lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Azzaluman mamaguntan Gwamnoni

Wakilai da gwamnoninsa a fadin garuruwan musulmai sun yi mulki na zalunci da matsi don karfafa turakun gwamnatinsa.

Mas'udi ya rubuta cewa: Abdul Malik Ibn Marwan ya kasance mutum mai zubar da jini, gwamnoninsa da wakilansa misalin Hajjaj da ya kasance gwamnan Iraki  da Muhallab Gwamnan Kurasan  da Hisham Ibn Isma'il Gwamnan Madina dukkaninsu sun kasance irinsa zubar da jini da kisa.

 

Note page no 63 akwai rubutu anan..

Bayan mutuwar Abdul Malik sai `dansa Walidu ya karfi ragama halifanci, duk da cewa Walidu ya kasance yana son gina kasa da rayata amma tareda haka ya sai ya zamana ya cigaba ya dora inda babansa ya tsaya ya nada lalatattun mutane Azzalumai matsayin wakilansa kan al'umma yanayin da ya kara kuntata rayuwar mutane.

A wannan zamani yankin Sham ya kasance karkashin ikon Walid, a Iraki ya nada Hajjaju Ibn Yusuf Sakafi, a Hijaz kuma Usmanu Ibn Hubaratu, a Masar Kurratu Ibn Sharik, dukkaninsu sun shahara da rashin adalci.

Ance tareda la'akari da wannan rashin adalci na shugabanni da danne hakkokin musulmai Imam Sajjad a cikin bayaninsa ya karkasa mutane wannan zamani zuwa gida shida, ya siffanta  masu rike da ragamar iko da mulki da Zakuna, sannan ya kamanta talakawan da ake Mulki da Tumaki ya samu kansa tsakankanin Zakuna da Kuraye da Dila da Aladu ya kasance Zakuna suna `daye nama da kashi da fata .

Tura tambaya