lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kowacce rana ashura ce kowacce kasa ma karbala ce

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Allah matsarkaki madaukaki ya ce:

﴿أَلَمْ تَرَى كَيْفَ ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلاً كَلِمَةً طَيِّبَةً كَشَجَرَةٍ طَيِّبَةٍ أَصْلُهَا ثَابِتٌ وَفَرْعُهَا فِي السَّمَاءِ *تُؤْتِي أُكُلَهَا كُلَّ حِينٍ بِإِذْنِ رَبِّهَا: ﴾

Ashe baka ga yandaAllah ya buga misali da kalma tsarkakka kamar misalin tsarkakka bishiya ce wadda asalinta ke tabbatacce reshenta kuma yana sama tana bada abincinta da izinin ubangijinta[1]

Bayan haka ka sanin ya `dan`uwa cewa ita bismillah da hakikarta da zurfafarta  ita ce mafarin samuwa cikin dukkanin wani abu da yake koma bayan Allah madaukaki matsarkaki daga dukkanin halittu da kasantattu samammu daga dabi`a da suke rayuwa ta zahiri da ta badini daga abubuwa da basu da jikkuna  da duniyar malakutiyya  ta gaibu, lalle Alla matsarkaki  shi ya halitta ya kagar da dukkanin wani abu  don rahamarsa da jin kansa sai ya sanya soyayya da alakoki cikin zatin ababen halittarsa  haka cikin ya sanya cikin tsarin halittarsu saboda rahamarsa da jin kai da girmamarsa da kwarjininsa lalle shine mai yawan kyauta da karamci ga wanda yayi Imani da shi da man wanda ya kafirce masa, yana azurta mumini sai dai cewa rahamarsa da jin kansa wadanda suka kasance bayansa akwai soyayya da debe haso da kyawunsa da kamalarsa  mai girma da daukaka sun ratayu ga wanda ke sanya wannan soyayya da wadancan alakoki da karkatarsa ta zuciya cikin hidimar ubangijinsa shumagabansa  majibancin lamarinsa, duk wanda ya yanke zuciyarsa da alakoki da abinda suka ratayu da ya mika ta ya sallamata ga hidimar Allah matsarkaki lalle babu makawa zai isa ga ya kai ga soyayya da rahamar da jin kan ubangijinsa.

Farkon abin halitta: sannan farkon abinda Allah ya halitta shi ne hankali daga haske sai Allah ya ce masa juya sai ya juya ya ce masa fuskanto ya fuskanto sai ya so shi ya ce: na ranste da girman da daukaka ban taba halittar wata halitta da ta fifice ka ba da kai na ke ba da lada da kai nake ukuba da azaba, kamar yadda Allah ya halicci jahilci daga duhu, yayinda ya halicci jahilci sai ya ce masa juya baya sai ya juya  ya ce masa fuskanto sai yaki fuskantowa sai Allah ya fusata kansa, lalle shi hankali masoyin Allah ne duk wanda hankali ya kasance cikinsa  lalle Allah mai girma da daukaka zai so shi kamar misalin masu takawa da masu kyawuntawa. Shi ko jahilci ya kasance abun ki a wurin Allah matsarkaki  shi jahilci na da ma`anar juya baya wanda yake kishiya ga juyowa gaba da fuskantowa, lalle shi sabo ne ga Allah ya kuma cancanci azaba da fushin Allah, wannan jahilci shi ke yakar hankali kamar yadda shi ma hankali na yakarsa, kowanne cikinsu yanada runduna da sojoji kamar yadda ya zo cikin hadisai

Idan jahilci ya zamanto cikinsa tareda shi akwai juyowa gaba da fuskantowa, to wannan jahilci yana daga cikin kason jahilcin da yake kishinyantar ilimi da rashin sani, lalle jahili wanda ke neman sani yana daga cikin halittun da Allah yake so lalle jahilcinsa baya cikin kason jahilcin da ake kidaya shi daga juya baya  wanda babu alheri cikinsa.

