lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 5 RABIU SANI 1441 CIKIN TA’ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHI DA NAKADI A KAN TA’ARIFOFIN DA AKA AMBATA

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalu Amil Islami.

Lokaci: karfe 9 na safe.

Cigaba kan bahasin da ya gabata cikin ta’arifin ijtihadi a isdilahin fikhu da abubuwa da suka gangara kansa da nakadodi da ishkalai cikin wannan mukami daga munakashoshi daga fuskar kasantuwarsa bai tattaro dukkanin abubuwa da suke cikinsa ba bai kuma katangu daga kutsen bare ba bisa gini kan kasancewa ta’arifi a hakikance ko da kuwa cikin abubuwan jeka na yika kamar yanda yake cikin tabbatattun abubuwan halitta cikin ta’arifin abubuwa da zatinsu wanda yake banbanta sashensu daga sashe, hakika banbantuwa kamar yanda yake cikin ilimin falsafa yana tabbata ne da mahiya hakika bisa gini kan Asalatul wujud kamar yanda yake shi ne ra’ayin Masha’iyun daga falasifa.

Daga ciki ta’arifi akwai wanda Muhakkikul Iraki (k.s) ya kawo a cikin littafin Makalatul Usul juz 2 sh 201 da cewa: (tabbatar da samuwar wazifa ta take ta aiki) bisa gini kan cewa kaidojin kaidojin na katangewa fadinsa (tabbatar da wazifa) yana nufin taklifin adddini da wazifar shari’a ya tattara kan idan istinbadi ya lazimta sadaukar da dukkanin karfi kamar misali idan ace mas’alar ta kasance mas’ala ta furu’a buyayya mai wahalar gaske kishiyar hakan shi ne idan mas’alar ta kasance bayyananna saukakka.

Kamar yanda kalmara (wazifa) ta zo ne maimakon Kalmar hukuncin shari’a wanda ya tattaro kowanne wuri daga wuraren istinbadi babu banbanci cikin kasancewarsa ya tuke ga sanin hukuncin waki’i tabbataccen hukunci kamar yanda yake cikin Amarat haka zalika da Hukumul zahiri kamar yanda yake cikin Usul babu banbanci cikin kasantuwarsa hukuncin shari’a ko na hankali, kamar misalin ihtiyadi da takyir da hujjiyar zannil insidadi kan hukuma da kashaf.

Assayid Muruj (k.s) cikin littafin Muntahal Dirayatu juz 10 sh 224 ya tafi kan cewa mafi dacewa cikin ta’arifi bayyana shi a matsayin: mumini ya tabbatar da hukunci a shari’ance ko hankalce daga dalilan fikhu wanda sanadinsa yake dacewa mufradat da kaidoji na katangewa tareda dukkanin maginai na sabani cikin mas’alolin usul babu banbanci cikin wanda yayi inkarin hujjiyatul zanni kai tsaye mudlakan ko kuma ya tafi kan hujjiyatl zunun a kebance kamar misalin Kabarul Sikatu da zawahirul kitab kamar yanda yake a wuri malaman ilimin usul daga malamanmu na imamiyya ko kuma ya tafi kan hujjiyar zannul insidadi ratayayye babu banbanci cikin ratayuwarsa kan kashaf ko kan hukuma da dai makamancinsu.

Karin bayani kan haka: hakika kaidojin da suka zo cikin ta’arifi suna daga cikin kaidojin katangewa.

Na farko: fadinsa: (tabbatarwa mumini) lallai mukallafi a cikin wannan mukami ya zama dole ya samu yakini da ya kuma tabbatar da abinda zai amintar da shi daga ukuba cikin aiki ko bari, tabbatarwa mumini ya tattaro ijtihadi da yake karkarewa zuwa ga sanin hukunci na waki’i da na zahiri.

Canja (wazifa) da (mumini) yafi dacewa, sabida ya tattaro wuraren Usulul Amaliyya bisa gini kan inkarin hukumul zahiri, sai dai cewa zahiri daga (wazifa) cikin hukunci mudlakan daga hukumul waki’I da hukumul zahiri, baya tattaro ijtihadi cikin Usulul Amaliyya shar’iyya kamar misalin bara’a shar’iyya a wurin wanda yake inkarin sanya hukunci zahiri cikinta lallai shi yana wadatuwa daga hukumul waki’i, bari dai hukumul waki’i shi ne masaukar bara’a yayin rashin nassi da jumlacewarsa ko kuma cin karo da juna tsakanin nassoshi gud abiu da faduwar dukkaninsu.

Kamar yanda ake nakadi da ishkali kan ta’arifin Muhakkikul Iraki (k.s) da cewa da ya halasta ayi riko da wazifa cikin ta’arifin da hakan ya wadatar daga kawo kaidi fi’iliya a ai aiki wanda ya kasance daga wata fuskar daga marhalolin hukunci daga iktiza’iyya da insha’iyya da fi’iliya da tanajjuz, sabida maksudin wazifa shar’iyya shi ne hukunci wanda ya kai martabar aike cikin umarni da tsawatarwa cikin hani, sakamakon rashin waiwaye ya zuwa hukumul iktiza’i da insha’i da suka kasance maudu’in hukuncin hankali da yake wajabta sauke nauyi daga gareshi kuma mumini ya samu tabbas kansa, a bayyane yake cewa Magana kan ijtihadi wanda yake dan’uwan ihtiyadi da taklidi da ma’anar sauke wazifa, lallai mukallafi dole ya kasance daya daga cikin mutane uku: ko dai ya kasance Mujtahidi ko Muhtadi Ko Mukalladi.

