lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Labarin dan karamin Yaro da bishiyar tuffa

                                                        An hakaito labari cewa wata rana wata katuwar bishiyar tuffa ta kasance wacce reshenta babu komai jikinsa ta kuma cika da kayan marmari tana kuma da karfin jijiyoyi a gefen wannam bishiya akwai wani karamin Yaro da yake wasa kusa d aita ya kan hawa kan reshenta ya sulu ya sauko kasa, sannan yana cin kayan marmarinta, idan kuma ya gaji da yin wasa sai ya kwanta karkashinta yana mai shan inuwarta, ya kasance yana yin haka kulli yaumin a kowacce rana, yau da gobe yau da gobe har wannan Yaro ya girma ya shagaltu da wani abu ya dena zuwa wurin wannan bishiya, sai dai cewa wata kwatsam sai ga shi ya dawo wurinta cikin bakin ciki, sai wannan bishiya ta nemi suyi wasa tare, sai wannan yace: ni fa yanzu ba karamin Yaro bane yanzu ni ina cikin bukatar `yan kudade ne domin in sayi ba'arin wasu abubuwa da nake bukata, sai bishiyar ta ce masa: ni bani da kudi amma ka debi kayan marmarin da nake da su kaje ka sayar kayi amfani da ribar wajen biyan bukatar ka, sai ya tattara kayan marmarin yana cikin murna da farin ciki ya tfai bai dawo ba, wannan bishiya ta kwana cikin bakin ciki da damuwa.

Bayan shudewar wasu `yan shekaru sai a kara dawowa kamar yanda ya dawo a wanca karon ta ce masa zo muyi wasa tare, sai ya ce mata ni fa yanzu na zama babban mutum ian da mata da `ya`ya da nake daukar nauyin kula da su, ina bukatar gina musu mahallin zama, shin zan samu taimako daga gareki ? sai tace masa ni banda muhallin da zan baku amma zaka iya dibar kayan marmarina daga jikin reshena yadda ranka ya so ka je ka gina gidan da zaku zaun, sai ya aikata hakan cikin farin ciki ya tafi yana halin murna.

Shekaru na shudea da lulukawa wannan bishiya na halin kadaici da baklin ciki kan rashin abokin wasanta wannan karamin Yaro da yana zuwa wajenta wanda yanzu ya wayi gari ya zama babban mutum ya kaurace mata, kwatsam sai gashi ya zo lokacin kakar zafi bazara ana tsananin zafi, sai wannan bishiya ta yi murna da farin ciki da ganinsa, ta ce masa zo mu yi wasa, sai yace: ni fa na zama babba na ma zama tsoho ina son in `dan huta ne daga gajiya da nake dauke da ita daga duniya, ina son in nesanta daga idanun mutane sai dai cewa banda abun hawa da zan yi kwalekwale da shi in shallake tafki, sai tace masa ka ciri itace na da reshena  ka kera kwakwale da su , sai ya cira ya tafi bai kara dawowa ba sai bayan wasu shekaru kamar yanda ya saba bayi harma ita bishiyar ta saba da wannan hali nasa baya zuwa sai wata bukata ta kama shi yayinda ya zo wannan karo sai ta rgaye shi fara magana tace masa kash wayyo nima na girma matuka bana da wani abu da zan iya baka, ta cigaba da ce masa babu tuffar da zaka ci ko kuma ka diba ka sayar , sai yace mata babu bukata saboda ni yanzu banda hakoran da zan tattauna tuffar in ci, sai tace masa bani da reshe da zaka hau kayi wasa kansa, sai yace bani da bukatarsa na rigaya na tsufa tukuf bam azan iya yin wasan ba, sai wannan bishiya tayi bakin ciki matuka kan rashin abinda zata bashi ta wayi ta zama kamar matacciya hatta reshenta ya tsufa, sai ya bata iya abinda nake bukata shine in huta a wannan lokaci, ina bukatar hutawa kadai, sai tace masa wannan reshena da jijiyata sune kadia abinda ya rage mini zaka iya zama karkashinsa ka huta a inuwata kayi kwanciyarka yanda kaso.  

 Hikima da aka fa'idantu da ita a wannan kissa shine cewa: wajibi mu girmama ni'ima da mu ka azurtu da ita a rayuwance, kamar misalin ni'imar mahaifa, ni'imar lafiya, ni'imar kyawun rayuwa da kyautukant, sannan wajibi koda yaushe mu kiyaye wannan ni'imomi, marubucin wannan kissa ya suranta bishiya a matsayin mahaifiya wacce take wanzuwa tana ta rainon `danta har ya girma ta karar da baki dayan rayuwarta cikin samar masa da dukkanin abinda yake bukata kuma ta bashi dukkanin abinda yake bukata duk sanda ya waiwayeta, har sai ta karar da dukkanin karfinta ta wayi gari bata iya bada komai, shi kuma wannan Yaro ya girma ya zama cikakken mutum ya tsallaka zuwa dattijo har ya kai ga tsufa amma ya gaza fahimtar kima da muhimmancin mahaifansa sai sanda ya gay a rasa komai, yanabukatar hutu sai ya kara dawowa zuwa garesu saboda yana da yakina kan cewa mahaifa sune tushen duk wani hutu.   

Tura tambaya