Shi hankali na ilimi shine wanda ka bautawa Allah da shi  aka samu aljanna da shi, shi mai hankali shi ne wanda yayi Imani da farko da kuma ranar komawa da abinda ke tsakaninsu daga annabta da imamanci da addini mai karkata ga gaskiya  sai ya zamanto mumini wanda yayi aiki nagari domin Allah matsarkaki.

Halittar adamu da juya bayansa ga alakoki da suke koma bayan ubangijinsa da kuma fuskntuwa zuwa ga ubangijinsa:

Lokacin da Allah ya halici adamu (as) sai mala`iku suka ce misalin wannan halitta za ta yi barna aban kasa, sai Allah yace musu ni nasan abinda baku sani ba* sai Allah ya sanar da adamu sunaye baki dayansu. Sai mala`iku sukayi tasbihi sakamakon basu da dangantuwa ga ubangijinsu irin yadda annabi yake da dangantuwa gareshi, saboda tsananin tsarkakarsu suke tasbihi ga Allah matsarkaki sai dai cewa kamalar tasbihi na kasancewa ga wanda yake da alakoki madawwama  da duniya amma sai yayi watsi da su domin Allah matsarkaki ya tsarkake ubangijinsa  daga ilimin da yakini da yake da shi da tsarki bayan ya na da zabi cikin faloli da kishiyarsu daga munana daga sharri da alheri da gaskiya da karya  da wannan ne dana dam ke fifita kan mala`iku.

mala`iku(as) sunga dangantakar adamu(as) da kasantuwarsa yana son alakokinsa da abinda ya alakantu da shi zai jawo alheri zuwa gareshi  domin cike gibin da yake tare da shi, sannan zai afka cikin gwagwarmaya da babu makawa daga gareta da barna ban kasa  da zubar da jini don biyan bukatar kai da sha`awarsa, sai dai cewa Allah ya san wani abu daga adamu cewa shi adamu  saboda soyayar da yakewa Allah da kusancinsa gareshi da sannu zai yi watsi da wadancan abubuwa na barna da mala`iku suka ambata a sama sannan kuma da sannu zai rabauta da samun yardar Allah da saduwa da shi.

Allah mai girma da daukaka ya cewa hankalin dan adam: juya ma`ana kayi watsi da alakokinka da karkatarka  da baubuwan da kake so sai ya juya, sannan ya kara ce masa juyo gaba ka fusknatar da fuskarka ga wanda ya halicceka ya halicci sammai da kassai sai hankali ya juyo gaba, kamar yadda Ibrahim masoyin Allah ya aikata, lalle alakar Ibrahim da soyayyarsa ga dansa isma`il wani abune da yake a tsarin halittarsa, sai dai cewa duk da hakan Allah ya nufi ibrahim ya juya baya daga wannan soyayya da alaka da yke da ita ga dansa domin shi ya kuma umarce shi da yanka dansa nasa, sannan daga baya yace masa ya juyo gaba ya fuskanto sai ya juyo gaba ya fuskanto, yace masa ya sallama Ibrahim take ya sallama ya ce: ina sallama fuskata ga Allah, wannan duk ya faru lokacin Ibrahim yana dattijo kamar yadda ibrahim a samartakarsa ya juya baya ta hanyar kakkarya gumaka ya kuma ya juyo gaba da fuskatowa ga Allah ta hanyar majaujawa da aka wurga shi cikin wutar sarki namarudu  da ita, amintacce Allah jibrilu(as) ya zo gurin Ibrahim(as)  lokacin da Ibrahim yake lilo tsakanin sama da kasa bayan makiya sun cilla shi zuwa ga wuta kafin ya fada sai jibrilu ya tambaye shi shin kana bukatar tallafi? sai Ibrahim ya ce masa indai daga gareka bana bukata, amma idan daga ubangiji ne to saninsa da halin da nake ciki ya wadatar dani daga rokonsa.

