lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wahabiyanci tsakanin guduma da uwar makera

Dukkanin godiya tabbata ga Allah mai shiryarwa zuwa gaskiya da daidai, tsira vda aminci su tabbata ga mafi darajar halittunsa muhammadu da iyalansa

Ya ubangiji ka bude bakina da shiriya ka kimsa mini tsoranka:

Bayan haka:

Hakika ubangiji madaukaki na cewa cikin littafinsa mai cike da hikima: 

 (أَفَمَن يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لاَّ يَهِدِّيَ إِلاَّ أَن يُهْدَى فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ)

Shin wanda ke shiryarwa zuwa gaskiya shi yafi cancanta da yiwa biyayya ko kuma wanda bai shiryarwa sai dai shima a shiryar da shi.[1]

a wani wajen kuma yace:

 (فَبَشِّرْ عِبَادِ * الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ)

ka yi bushara ga bayina wadanda suke sauraron zance su bi mafi kyawunsa.[2]

 

  lallai daga cikin ladubban muslunci kamar yadda ubangiji ya

ladabtar damu shi ne cewa mu tsaya mu saurari maganar wasunmu musammam a lokacin muhawara, idan ya zamanto muna da sabani suna sukanmu da harkan akidunmu da tabbatattun abubuwa a wurinmu sai mu kishiyance su cikin nutsuwa mu kare akidarmu ta hanyar kafa hujjoji da dalilai karfafa masu yanke uzuri saboda abin da muka koyo daga ladabin muslunci kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:

 
: (قُلْ هَاتُواْ بُرْهَانَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ)

Ka ce ku zo da dalilanku idan kun kasance masu gaskiya.

Lallai ma'abocin gaskiya ya zama dole ya zamanto a bayansa akwai lafiyayyen furuci da dataccen zance da hujja ta gaskiya mabayyaniya, bai girgiza a gaban karya ba ta bashi tsoro matukar dai yana kan gaskiya yana kan hanyar gaskiya  yana tare da gaskiya gaba da baya zahirinsaa da badininsa, a ilimance da aikace, a akidance da kuma cikin sulukinsa.

Cikin wannan dan takiataccen littafin za mu bijiro da tattaunawa ta ilimi da lafiyayyen nakadi kan muhimman akidun wahabiyawa a wannan zamani, hakan zai kasance ne cikin tsarin tambaya da bada amsa, Allah shi ne mai shiryarwa zuwa daidai.

Tambaya: wanne suka ne mai gamewa da ya hau kan wahabiyanci. 

 

Amsa: babu shakka ko kokwanto kan cewa kungiyar wahabiyanci ta wannan zamani ta na komawa cikin farkon al'amarinta da kasantuwarta da assasata zuwa ga shaik muhammad ibn abdul-wahab wanda aka haifa a shekara ta 1115 a cikin garin uyaina ya kuma mutu a shekara ta 1206 a garin najad hijaz, mabiyansa sun shahara da amsa sunan wabiyawa sun samu wannan suna daga sunan mahaifinsa Abdul-wahab. Hakika ya kafa tushen mahangar akidunsa bisa dogaro da kuma tasirantuwa da rubuce rubucen Ahmad ibn Abdul-halim wanda aka fi sani da ibn Taimiya wanda ya rayu a karni na bakwai bayan hijra wanda aka haifa a garin Harran a shekara 661 ya yi wafati a garin damashk shekara 728. bugu da kari ya kuma tasirantu da mahangar almajirin ibn taimiya wato ibn kayyum aljauzi wadanda dukkaninsu suna daga sanannu shehunan mazhabar hanbaliya masu kuma tsatstsauran ra'ayi babu banbanci cikin fikihu ne ko kuma a cikin akidoji, lallai su biyun tare da mabiyansu suna sassabawa da ragowar musulmai fiye da sabaninsu da ahlus-sunna wal'jama'a ko shi'a ko sufaye kai su sun saba da dukkanin `dan sunna da `dan shi'a kai hatta hanbalawa suna da sabani da su musammam magabata daga garesu.

Sun kudurce da shirkantar da dukkanin wadanda suke ziyartar kaburbura ko kuma masu kamun kafa da salihan bayi ko neman tabarrukinsu da dai makamantan haka daga akidun wuce gona da iri wadanda suka karkace daga hanya da daidai da hankaltuwa da ruhin  muslunci mai girma na asali, sun cusa bidi'o'I da da bata cikin musluncin asali, sun takaitar da muslunci a iya kawukansu sun kafirta ragowar musulmi, sunyi amfani da sunan tauhidi tsantsa don nuna kiyayya da cutarwa irin ta zamanin jahiliya gabanin bayyanar mujslunci, sun bata sunan muslunci wannan addini mai kima da ya zo ga dukkanin mutane, amma sakamakon jahilcinsu da ta'addancinsu sun girgiza tsarin zamantakewar musulmi, sun karkata zuwa ga soye-soye zukatansu da jahilcinsu ga hakikanin asalin muslunci madidaici wanda bai karkace daga gaskiya ba, cikin tsarin yadda suke tafiya a aikace wajen kafirta dukkanin musulmi wanda basu ba da kuma kai musu hare hare ba kakkautawa kai suna mu'amala da musulmi da wani yanayi da kai kace an shafe addinin annabi muhammadu (s.a.w) kamar yadda aka shafe ragowar addinai an kawo musu sabon addini da jagoranci shaik muhammadu ibn abdul-wahab, kamar yadda hakan yake bayyana daga littafinsa mai suna (tauhid) lallai shi kadai da mabiyansa sune ma'abota tauhidi da dayanta Allah tsantsa, da tsantsar muslunci da tsantsar tauhidi, amma ragowar musulmai wadanda ba su ba dukkaninsu sun jarrabtu da shirka mafi girma.

Wannan kenan a takaice sannan dukkanin wanda zai soki ra'ayoyinsu da akidunsu na bata masu batarwa lallai shi zai soke su ne wani lokaci ta fuskar gamewa a wani lokacin kuma a kebance, sai ya shiga bayanin yankoki da daidaikun akidun su daya bayan daya don rusasu da dalilai masu yanke uzuri da rusa karya, ya bayyana karyarsu da wofintarsu daga gaskiya da hakika da lafiyayyen hankali da nakali daga littafin Allah mai girma da sunnar annabi (s.a.w)

Manufar rubutan wannan `dan karamin littafi shi ne gangaro da suka na baki daya gamamme kan mafi bayyanar da mafi muhimmancin akidun karkata da bata a wurin wahabiyawa, da sannu zamu tabbatar cewa akidunsu sun kafu kan bakin wawakeken rami, da sannu wannan akida zata gushe da zinin Allah matsarkaki ko da kuwa sarakunan zalunci da shugabanni dagutai suna tallafa musu da kudi da takubba da makamai…. ashe asuba bata kusa.

 



[1] Yunus:35

[2] Zumar:17-18

Tura tambaya