lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Darussan hauza> darasin bahasul karijul fikhu shekara ta 1438-1439 watan rabi'u awwal hijri-bayani kan cin karo da juna tsakanin riwayar sahihatu Halabi mai shiryarwa zuwa ga halascin yanke sallah gabanin shiga ruku'u cikin wanda ya manta yin kiran sa

 

وفي صحيحة علي بن يقطين:

وبإسناده ـ محمد بن الحسن ـ عن أحمد بن محمد عن الحسن بن علي بن يقطين عن أخيه الحسين علي بن يقطين قال: سألت أبا الحسن عليه السلام عن الرجل ينسى أن يقيم الصلاة وقد إفتتح الصلاة؟ قال عليه السلام: إن كان قد فرغ من صلاته فقد تمت صلاته، وإن لم يكن فرغ من صلاته فليعد([2]).

Ya zo cikin sahihatu Aliyu ibn yakdinu:

Da isnadinsa-daga Muhammadu ibn hassan daga Ahmad ibn Muhammad daga Hassan ibn Aliyu ibn yakdinu daga `dan'uwansa Husaini ibn Aliyu ibn yakdinu ya ce: na tambayi Abu Hassan amincin Allah ya kara tabbata gare shi gameda mutum da ya tada sallah sai ya zama ya manta da tsayar da ikama? Sai ya ce: idan ya kasance ya riga ya idar da sallarsa hakika sallar ta cika, idan kuma bai idar da sallarsa ba to ya sake sallah.

Ance hadawa ne tsakankaninsu biyun zaka dora ta farko gabanin ruku'u sai dai cewa wannan ra'ayi ya nesanta matuka, lallai fadin imam amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

 (وإن لم يكن فرغ من صلاته).

Idan bai kasance ya idar da sallarsa ba.

Wannan nassi ne mabayyani da ya ke shiryarwa kan cewa ko da tunawarsa ta kasance bayan dagowa daga ruku'u ne lallai matukar dai bai idar da sallah ba sai ya sauya sabuwar sallah bayan ya gabatar da tsayar a ikama. Bari dai abin da ya fi cancantuwa da dorawa shi ne ka dora sahihatu halabi kan halascin wucewa da fuska mudlaka wasu  nassosi na daban na yin shaida kan haka, wadanda suka gangaro cikin babin kamar yadda ya gabata, sannan ka dora sahihatu Aliyu ibn yakdinu kan dukkanin juyowa matukar dai bai fita daga sallarsa, zuwa ga wannan ma'ana ne shaik dusi ya tafi cikin litattafansa Tahzibul Ahkam da Istibsar. Sai dai cewa malamanmu sunyi suka kan sahihatu Aliyu ibn yakdinu, bari ma dai cikin littafin muktalaful shi'a akwai da'awar ijma'I kan sabaninsa, sakamakon rashin samun wanda ya tafi kan juyowa bayan dagowa daga ruku'u, sai ya zamanto abin da ya ayyanu shi ne watsi da riwayar kamar yadda hakan shi ne ra'ayin da muka zaba.

Sayyidul Ku'I (ks) ya tafi kan cewa ingantaccen ra'ayi cikin fuskar hada riwayoyi biyu shi ne ra'ayin da shaik Dusi ya tafi kai cikin Tahzib da Istibsar ya bishi cikin mafatihu daga dora al'amarin cikin wucewa cikin sahihatu Halabi kan halasci sakamakon bayani karara na wannan ingantacciyar riwaya cikin son maimaici matuakr bai idar da sallah b, lallai haramcin yanke sallaha na kan fadinta dalilinta kuma ijma'I ne, shi daga dalili lubbi yake sannan gwargwadon abin da aka samu yakini kansa shi ne ara'ayin da muka zaba muke kai bari dai babu ijma'i cikin wannan mukami bayan tafiyar shaik Dusi kan halascin yanke sallah matukar dai bai idar da ita ba sakamakon aiki da sahihatu Aliyu ibn yakdinu na'am hakika mashhur din malamai sun bijire mata sun ki aiki da ita, sai dai cewa bijirewarsu ba zai korewa ingantacciyar riwaya matsayinta bisa ra'ayin da muka zaba.