Sai wannan wuta da aka wurga ibrahim cikinta ta juya ta zamanto aminci da sanyi, wanda zai Imani yayi Imani bayan sun tsinkayi cewa gumakan da suke bautawa sun gaza daukan fansa kan Ibrahim sun kuma ga yadda ubangijin Ibrahim ya tseratar da shi daga konewa cikin wutar da namurudu ya kuma bashi nasara da sanyi da aminci.

Allah ya umarci hankali da ya juya baya daga zunubai da munanan dabi`u  sannan yak aa sa shi juya baya daga karkace karkacen zuciya domin ya juya ya fuskanci soyayyar Allah da kusantarsa daga gareshi.

Mafi cikar abinda ke gasgata juya baya da juyo gaba shi ne abinda ya gudana a ranar Ashura a filin karbala ta yanda shugaban shahidai imam husaini(as)  yaya juya gaba ya fuskanci uabngijinsa, hankali baki dayansa ya juya gaba ya fusankanto da juya gaban husaini(as) da fuskantowarsa(as)ga Allah matsarkaki madaukaki. Kamar yadda yake fadi cikin wake:

Na yi watsi da dukkanin halittu baki dayansu domin soyayyarka* na maraitar da iyalina domin neman ganainka* da zasu yankani gunduwa gunduwa domin soyayyata gareka to da har abada zuciyata ba zata karkata zuwa ga waninka ba.

Hankali da wahayi:

Sannan Allah yanada hujjoji biyu kan halittunsa: sune hankali da wahayi shi wahayi shine hujjar Allah ta zahiri, kamar yadda shi kuma hankali ya kasance hujjarsa ta badini ta boye, sannan kamar yadda ya ajbata a girmama da tsarkake hujjar zahiri daga annabi da wasiyyinsa imami to haka ya zama wajibi a girmama hankali  sai dai cewa shi dan adam ya kasance mai yawan zalunci da jahilci baya girmama hankali sai ya zamanto yana biyewa sha`awe sha`awensa da son zuciya sai hankalinsa ya wayi gari a matsayin abinda kai galaba akansa aka fi karfinsa sakamakon biyewa son rai, sai hankali ya wanzu cikin juyan baya bai fuskanta ga ubangijinsa, lalle shi ya ji kra amma sai ya juya baya sannnan bai ji kira ba ya juya gaba ya fuskanto, sai ya zamanto ya wakana cikin jahilci da zaluntar kansa da hasara duniya da lahira wadancananka shi ne ainahin hasara mabayyaniya, kamar misalin hasarar umar ibn sa`ad ibn abi wakas ga shugaban shahidai(as) ma`ana juya bayansa ga Allah girmansa ya girmama  da kuma fusnkantowarsa ga mulkin kasar rayyu sai dai cewa bayan ya juyawa Allah baya bai samu nasara ba kan mulki da ya fuskantowa na kasar rayyu a wannan lokaci yake cewa kansa: hasarar duniya da lahira.

Juya bayan farko ga hankali ya kasance daga biyayya domin shi hankali hankali ya juya saboda umarnin Allah domin fuskantar duniya sai dai cewa ya dawo ya nufi ubangijinsa da juyawar da fuskantowa duka sun kasance daga biyayyar ubangiji, ai ai cewa ita juya bayan jahilci ya kasance daga sabon Allah domin fuskantowa bata biyo bayansa bay a na wanzuwa cikin jahilci wanda aka halitta daga duhu wanda karshensa shi ne wuta kamar misalin kafiri a munafuki da fasiki wanda bai tuba ba daga zunubun da yake aikatawa.

mulkin sulaimanu  da mulkin shugaban shahidai imam husaini(as):

Sannan annabi sulaimanu ya nemi ubangijinsa da ya bashi wani mulki da wani bai same shi gabaninsa kuma wani bai iya samunsa bayansa, sai Allah ya bashi abinda ya nema sai dai cewa shi yana saka gidan zuma da hannunsa wanda da shi yake ciyar da kansa ya samu karfafar kan biyayyar Allah, kololuwa burinsa cikin samun mulki shine tsayar da adalci cikin talakawansa bawai ya azurta kai da mulkin ba.

