lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

DAGA CIKIN SIRRIKAN HADAYA

DA SUNAN aLLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

tsira da aminic su kara tabbata ga Annabin karamci da gaskiya muhammad da iyalansa jagorori 

قال الله تعالى : (وَلاَ تَحْلِقُوا رُؤُوسَكُمْ حَتَّى يَبْلُغَ آلْهَدْيُ مَحِلَّهُ )[1]

1 Allah madaukakin Sarki yana cewa: kada ku aske gashin kanwukanku har sai hadaya ta isa mahallinta

(لاَ تُحِلُّوا شَعَائِرَ آللهِ وَلاَ آلشَّهْرَ آلْحَرَامَ وَلاَ آلْهَدْىَ وَلاَ آلْقَلاَئِدَ)[2]

Ka da ku halasta ibodajin Allah da wata mai alfarama da hadaya da ratayar rakuma.

2-hakika kissar Ibrahim badadin Allah da umarnin da aka bashi cikin mafarki na yanka dansa Isma'il (as) da canja yankan dansa da ragodaga aljanna wadanda aka amabace su cikin littfan tafsirai da hadisaioshin annabawa da tarihinsu, hakika gareku cikin Ibrahim akwai abin koyi kyakykyawa.

3-daga cikin falsafar hadaya ranar goma ga zul hijja a mina shi ne mutum ya tsarkake kansa daga danfaruwa da duniya da biyewa sha'awe sha'awe da fakewa daga babin da ke cewa:

 (اقتلوا أنفسكم )

Ku kashe kawukanku.

 قال الامام الصادق  7: «واذبح حنجرتي الهوى والطمع عند الذبيحة ».

Imam Sadik (as) yana cewa: ka yanka makogaron son zuciya da kwadayi yayin yankanka.

4- idan kuma bai samu dama ba daga hadaya to sai ya yi azumin kwanaki goma, domin ishara zuwa ga raunana sha'awa da fakewa da mutumtaka.

5-ya zama dole a kalli sharuddan abin yin hadaya tun daga lafiyarsa da isarsa yanka, haka tilas a kiyaye sharuddan yankan rai, ma'ana sabawa son zuciya da rai mai yawan umarni da mummuna ka da abain hadaya ya kasance karami sosai ko rarrauna yayin yankansa ko kuma ma'abocin aibu da ciwo da zai kasance ma'abocin wannan siffofi da bai da wata kima, ya kamata mai hadaya ya sabawa ran nan tasa mai yawan umarni da mummuna yayin samartakarta da nishadinta ma'ana lokacin kuruciyarsa shi kansa

 (موتوا قبل أن تموتوا(

Ku kashe biyewa son rai gabanin mutuwarku.

6- ana karkasa abin hadaya ranar idi ya zuwa kaso uku kaso daya zaka ci daga gareshi kaso daya kuma talakawa da muminai su ci daga gareshi, shi mumini a rayuwar ba don kansa ka dai yake yenta ba aishi mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da su

 قال الله تعالى : (لَن يَنَالَ آللهَ لُحُومُهَا وَلاَ دِمَاؤُهَا وَلكِن يَنَالُهُ آلتَّقْوَى مِنكُمْ ( [3]

7-Allah madaukakin Sarki na cewa: namanta da jininta bai samun Allah sai dai cewa takawa daga greku na samunsa.

Sai Allah ya karba daga abin yanka abin da ya kasance daga takawa don takawa zuwa ga takawa.

 (إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ آللهُ مِنَ آلْمُتَّقِينَ([4]

Kadai dai Allah na karba daga masu takawa.

8- yanka da soke abin hadaya sun kasance tun lokacin jahiliya sai dai cewa a wancan lokaci an cudanya su da shirka, ya kasance ana shafe ka'aba da jinanansu kamar yadda mushrikai suka kasance suna dora naman abin hadaya kan dakin ka'aba domin wai Allah ya karbi hajjinsu, sai muslunci ya zo domin tabbatar da hadaya sai dai cewa si musluncib ya tsarkaka daga shirka, sai ya zamanto addini m'abocin kebantacciyar alfarma, abin da ke isa ga yardar Allah bi kasance nama ba ko kitsen dabbobin hadaya, kadai makasudi cikin yardarsa shi ne ruhin aiki wanda shi ne takawa, hakika da takawa bawa ke samun damar kusantar ubangijinsa, da takawa ne hajjin alhaji da hajiya ke samun karbuwa, saboda haka neama ake kiran ranar hadaya da sunan ranar babban hajji.