Sannan kaidin (tabbatarwar mumini) ya tattaro ra’ayin insidad babu banbanci cikin kansantuwar mai kashafi ko kuma hukuma haka zalika ya tattaro ra’ayin infitahu, sabin abinda ake bukata daga kowa da kowa daga ijtihadi shi ne tabbatarwar mumini, bayan zartuwar hukunci karkashin inuwar ilmul ijmali ko ihtimali duk yanda yanayin ijtihadin da tabbatarwar ta kai.

Amma kaidin (a hankalce) lallai wannan yana shiga karkashin zaton da hukuncin shari’a kan hukuma bisa gini kan insidad ai kullewar kofa zuwa ga sanin hukuncin shari’a a hakikance, haka zalika a wuraren Usul Amaliyya wanda suka jingina ya zuwa hukuncin hankali kamar misalin Bara’a Akliya da ta jingina ya zuwa munanar yin ukuba ba tareda yin bayani ba da ka’idar Ihtiyad da Ishtigalul zimma cikin geffan abinda aka sani a jumlace cikin ilmul Ijmali da Asaltul Takyir.

Amma kaidin (a shari’ance) lallai yana shiga karkashin istinbadul galibin hukunce-hukunce, sabida jigo dalilai na tafsiliyya wacce Mujtahid yake komawa zuw agaresu cikin mukamin istinbadi sune Kur’ani da Sunna tsarkakka.

Amma kaidin (daga dalilan fikhu) lallai hakan yana fitar da ihtiyadi da taklidi, sai ta’arifin ya zama katangagge daga shigowar bare, amma ihitiyadi sakamakon kasancewarsa makoma ta aiki ga waki’u a kankinsa ba tareda bukata tabbatarwar mumini ba, sai ka lura, amma taklidi sakamakon kasancewarsa bayyane  hakika tabbatarwa madaukakiya ga mumini ta jingina zuwa ga fatawar wanda yakewa taklidi bawai daga dalilan fikhu daga littafin Allah da sunna da ijma da hankali ba.

A karshe duk da cewa ba da shi zamu rufe bahasin ba: hakika istinbadin hukuncin shari’a daga dalilansa na tafsili ya dogara kan zuraffar malaka cikin zuciya wacce da ita ne mujtahidi yake samun ikon mayar da rassa zuwa ga asalai, malaka kamar yanda yake a Ilmul Aklak a matakin farko bata samuwa face da aiki da dukufa a kai, a mataki na biyu shi ne a halance, sannan malaka iata wani yanayi ne na zuciya da take samuwa sakamakon dukufa kan tamrini ba tareda kakkautawa ba cikin kowanne irin ilimi da fanni kamar misalin tukin mota da ijtihadi, bata samuwa face dda sanin ilimummukan nazari da dokoki da ka’idodji da istinbadi ya doru kansu kamar yanda da yardar Allah bayanin zai zo a nan gaba kan haka, shi ijtihadi a isdilahin fikhu ya dogara ne da wadannan ilimummuka na nazari kamar yanda yake cikin Hauzozin ilimi a wurin malamanmu na imamiyya, bai buya ba cewa yanki na karshe da yake dalili da illa kan samun wannan karfi da malaka shi ne kwarewa da gogewa kan ilimin Usulul Fikhu da sanin ka’idoji da Anasirul mushtaraka cikin mas’lolin fikhu na rassa na shari’a da akai tanadinsu domin samun hujja kan hukunci kamar yanda bayani ya gabata daga ta’arifi na Usul.

Duk wanda ya kware ya samu gogewa cikin wadannan ilmummuka daga ka’idojin fikhu da ilmul usul daga ilmummukan nazari da ake bukatuwa da su cikin samun hujja da tsamo hukunce-hukunce daga dalilansu zai kasance Mujtahidi da za a iya dogaro da shi kuma a haramun ne gareshi ya koma zuwa ga wani Mujtahidi daga Mujtahidai, domin a yanzu ya san halal da haram, cikin haka babu banbanci cikin kasantuwarsa Adali ko faisik a kankin kansa, sabida sharadin adalci kadai yana kasancewa kan mai bada fatawa da Marja’in da ake taklidi da shi haka cikin Alkali, sabida haka ijtihadi a isdilahance bai dogara kan ba tsaya kadai kan karfi na tsarkaka kadai da haske daga Allah da yake jefa shi cikin zuciyar wanda ya so daga masu istinbadi, duk da cewa dukkanin kamalar ilimi da aiki daga gareshi uske gangarowa matsarkaki ta’ala daga cikin tajallin kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa cikin mukamin siffar aiki da aka ciro daga siffofin zati da aka ciro su daga zatin Allah matsarkaki.

Abinda ya zo cikin littafin Alkawanin da Alfusulul muhimma daga (la’akari da karfi na tsarkaka) idan suna nufin tsuran malaka da kudura kan istinbadin hukunci to maganarsu ta kasance a mahallinta.

Sabida ba abu mai sauki ba ace koma ince bama abu ne mai yiwuwa ace anyi istinbadi ba tareda malaka ba, idan kuma suna nufin wani abu daban daga ishraki da failolin ubangiji kan zuciyar Mujtahidi to wannan yana daga abinda bamu samu dalili kan ingancinsa ba kuma bama a la’akari da shi a cikin asalin istinbadi da ijtihadi domin samun malaka ga wanda ya dandake ilmummukan nazari daga fikhu da usul babu banbanci cikin kasancewarsa Adali ko Fasiki Mumini ko Munafiki.

Zamu cigaba da yardar Allah ta’ala.

Tura tambaya