Haka al`amarin yake ga shugaban shahidai imam husaini(as) ya nemi mulki don daukar musibu da juriya kan musibu wanda bai kasance ga wani ba gabaninsa da bayansa, sai shugaban shahidai ya dauki dukkanin bala`i  yayi watsi ya kyale dukkanin mutane ya maraitar da iyalinsa domin soyayyarsa ga mahaliccinsa da kuma shaukin son ganinsa, ma`ana ya yanke dukkanin alakokinsa  ya juya masu baya  domin fuskantar ubangijinsa har ya zamnto abin kwaikwayo da koyi ga `yan baya cikin dukkani duniyoyi, sannan sammai da kassai da dukkanin abinda ke cikinsu daga abinda ake iya gani dama wand aba a gani sun yi masa kuka.

 baban Abdullah imam husaini (as) yayi shahada wanda ya kasance masu neman daukar fansa jininsa na yi msa kuka dare da rana suna msa kukan jini maimakon hawaye, har ya kasance hankalin dan adam na dandanar adalci da da hankaltar imam husaini ranar Ashura, lalle tsrakakakkiyar kalma wadda tusheta da asalinta ya kasance daga tabbatacce reshenta ya bazu a samaniya  tana ba da kayan marmarinata a cikin kowanne lokaci da izinin ubangijinta, munafukai basu yaki imam husaini(as) face abinda suke fadi da bakunansu(mu muna tsananin kiyayya da babanka) lalle sarkin muminai ali(as) ba komai bane face tsagwaron hankali da tajallinsa da adalci cikin dukkanin halittu lalle zamani bai haifi wani mutum kwatankwacinsa ba, me yasa munafukai ba sa sonsa?

Mutum da arziki:

Babu shakka ko kokwanto cikin kasantuwar mutum mafificiyar halitta, lalle manufar halittarsa  shine ya kasance halifan ubangiji a ban kasa cikin sunayensa da siffofinsa domin ya azurtu duniya da lahira.

Sannan abin nufi daga arziki shine Allah matsarkaki  ya karbe shi haka waliyyai da mukarrabai su karbe shi domin ya kasance tareda su a cikin aljanna da koramu cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai iko, takaitacce baiti cikin wannan kasida ta irfani(sanin Allah) shi ne ya zama dole da farko musan waye mutum menene shi shin kamar yadda masana mandik ke fadi cewa shine (dabba mai Magana) hakanne kadai babu wani Karin bayani, ko kuma dai kamar yadda arifai ke fadi cewa shine (rayayye mai bautar Allah)  wanda sunayen Allah da siffofinsa ke tajalli cikinsa.

Na biyu y zama dole muyi bayani duniya mecece ita, menene halittu da muke cewa kasantattu, menene manufar halittar duniya da kagarta? Anan mahanga kan duniya ta sassaba  tsakanin masu Imani da samuwar Allah da wanda ke kore samuwarsa kamar yadda bayanin hakan yake dalla dalla a muhallinsa.

Na uku: menene bigire da muhallin dan adam a wannan duniya mai fadin gaske da ta shallake fahimta dana dam.

A wannan lokaci zaka san ma`anar azurtar dan adam da kuma kasantuwar lalle Allah matsarkaki ya halicci halittu domin dan adam ya hore masa abinda ke cikin sammai da kassai, ya sanya karkata da soyayya cikin tsarin halittarsa da zuciyarsa fuskanin alakokinsa da abubuwan da ya alakantu da su da abubuwan da ya ke tattare da su da abinda ya mallaka, dukkaninsu sun kasance da da rahamar Allah da jin kansa, sannan Allah ya nemi dan adam da ya fuskanto ya juyo ya zuwa gareshi da kuma juya baya ga dukkanin alakoki da dangantaka da abinda ya dangantu daga sha`awe sha`awensa na jinsi domin ya zamanto halifan Allah cikin kasarsa, lalle babu mai kacibus da kyawuntawa da kusanci ga ubangijinsa face wanda ya ciyar ya sadukar da abinda yake so ma`ana sai wanda ya juya baya ga abinda ya alakantu da shi daga duniya.