9- duk aikin da akayi da niyyar kusantar Allah zai kasance karbabben aiki, kamar yadda hakan ya zo cikin hadisi mai daraja:

«انّ الزكاة جعلت مع الصلاة قرباناً لأهل الاسلام ».

Lalle hakika ita zakka an sanya tare da sallah matsayin kusanci ga ma'abota muslunci.

10- alhaji da hajiya suna yanka hadayarsu yankan ifritun biyewa son rai da kwadayi da mafaka ta haramun cikin rayukansu.

 

 عن الامام الباقر 7: «ان الله يحب إطعام الطعام وإراقة الدماء

11- daga Imam Bakir (as) hakika Allah na kaunar ciyarwa da zubar da jinni.

Ma'ana yanka dabbobin ni'ima cikin tafarkin Allah domin ciyar da talakawa da mabukata

 لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا آسْمَ آللهَ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُم مِن بَهِيمَةِ آلانْعَامِ  [5].

12- daga cikin manufofin layya da hadaya shi ne ambaton Allah.

Domin halarci amfanunsu su ambaci sunan Allah cikin kididdigaggun kwanaki bisa abin da Allah ya azurta su daga dabbobin ni'ima

13- hakika kusanci na da tarihi wanda ke komawa tun daga `ya`yan adamu, lalle kowanne daya daga cikinsu ya gabatar da kusanci sai dai cewa Allah madaukakin sarki akdai ya karbi kusanci habila salihi da koma bayan kabila azzalumi lalatacce, lalle Allah kadai yana karba daga masu takawa wadanda ke gabatar da mafi falala mafi soyuwarsu a cikin kowanne hali, sai kuma daga baya Ibrahim ya gabatr da dansa Isma'il matsayin kusanci, sannan manzon Allah(s.a.w) ya gabatar da rakuma 66 fansa daga kansa ya kuma bada rakuma 24 kan sarkin muminai Ali (as) a ranar hajjin ban kwana..

14- cikin kusanci akwai tajalin fifita da ishara zuwa ga sallamawa Allah matsarkaki, daga cikin addu'ar yanka akwai fadin:

بسم الله وجهت وجهي للذي فطر السماوات والأرض حنيفاً مسلماً وما أنا من المشركين ، إنّ صلاتي ونسكي ومحياي ومماتي لله ربّ العالمين).

Da sunan Allah na fuskantar da fuska ga wanda ya kagi sammai da kasa babu karkata yana mai sallamawa ni bana daga cikin mushrikai, hakika sallah ta da yanka na da rayuwata da mutuwata ga Allah ubangijin talikai.

15- yanka amina tsira ne dagta wuta.

قال الامام السجّاد 7: «إذا ذبح الحاج كان فداه من النار.

Imam Sajjad (as) yana cewa: iadan mahajjaci ya yanka hadaya zai kasance fansarsa daga wuta.

Abin yanka na da zahiri wanda shi ne kasantuwarta dabba da siffanrta da aka anbata cikin fikihu muslunci. Haka ma yanada badini wanda shi ne ran dabbantaka, lalle shi ranar idi ya yanka domin neman kusanci ga Allah matsarkaki.

16-yanka da abin yanka na daga cikin ayoyin nuna godiya ga Allah, lalle mahajjaci dayanknsa yana godiya bisa ni'imar ubangijinsa da samun nasararsa da galabarsa kan biyewa son rai wadda ke yawan umarni da mummuna, da yankan da yakewa abin yanka kamar yana yanka son ransa wadda ke yawan umarni da mummauna, sai ya nuna godiyarsa ga Allah bisa hakan.

 (وَآلْبُدْنَ جَعَلْنَاهَا لَكُم مِن شَعَائِرِ آللهَ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌ فَاذْكُرُوا آسْمَ آللهَ عَلَيْهَا صَوَافَّ فَإِذَا وَجَبَتْ جُنُوبُهَا فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا آلْقَانِعَ وَآلْمُعْتَرَّ كَذلِکَ سَخَّرْنَاهَا لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ( [6]

Kuma rakuma na sanya su gareku daga ibadojin Allah gareku ckinsu akwai alheri ku ambaci sunan Allah kansu suna tsaye kan kafafunsu uku sannan idan geffansu suka fadi to kuci daga garesu kuma ku ciyar da mai wadatar zuci da maroki. Kamar haka muka hore muku ita tsammaninku kwayi godiya.

Wannan yankan abin hadaya nuna godiya ne ga Allah bisa shiryarwarsa da datarwarsa kamar yadda Allah matsarkaki ya umarci annabinsa kan godewa ni'imarsa ta alkausar da soke rakumi:

 (إِنَّا أَعْطَيْنَاکَ آلْكَوْثَرَ * فَصَلِّ لِرَبِّکَ وَآنْحَرْ)[7]

Hakika maun baka alheri mai tarin yawa* kayi sallah domin ubangijinka sannan ka soke rakumi.

