsa shi ne ya wajabtawa kansa aiko musu da Manzo, domin ya koyar da su ya kuma shiryar da su zuwa ga abin da yake so daga gare su, domin su samu farin ciki duniya da lahira

(لِئَلاَّ يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى اللهِ حُجَّةٌ بَعْدَ الرُّسُلِ ).

Domin kada wata hujja ta kasance ga mutane bayan aiko da manzanni.[5]

Daga karshe cikin asalin adalci akwai bahasosi masu tarin yawa masi kima da amfanarwa, kamar misalin mas'alar husnu wal'kubuhu (kyakkyawa da mummuna) na zati da hankali da mas'alar jabaru da tafwizu da kada'u da kadaru da mas'alar shiriya da bata da radadi, da arzuka da mafi maslaha da hakika da ludufi da makamantansu, dukkaninsu an ambace cikin masadir da sukai bayaninsu mai fadi filla-filla daga litattafan ilimin kalam da mujalladan falsafar muslunci.

Hakika bangarorin da sukai imani da adalcin ubangiji sun baiwa hankali matukar kima, lallai shi manzo nena boye kamar yadda ya zo cikin hadisai, kamar yadda ayyuka na da kimata zati ba tare da kyawuntawa ba da munanawar shari'a, hakan ba daga shari'a bane kadai, bari dai hankali yana asali cikin tsamo hukunci daga kyawu da muni da makamancin haka, kamar yadda adalcin Allah yake da muhimmanci matuka cikin kasantar da jama'ar musulmada daidaita halkokinsu da janibobinsu babu danniya babu zalunci babu wuce gona da iri babu ta'addanci babu babakere babu barna babu zaman kashe wando da son baza babu barai dai da makamantansu daga barnoni da fasadin jama'a da daidaiku.

Allahgirmansa ya girmama adali mai hikima, bai wofinta daga wani wajibi bai aikata mummuna, baya zaluntar bayinsa, da bai kasance haka ba da ya kasance tauyayye, Allah ya daukaka daga kasantuwa haka, da zai aikata mummuna da karya da halasta kansa, sai amintuwa da alkawarinsa na ni'ima da alkawarin narkonsa ya bushe ya kauce, sai dukkanin hukunce-hukuncen shari'a su dauke su dage, hadafin da kae son cimma daga aiko annabawa da manzanni ya samu matsala, komai ya zama ya tafi iska babu wani amfani cikinsa.

Saboda haka ne ya sanya adalci asali na biyu daga asalai da asasan addini bayan tauhidi, wasu sunce adalci yana daga asalan mazhaba, bisa kasantuwa dukkanin kungiyoyin da suke da'awar muslunci suna tarayya cikin asalai guda uku wanda sune:tauhidi annabta da ma'ad.

Amma adalci da imamanci to wadannan biyun suna daga asalan mazhaba, akwai magana kansu da sanya lura, ana kiran dukkanin wanda yayi imani da adalcin Allah daga mu'utazilawa da imamiya da sunan Adaliyya (masu imani da adalcin Allah) amma asha'ira su suna da'awar yancin Allah d kore kyakkyawa da mumuna na zati da hankali, wanda wannan ra'ayi nasu fagarniya ce tsantsa da wahami domin ai babu wani cin kao da juna tsakanin yancin Allah da adalcinsa a hankalce da jiye, lallai Allah tsarki ya tabbatar masa madaukaki adali ne da bayani karara da ga hujjoji hankali da dalilan nakali daga littafin Allah da sunna da fidira lafiyayya data wofinta daga shubuhohi tsarkakka daga sabo da zunubai, lallai shi ubangiji shi ne wanda ya wajabtawa kansa rahama da adalci tare da tsantsar yanci, lallai shi ne yake tambaya amma babu mai tambayarsa, saboda haka babu cin karo da juna tsakankanin adalcin Allah a yancinsa.

Wurin Allah muke neman taimako

 



[1] Zukruf:1

[2] Addahru31

[3]Hudu:44

[4] Annahlu:90

[5] Nisa'i:165

Tura tambaya