Allah matsarkaki yace:                       

﴿ لَنْ تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّى تُنْفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ ﴾

Ba za ku taba samun kyautatawa ba har sai kun ciyar daga abinda kuke so.[2]

Ya kai dan adam lallai kai mai fafutika ne zuwa ga ubangijinka matukar fafutika kuma tabbas zaka sadu da ubangijinka, saboda ka fuskance shi ta hanyar juyawa duniya baya da guje mata, sannan ka saukar da ni`imomi cikin hidimar wanda yayi maka ni`imar domin nuna godiya gareshi , ka bautawa ubangijinka saboda shauki soyayya da iklasin da saninka gareshi.

Allah matsarkaki sakamkon rahamarsa ya baiwa dan adam abinda yake so daga abubuwan da ya alakntu da su daga duniya da sauran dadudduka mala`iku suna ganin hakan yana daga cikin abubuwan da zasu bada gudummawa wajen fadawa mutum cikin wutar hawiya  da barna da zubar da jini sunga yadda mutum yake juya baya ga ubangijinsa da kuma karkatarsa ga tarkacen duniya da kayayyakin adonta da rudunta sai dai cewa karkatar dan adam ga ubangijinsa da watsi da duniyarsa da abinda ke cikinta saboda zuhudu da tsantseni da tsoron Allah da begensa ta buya garesu, sai ya kasance kadai dai sunka tsundumar dan adam cikin munana ayyuka bas u ga daukakarsa da hawansa zuwa ga falaloli ba saboda misalin wannan Allah yake cewa:    

﴿ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لا تَعْلَمُونَ﴾

Ni na san abinda baku sani ba.[3]

Allah yanada ilimi kan cewa adamu zai fuskanto zuwa gareshi lalle shi Adamu ba kamar iblis bane a kowanne lokaci da zai kasance cikin juyawa ubangijinsa ba hakama ba kamar mala`iku bane da su tsantsar  fuskantowa ga ubangiji suke, da wannan ne ma  adam ya fifita kan mala`iku, mala`ikun sukan kasance cikin hidimarsa ya zamanto shi sukaiwa sujjada, sai mu lura.

 

Habila da kabila da `yan`uwan annabi yusufu:

Domin Karin bayani cikin abinda muka ambata a sama zamu dan kawo misali, lalle habila da kabila sun kasance daga uwa da uba daya, lalle su biyun dag adamu da hauwa`u suke, sai kabila ya nemi daukaka duniya  ya ga cewa kusanci da sadaukarwa `dan`uwansa ya karbu wajen ubangiji koma bayan nasa kusanci da sadaukarwa  sai hakan ya sanya masa yin hassada ga `dan`uwansa har ya kai ga ya kasheshi shi kuma ya fadawa cikin wutar hawiya saboda juyawa bayansa baki daya ba tareda wani kaidi ba ya kuma mutu kafiri, haka lamarin yake dangane da `yan`uwan yusufu, lalle soyayyarda mahaifi duk da kasantuwarta abu mai kyawu `yan`uwansa sun nufi kau da yusufu daga fuskar mahaifinsu  sakamakon suna tunani cewa mahaifinsu yana karkata ga yusufu fiye da yadda yake karkata garesu alhalin dukkaninsu `yan`uwan juna ne wannan aiki na mahaifinsu bai kasance kface rashin sanin yadda suke kallon abinda yake aikata dangane da `dan`uwansu. Sai suka yanke shawara kashe yusufu sukace ku kashe shi ko kuma ku batar da shi har ya zamanto ya bace daga fuskar mahaifinku abinda ya faru ya faru, sai dai cewa daga baya sun tuba an kuma karbi tubansu.