Natijar da ka cimma daga dukkanin abin da ya gabata shi ne cewa: manta kiran sallah da tsayar da ikama har ta kai ga shiga farilla mustahabbi ne a yanke sallah domin riskarsu, kololuwar al'amarin shi ne wuraren faifaicewa suna sassabawa bisa sassabaar wuraren yankewa, abin da yafi shi ne idan tunawa ta kasance gabanin shiga karatun sallah, haka falala na biyo masa idan yaksance gabanin shiga ruku'u, kasansu cikin falala shi ne idan ta kasance gabanin idar da sallah. Maganarsa ta kare Allah ya daukaka matsayinsa.

Sannan cikin wani mukamin bijirewa da cin karo da juna daban tsakanin sahihatu Halabi da riwayar Zakariya ibn Adam.

وعنه ـ محمد بن الحسن ـ عن محمد بن الحسين عن إسحاق بن آدم عن أبي العباس الفضل بن حسان الدّالاني عن زكريا ابن آدم قال: قلت لأبي الحسن الرضا عليه السلام: جعلت فداك كنت في صلاتي فذكرت في الركعة الثانية وأنا في القراءة أني لم أقم فكيف أصنع؟ قال: اسكت موضع قراءتك وقل: قد قامت الصلاة، قد قامت الصلاة، ثم أمض في قراءتك وصلاتك وقد تمت صلاتك([7]).

  daga gare hi daga Muhammadu ibn Hassan daga Muhammadu ibn Husaini daga Is'hak ibn Adam  daga Abbas ibn Hassan dallani daga Zakariyya ibn Adam ya ce: na cewa Abu Hassan Rida  amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: raina fansarka: na kasance cikin sallata cikin raka'a ta biyu sai na tuna cewa lallai ni banyi ikama ba to kaka zanyi? Sai ya ce: kayi shiru a wurin da kake karatu ka fadi (kad kamatus salat) sau biyu sannan daga bayan ka cigaba da karatunka da kuma sallarka.

Ta yiwu ace an samu bijirewa juna da sahihatu da farko, kamar yadda ita ta kebantu ga abin da ke shiryarwa kan gurbatar sallah da maganar gurgu, sai dai cewa an amsa kan wannan bijrewar da cin karo da junan da kebanta kasantuwa raunin isnadin da Ishak ibn Adam lallai shi abin wurgi ne, haka raunanar isandin da Abu Abbas  lallai ya kasance wanda ma ba a sanshi, saboda haka wannan bijirewa ba ta karfafa haka kebanta, sai a lura.

Sannan ya kawo abin da yake bijirewa sahihatu abin da ya zo cikin riwayar nu'umanu razi.

وعنه ـ محمد بن الحسن ـ عن محمد بن الحسين عن جعفر بن بشير عن نعمان الرازي.

قال: سمعت أبا عبد الله عليه السلام وسأله أبو عبيدة الحذاء عن حديث رجل نسي أن يؤذن ويقيم حتى كبّر ودخل في الصلاة؟ قال: إن كان دخل المسجد ومن نيته أن يؤذن ويقيم فليمض في صلاته ولا ينصرف([8]).

Daga gare shi daga Muhammadu ibn Hassan daga Muhammadu ibn Husaini daga Jafar ibn Bashir daga Nu'umanu Arrazi.

Ya ce: na ji Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata gare shi Abu Ubaida Hazza'u ya tambaye shi game da maganar mutum da ya manta yin ikama har ta kai ga yayi kabbarar harama ya fara sallah? Sai ya ce: idan ya kasance tun farko ya shiga masallaci da niyyar yin ikama to ya cigaba da sallarsa kada ya yanke.

Fuskar karo da juna: ta yiwu ace lallai ita wannan riwayar tana wajabta kayyaduwar sahihatu da kebanta da yankewa da maimaita sallah gabanin shiga ruku'u da kasantuwar idan bai kasance daga niyyarsa ba kiran sallah da tada ikama, amma sun kasance cikin niyyarsa lokacin da ya shiga masallaci to sai ya cigaba da sallah ya isu da danganawa daga aiki. Ta yiwu wannan fuska ta samo asali ne daga abin da aka rawaito daga gare su amincin Allah ya kara tabbata gare sun a fadin cewa  

 (إنّما الأعمال بالنيات).

