lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Gwamnatin zalunci ta Abdul-Malik ibn Marwan Iban Hakam

lokacin Imamanci Hazrat Sajjad (a.s) ya dace da lokacin bakin mulkin a daurorin tarihin muslunci, duk da cewa gabanin Imam hukumar muslunci ta fada hannun karkatattu Azzalumai, sai dai cewa a zamanin Imami na hudu yana da banbanci da daurorin da suka gabace shi a zamaninsa wadannan Azzaluman mahukunta kai tsaye a bayyane ba tareda wani boye boye ba suke take alfarmar abubuwa masu tsarki da daraja, a bayyane suke keta alfarmar Asalan addini kuma babu wani mutum da yake da tsaurin ido da zai nuna mafi kankanatr rashin laminta da yarda daga ayyukansu.

  Gabanin fara jan ragamar Imamanci Imam Sajjad ya kasance daya daga cikin fitattun Fakihai a Madina kuma ya shahara da riko da addini da zuhudu ya kasance ya sarrafa lokacinsa cikin ibada ta kai ga mutane suna kiransa da lakabin Tattanbarar cikin masallaci.

A wani fadin ance: bayan mutuwar mahaifin Halifa Abdul Malik wato Marwan Ibn Hakam Halifa Abdul Malik yana cikin Karatun Kur'ani sai dia cewa bayan yaji labarin mutuwar mahaifinsa sai ya rufe Kur'anin yace: a yanzu fa ni da kai mun raba hanya yanzu bbau ruwana da kai.

Abdul malin Ibn  Marwan ya raba hanya da Kur'ani mai girma kuma giyar mulki da gururi sun canja sun mayar da shi wani mutum mara imani, malaman tarihi sun dawwana tarihin bakar hukumarsa da cewa shine mutum na farko da ya fara hana mutane magana a gaban Halifa kuma shine mutum na farko kauracewa Amru bil ma'aruf (umarni da kyakkyawa).

Abdul Malik mulikinsa yayi dogon zango, tareda zalunci da barna da danne hakkoki ta yanda hasken imani sai da ya zamana kwata kwata babu cikin zuciyarsa, wata da kansa yayi ikirari da faruwar hakan yana mai gayawa Sa'idu Ibn Musayyab: yanzu ta kai ga na zama idan nayi aiki nagari na kwarai samsam bana yin farin ciki da shi, amma idan na aikata mugun aiki samsam bana bakin ciki daga faruwar hakan, sai Sa'idu Ibn Musayyab yace: baki dayan zuciyarka ta rigaya da mutuwa!.


Tura tambaya