Alakantuwa da duniya itace tushen dukkanin wata barna da fasadi haka watsi da duniya ya kasance tushen dukkanin gyara da alheri. Lalle wani lokaci danfaruwa na kasancewa asasin alheri, sai dai cewa na farko yana kasancewa idan an fuskanceta an kuma juyawa uabangiji baya  na biyu kuma na kasancewa idan an fuskanci ubangiji an juya mata baya, ba nufi wai kada kwata kwata mutum ya ki duniya ya guje ta ba tareda kaidi ba kadai abin nufi shine ya maida duniya wajen neman lahirarsa wajen kasuwancin ibadarsa mahalin sujjadarsa, ya kuma tafiyar da wadannan alakoki karkashin dokokin hankali  da koyon ilimi  tarbiyar wahayi, ya sanyata  cikin hidimar masoyinsa abin kaunarsa Allah matsarkaki madaukaki  ya mayar da dukkanin alkokinsa su kasance domin Allah ya sadukar da su cikin tafarkin Allah, iadan zai so wani `d ya zamanto ya so shi domin Allah cikin sha`aninsa, idan ubangijinsa ya nemi ya sadukar da wannan `da don kusanci to lalle shi ya zamanto ya aikata hakan da cikar soyayyarsa da tsarkin niyya, ya zamanto ya sadaukar da misalin shugabanmu aliyul akbar (as) shahidi  cikin tafarkin soyayyar Allah wanda ya kasance yafi kowa kama da manzon Allah(s.a.w) cikin kyawun dabi`u da siffar halitta.

(ya Allah ka azurta da sonka da son wanda ya ke sonka da son duk wani aiki da zai kusanta ni gareka) ka dandana mini zakin soyayyyarka wanene wanda ya dandani soyayyarka sannan kuma ace daga baya ya nemi waninka, lalle shi zai sadaukar da dukkanin komai cikin tafarkin Allah gwargwadon yadda zai samu kyautatawa daga Allah( ba zaku taba samun kyautatawa har sai kun ciyar daga abinda kuke so) lalle shugaban shahidai imam husaini(as)  ya ciyarda dukkanin abinda ke gareshi domin Allah kai har ruwan fuskarsa ba bari sai da ya ciyar da shi, lalle aliyul zainul abidin (as) ya kasance wucewa ta gefen gawawwakin shahidan karbala sai ya gansu ba a binne su ba  ransa ya kusa ya fita saboda tsananin takaici da bakin ciki sai gwaggonsa sayyada Zainab ta ce masa yaya nake ganinka kana kyauta da rayuwarka kana kokarin halaka kanka sai yace hakika makiyanmu sun binne gawawwakinsu koma bayan namu gawawwakin kama basa ganinmu musulmi da har binne gawawwakinmu zai zama wajibi kans.

Dukkanin wanda bai watsi da lakantuwa d duniya ba zai wayi gari cikin mabiaya iblis tsinanne, yayinda yake cewa adamu ni nafi alheri daga gareshi , domin shi iblis ya kalli ibadarsa  cikin ruku`un shekaru dubu sittin sai ya ksa aje hakan yayi tawali`u da sujjada ga adamu, da wannan kallo na irfani zak san cewa( kowacce rana Ashura ce kuma kowacce kasa ma karbala ce) lalle cikin kowacce rana da mintunanta da sakonninta  cikin kowanne bigire  daga kasa  lalle kai kana cikin Ashura  ta hanyar juyawa zunubai da sabo da shubuhohi da makaruhi baya da kuma fuskantar Allah da falaloli da da kyawawan halaye da addinin muslunci da aiki da umarni da biyayyar Allah da nesantar sabonsa ta hanyar watsi da dukkanin abinda ya hana.

Falsafar addinin Allah da shari`arsa  dan adam domin tsara rayuwar mutane da daidaita su da tsayar da adalci cikin daidaiko da jama`a da gudanar alakantuwa da alakoki ta yanayin da zai tuke zuwa ga soyayyar Allah da bautarsa, sannan  so da kauna tsakanin daidaiku da jama`a    

﴿يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ﴾

Ya na Imani da Allah kuma yana aminta da muminai.[4]

Sai ya zamanto ya sadaukarwa dan`uwansa abinda yake gareshi.