17- da yankan hadaya zaka tuna da kissar Annabi Ibrahim (as) da sallamawarsa ga umarnin ubangiji da hakuncin dansa Isma'il da imaninsa.

 (يَا أَبَتِ آفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ آللهُ مِنَ آلصَّابِرِينَ ) [8]

Ya babana ka zartar da abin da aka umarceka da izinin Allah z aka sameni daga cikin masu hakuri.

Kan wannan ma'anar ne imam sajjad (as) ya yi ishara

الامام السجاد 7 بقوله : «فعند ما ذبحت هديک نويت انّک اتّبعت سنّة إبراهيم بذبح ولده وثمرة فؤاده وريحان قلبه وحجّة سنّته لمن بعده ، وقرّبه إلى الله تعالى لمن خلقه » فالحاج كابراهيم وإسماعيل في معرض الابتلاء الإلهي والاختبار والامتحان في دار الدنيا، ولن ينال الله لحومها ولا دمائها ولكن يناله التقوى منكم ، فيقبل قربان ما كان مثل قربان هابيل وإبراهيم الخليل  8.

Imam Sajjad (as): lokacin da kake yanka abin hadayarka to kayi niyyar cewa kai ka yi biyayya ga sunnar annabi Ibrahim (as) wanda yake yanka dansa Isma'il kayan marmarin zuciyarsa furen zuciyarsa, hajji sunnarsa ne ga wanda ya zo bayansa, kusancinsa ne ya zuwa ga Allah madaukaki ga wanda ya halitta.

Mahajjci misalinsa kamar misalin Ibrahim da dansa Isma'il ne cikin bijira ga jarrabtar ubangiji da ibtila'I cikin gidan duniya, naman hadaya da jininta bai kaiwa ga yardarm Allah sai dai cewa takawa daga gareku ke risker yardarsa, Allah zai karbi hadaya da kusanci kwatankwacin kusancin habila da Ibrahim.

ـ قال رسول الله 6: «إنّما جعل الله هذا الأضحى لتتّسع مساكينكم من اللحم فأطعموهم[9] .

18- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: kadai dai Allah ya sanya wannnan layya domin talakawan cikinku su yalwata da nama saboda haka ku ciyar da su.

19- hadaya da kusani na daga girmama ibadojin Allah cikinta akwai babban alheri mai yawa.

(وَآلْبُدْنَ جَعَلْنَاهَا لَكُم مِن شَعَائِرِ آللهَ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌ)

Kuma rakuma mun saya su gareku daga ibadojin Allah cikinsu akwai alheri babba.

(وَمَن يُعَظِّمْ شَعَائِرَ آللهَ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى آلْقُلُوبِ) [10] .

Duk wanda ya girmama ibadojin Allah lalle ita na daga cikin takawar zukata.

قال الامام الصادق  7: «إذا رميت الجمرة فاشتر هديک ان كان من البدن والبقر... وعظّم شعائر الله عزّوجلّ [11] .

Imam Sadik (as) ya ce: idan ka yi jifan sahidan ta ka je ka sayo abin hadayarka, idan ya kasance daga rakuma da shanu…. Ku girmama ibadojin Allah mai girma da daukaka.

20- yankan abin hadaya na jawo gafarar Allah.

قال رسول الله 6: «كانت أوّل قطرة له كفّارة لكلّ ذنب .

Manzon Allah (s.a.w) ya ce:  digon jini na fara da zuba daga abin hadaya zai kasance kaffara ga dukkanin zunubansa.

قال الامام الصادق  7: «انّه يغفر لصاحبها عند أوّل قطرة تقطر من دمها إلى الأرض ».

Imam Sadik (as) ya ce: lalle za a gafartawa ma'abocin hadaya yayin digar jininta na farko ya zuwa kan kasa.

21- yankan hadaya zikiri ga Allah matsarkaki.

قال الله تعالى : (لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا آسْمَ آللهَ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُم مِن بَهِيمَةِ آلانْعَامِ) [12] .

Allah madaukakin sarki na cewa: domin su halarci abubuwan amfani garesu su ambaci sunan Allah cikin sanannun kwanaki bisa abin da Allah ya azurta su daga dabbobin ni'ima.

