lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul Karij-kan bahasin rashin halascin fara zikiri kafin kaiwa ga haddin ruku'u

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil-tareda Ustaz Assayid Adil-Alawi.

Lokaci: karfe 8-9 na safe.

Bahasi na 37, 22 ga watan Rabiu Awwal shekara 1442 hijiri.

Cigaba kan bahasin da ya gabata: cikin rashin halascin fara zikri kafin kaiwa haddin ruku'u zuwa karshen gabar da Musannif ya tsaya cikin mas'alar fatwa dalili kan haka: shi ne shi zikirin wajibi da farko yana da zarafi da mahalli, na biyu bayan kaiwa ga haddin ruku'u da samun daidaita da nutsuwa.

Zuwa da zikiri baki dayansa ko ba'arinsa kafin kaiwa ga ruku'u ko halin ruku'u ko lokacin dagowa daga ruku'u ko kuma cikin halin rashin samun daidaita a halin ruku'u cikin ganganci cikin dukkanin wadannan  surori babu banbanci ana kidaya shi cikin abind ayake kawo matsala da yake haifar da bacin sallah idna zikirin ya kasance da niyyar juzu'i, sabida riskarsa ba zai amfanar ba, amma idna ya kasance da niyyar mudlakin zikiri lallai zai riske shi da sharadin wanzuwa cikin mahallinsa sabida sakamakon rashin kari kamar yanda ya gabata kamar yanda yake shi ne zahirin fatawa.

Amma idan ya kasance ne sakamakon rafkanwa to cikin wannan hali mas'alar tanada surori: sura ta farko: babu matsala cikin ingancin sallarsa sai dai cewa tareda hakan yana lazimta masa riska abind aya subuce idna ya zo da zikirin kammale ko kuma ba'arinsa kafin kaiwa ya haddin ruku'u sai ya tuna cewa akwai matsala gabanin fita daga ruku'u lallai zai riskar da zikirin a mahallinsa tareda daidaita, kololuwar abind ayake cikinsa shi ne afkuwar zikiri farko matsayin kari da ya faru sakamakon rafkanwa, babu matsala da Karin rafkanwa lallai baya haifar da gurbatar sallah.

Na biyu: idan ya tuna da matsalar bayan fita daga ruku'u lallai sallarsa ta inganta sakamakon rashin yiwuwar riskar zikrin kuma afkuwar matsala ya faru sakamakon rafkana cikin juzu'in da ba rukuni ba, ana masa hukunci da inganci.

Na uku: idna yay a zo da zikiri a halin ruku'u sai dia cewa bai daidaita ba sai ya tuna kafin fita daga ruku'u, shin wajibi ne kansa ya riske shi ta hanyar maimaita zikirin cikin daidaita ko kuma ba wajibi bane bayan an rigaya an tafi kan ingancin sallarsa.

Anan wurin manyan Malamai sun sassaba sakamakon sassabawar maginarsu kan nutsuwa da daidaita shin sharadin zikiri ne ko kuma yanki ne da juzu'insa cikin ruku'u.

Ta yiwu wani ya ce ba wajibi bane a riske shi bisa gini kan cewa daidaita wajibin sallar ne mai cin gashin kansa kuma juzu'an sallah ne a halin shagalta da zikirin wajibi kuma na rigaya an wuce mahallinsa tunda farko sakamakon samuwar zikiri cikin kowanne hali na biyu: sakamakon faduwar umarni da shi, kuma wani abu baya canjawa daga yanda yake yab kasance shi ne farko, sakamakon koruwar maimatuwa abinda ya rasu ya zama babu shi kamar yanda a falsafa, da zia maimaita to zai zamana zikiri ne na mustahabbi ba wajibi ba, sai ya zama risk aba zata yiwu ba a wannan lokaci.

Amma bisa gini kan cewa daidaituwa da nutsuwa sharadin zikiri ne kuma wajibi ne Gairi bawai mai cin gashin kansa ba, lallai yana lazimta masa maimaitawa da riska, sabid arashin samuwar wajibi a wannan lokaci sakamakon koruwar abinda akaiwa shardi da karuwar sharadinsa.

sai dai wannan magina bata tabbata ba, tareda shakku cikin wajabcinsa Asali shi ne riko da bara'a daga maimaitawa, hakika Musannif yayi ishara ga haka cikin bahasin kalalu (matsaloli da suke afkuwa).

Assayid Kuyi (k.s) cikin Attakrirat juz 15 sh 64 ya tafi kan cewa zahiri shi ne wajabcin maimaici a fuskoki biyu da aka kaddarasu babu wani tasiri ga mgainai biyu a wannan mukami.

Bayanin haka: kamar dai yanda ya gabata cikin bahasin kira'a da ta rasa tsayuwa da cewa kaddarawa ya zama dole ya zama daga kaddara danganci tsakanin juzu'ai baki daya wannan kaddarawa tana matsayin kaddara dabaibayi da sanya sharadi, lallai kowanne juzu'i an masa sharadi da gabatar juzu'I ko sharadi da ya gabace shi, da riskuwar juzu'I da sharadi da yake zo daga bayansa ko kuma cudanye da sharadi ga juzu'I ana la'akari da haka, cikin wani lafazin muce duk wani sharadi ko dia ya kasance gabatacce kan juzu'I ko kuma ya zo daga bayansa ko cudanye da shi baki dayan haka ya kasance ne bisa hukunci danganci da ake tsinkayensu tsakankanin juzu'ai.

Misalin haka: kamar kira'a da akai umarni da ita cikin sallah ita juzu'i ce daga sallah kuma an mata sharadi da gabatar kabbara da riskar da ruku'au bayanta da cudanyuwa da suttura da kallon Alkibla da makamantansu, haka dai yake cikin sauran juzu'an sallah, shi danganci cikin juzu'ai dangane ga kowanne yana gangara zuwa ga danganci cikin sharudda da suka gabata ko jinkirtattu da cudanyayyu.

Kan wannan bayani ne shi zikirin wajibi cikin ruku shi ne wanda yake afkuwa cadanye da nutsuwa da daidaito shi zikiri ne da akai masa dabaibayi da nutsuwa shi daidaituwa zai zama abin la'akari cikin zikii a dabi'ance, babu banbanci mun tafi kan ma'anar shardiyya da la'akari da zuhurin dalilin daidaita da cewa sharadi ne na zikiri ko kuma mun tafi kan ma'anar juzu'iyya da ba'a la'akari da shi cikin zikiri, lallai shi la'akari da dabaibayi na daga abinda ya shiryar kan kiyaye danganci tsakankanin juzu'ai murakabbai, natija sai ta zama: ko dai ya faru daga mai ruku'u a halin ruku'unsa daga zikri da ya wofinta daga daidaita sakamakon rafkana bai kasancewa misdaki zikirin wajibi, ya zama dole a maimata shi a riske shi tareda wanzuwar mahalli kamar yanda hakane aka kaddara a mukaminmu bari dai wajibi ne.  akwai cigaba


Tura tambaya