﴿ وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ ﴾

Suna fifita wasunsu a kankin kansu koda kuwa suna cikin tsananin bukatuwa.[5]

Wannan shi ne abinda zaka gani cikin tarihin rayuwar yadda annabi(s.a.w) da iyalansa tsarkaka suka rayu, lalle sun kasance suna ciyar da talaka mabukaci da maraya da fursunan yaki abinci alhalin suna cikin bukatuwa da abincin, lalle sun ciyar fursunan yaki gurasa a rana ta uku alhalin suna tsananin bukatuwa da wannan gurasa fiye da shi fursunan domin suyi buda baki da ita daga azuminsu da sukayi na tsawon kwanaki uku ajere sai ya kasance basu yi buda baki da komai face tsuran ruwa  hakan ya sanya su kyarma da girgizar gabbai da jiki daga tsananin yunwatuwa, sai dai cewa sun sadaukar da gurasarsu ga fursunan yaki  wannan shine tsantsar musluncin muhammadu(s.a.w) na asalin.

Si dai cewa `yan`ta`addan wahabiyawan da`ish  a wannan zamani da muke ciki (ubangiji ya wulakanta su) hakika sun bata wa muslunci suna  sun munana fuskar muslunci mai karkata zuwa ga gaskiya lalle sun kasance suna kona fursuna da ransa suna msu dogaro da fadin Allah:    

﴿فَاعْتَدُوا عَلَيْهِ بِمِثْلِ مَا اعْتَدَى عَلَيْكُمْ﴾

Kuyi masa ta`addanci kamar yadda yayi muku.

Wai saboda sun zubo musu arburusai da bama bamai da wuta to suma sai suke kona fursunan da yake yakarsu a gaban idon duniya cikin akwatin talabijin kowa da kowa na kallo, to ta hakane shaidanu suke wahayi ga mutanensu cikin jirkita ma`anar kur`ani ma girma.

  husaini(as) yana ciyar da fursunan yaki a rana ta uku daga azuminsa da yayi ajere shi kuma ya kwana da yunwa. Wane mutum zai iya irin wannan sadaukarwa ta husaini.

Wanda raina yake fansarsa yana cewa: yaku shi`ana idan kuka sha daddadan ruwa ku tuna dani* idan kuka ji labarin wani bako ko shahidi ku tuna dani* ni ne jikan annabi wanda ba tareda nayi musu laifin komai suka kasheni* bayan sun kasheni sun tattake gawata da kofatun kafafun dokunansu* inama dai dukkaninku kun ga halin dana shiga ranar Ashura* ina ma kunga yadda na roki su shayar da jinjiri ruwa amma kememe suka ki shayar da shi suka ki tausayi na.

Shugaban shahidai(as)  ya gado annabawa cikin jurewa bala`o`I da musibu, idan annabi Ibrahim(as) ya shiga wutar namarudu, to imam husaini(as) ya shiga wutar yazidu(l.a) domin ya wanzu matsayin tatacacciyar zinari suka ragowar dukkanin mutane turbaya ne, lalle shi husaini(as) ya juyawa duniya baya ya kuma fuskanci Allah sai ya zamnto shine cikar hankali ta adalci a ranar Ashura a filin karbala, lalle mu da ku muna kan hanyarsa da tafarkinsa a juyin juya halin da yayi madawwami, lalle kowacce rana ashura ce kuma kowacce kasa ma karbala ce.

Karshen maganarmu muna godiya ga Allah ubangijin talikai amincin ya tabbata ga muhammadu(s.a.w) da iyalansa tsarkaka


[1] Suratu Ibrahim:24-25

[2] Alu imrana:92

[3] Bakara:30

[4] Tauba:61

[5] Hashar:9

Tura tambaya