Zikirin da ake yinsa mayin hadaya kadai dai shi na daga ambaton Allah matsarkaki dokmin yay i nuni ga abin da ake nufi cikin layya shi ne ambaton sunan Allah abu ne mai kyawu cikin kowanne hali lalle shi ni'ima ne kan bayinsa, lalle abin nufi daga rayuwar duniya shi ne neman kusanci ga Allah ta hanyar bautarsa da godiya cikin tsarkakar niyya, lalle ita duniya kamar wata gona ce da ake shuka lahira cikinta lalle ita duniya kasauwa ce ta waliyyan Allah

Abin nufi daga ayyukan hajji da suara game gari sh ne ambaton Allah cikin boye da bayyane cikin zahiri da badini kan harshe da zuciya da dukkanin gabban ciki da na waje, mahajjaci yana yanka  hadayarsa a zahiri ya ambaci Allah a cikin zuciyarsa, haka lamarin yake cikin kowanne aiki daga ayyukan hajji cikin kowacce ibada daga ibadojin Allah matsarkaki madaukaki, lalle hajji yana bayyana mana imani da tushe da makoma da abubuwan da ke tsakankaninsu daga akidoji da suluki da kyawawan ayyuka cikin muslunci, cikin kowanne hadaya da ibada akwai sirri kamar yadda bayanin haka a jumlace ya gabata, amma ta fuskanin dan buga misali zak kammala wannan babi da abin da ya zo daga sarkin muminai ali (as) domin mai karatu da fadakarsa da basirarsa ya dan tsinkaya daga abin da yake gurinsa daga taskokin sakafa da ilimi a bayan hakan akwai sirrika da hikimomi

إنّ أميرالمؤمنين  7 سُئل عن الوقوف بالجبل ـ عرفات ـ لِمَ لَمْ يكن في الحرم ؟ فقال : لأنّ الكعبة بيته ، والحرم ببابه . فلما قصدوه وافدين وقفهم بالباب يتضرّعون .

قيل له : فالمشعر الحرام لِمَ صار في الحرم ؟ قال : لأنّه لمّا أُذن لهم بالدخول وقفهم بالباب الثاني ، فلمّا كان تضرّعهم بها أذن لهم لتقريب قربانهم ، فلمّا قضوا تفثهم تطهّروا بها من الذنوب التي كانت حجاباً بينهم وبينه ، أُذن لهم بالزيارة على الطهارة ، قيل له : فلِمَ حرّم الصيام أيّام التشريق ؟ قال : لأنّ القوم زوّار الله، وهم في ضيافته ولا يجمل بمضيف أن يصوِّم أضيافه .

قيل له : فالتعلق بأستار الكعبة لأيّ معنى هو؟ قال : مثل رجل له عند آخر جناية وذنب ، فهو يتعلّق بثوبه يتضرّع إليه ويخضع له ، أن يتجافى عن ذنبه.[13]

Lalle wata rana an tambaye sarkin muminali (as) game da tsayuwar Arafat me ya sa hakan bai kasance a haram ba? sai ya ce: saboda ka'aba dakinsa ce shi kuma harami kofa ce ta sa, yayinda suka nufe shi sai ya tsayar da sub akin kofa suna magiya suna roko.

 Sai aka tambaye shi me yasa mash'arul haram ya kasance a haram? Sai yace: yayinda aka yi musu iziin shiga sai aka tsayarar dasu a kofa ta biyu, yayinda suka yi ta magiya sai aka yi musu izini domin kusantar kusancinsu, bayan sun kammala ibadarsu sai suka tsarkaka da ita daga zunubai wadanda suka zame musu hijabi tsakaninsu da ubangijinsu, sai aka musu izinin ziyara bisa tsarkaka, sai aka tambaye shi to me yasa aka haramta yin azumi kwanakin tashrik ma'ana ranakun 11-12 -13 ga Zul hijja? Yace: saboda mutane sunzo ziyarar Allah ne kuma suna cikin liyafarsa kuma bai kyawunta game karbar baki ya sanya bakinsa yin azumi

Sai aka kara tambayarsa to shi kuma rataya da labulen ka'aba da wacce ma'ana kenan? Yace: misalin mutumin da yake da laifi da zunubi sai yake lulluba da tufafinsa ya fake da shi don tsira daga zunubansa.

Kiran mu na karshe shi ne lalle godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

 

 



[1] Bakara:196

[2] Ma'ida:2

[3] Hajji:27

[4] Ma'ida:27

[5] Hajji:28

[6] Hajji:36

[7] Kausar:1-2

[8] Assafat:102

[9] Alfakihu: juz 2 sh 214

[10] Hajji:32

[11] Wasa'ilul shi'a:abwabul zabhi.

[12] Hajji:28

[13] Alkafi: juz 4 sh 224

Tura tambaya