Kadai dai dukkanin ayyuka suna tare da niyya.

Sai dai cewa an amsa wannan: da farko dai ba ta karfafa riwaya ta biyu cikin gogayya da sahihatu sakamakon raunin isnadinta da Nu'umanu Arrazi lallai shji babu wanda ya wassaka shi.

Na biyu: takaituwar shiryarwarta, lallai shiga masallaci babu wata kebata cikinsa, sai ya zama da matsayin isuwa kan kasantuwarta ta ginu a kan kiran sallah da tada ikama gabanin wasu yan mintuna daga shiga sallah, daga bayyanannen Abu shi ne galibin masallata haka suke, dorawa kan wanda ya manta a wannan lokaci kan wanda bai niyya ba yana daga dorawa mudlaka kan fardi da ya karanta, shi kamar yadda kake gani ne, sai a lura.

Sannan mawallafi (ks) ya ce: cikin kasantuwar abin da idan ya manta kiran sallah da tada ikama ya halasta gare shi yankewa da komawa matukar bai shiga ruku'u ba, shi kadai ya kasance ko waninsa a hlin zikiri.

 ba idan ya yi dauki azamar bari ba a zamani a sabu da shi sannan ya nufi komawa.

Amma rashin banbanta tsakanin kasantuwarsa shi kadai ko waninsa kamar limami wannan shi ne abin da mashhur suka tafi kai sabanin muhakkik cikin littafin shara'i'I ta yadda ya kebance shi da wanda yake sallah shi kadai,  makamancin haka abin da ya zo cikin littafin mabsud m 1 sh 95 da waninsa zahiri rasjhin dalili kan hakla bayan idlakin nassi da fatawa kamar yadda ya kasance daga fiye da mutum guda daga malamai, idan kuma ance tabadu ne da karkatar idalakin zuwa ga wanda ya manta alhalin yana sallah shi kadai to wannan wani ra'ayi da babu dalili kansa, sai dai cewa  kaddara manta kiran sallah da tada ikama cikin sallar jam'i yana daga abin da ya karanta, saboda ya kebanta da cikin abida idan limami ya manta kiran sallah da tada ikama wanda hakan yana daga abin da ya karanta, ya zo cikin littafin Almasalik       

 (لا فرق في ذلك بين المنفرد والإمام لإطلاق النص والأصحاب فتقييده بالمنفرد هنا ليس بوجه) وفي حاشية المبنى والإيضاح عنهما المستمسك (5: 207) (أنه من باب التنبيه بالأدنى على الأعلى لا للتقييد).

Babu banbanci cikin haka tsakanin wanda ke sallah shi kadai da limami sakamakon idalakin nassi da malamai saboda haka kayyade shi da mai sallah shi kadai a wannan muhalli bai da fuska. Cikin hashiya da idahu daga garesu biyun, lallai shi yana daga babin fadakarwa da mafi kusanci  a kan mafi daukaka ba kaidi bane.

Sannanabin da ya ambata daga halascin yanke sallah da komowa wajen zikiri a kebance ba idan ya kasance ya azamci barin sallar ba a kayyadadden lokaci sannan ya nufi komowa kuma ya zuwa wannan ma'anar ne shaik Hassan najafi mawallafin littafin jawahirul ya ke cewa: (sannan abin da a ka smau yakini kansa daga nassi da fatawar saukakawa cikin komowa wajen zikiri, amma idan ya dau azamar barinsa ko da kuwa wani aiki bai afku daga gare shi ba bai halasta ya komo ba, takaituwa cikin haramcin gurbata kan gwargwadon abin da kai yakini a kansa, bari dai abin da ya fi zama taka tsantsan da ihtiyadi gare shi shi ne hakan idan lokacin kokwanto ya wuce cikin dawowa da rashin dawowar bayan zikiri. Wannan magana cigabanta zai zo nan gaba insha Allah ta'ala

 

Tura tambaya