lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

lokacin tsanani da kuntatawa

Kan asasin kassama daurori guda hudu na imamanci bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) wanda muka yi bayaninsa cikin wani yanki daga rayuwar Sarkin Muminai Husaini (a.s) hakika rayuwar Imam Sajjad ta kasance cikin daura ta hudu, ma'ana:

*daura rashin fatan samun nasara daga motsin masu dauke da makamai.

*fafutika da kaikawo mai dogon zango da iyalan gidan Annabi suka yi don samar da hukumar muslunci..

*shiri da tanadi domin cimma wannan hadafi ta hanyar bada tarbiya da zabar hanyar d ata dace domin karfafa mutane.

*bayyanar da fikirar muslunci ta asali da tona asiri da bayyanar da bidi'o'I da karkata.  bayanin cewa musibar Ashura da ta kasance cikin gajeran lokaci ta cutar da harkar shi'anci, yaduwar labarin wannan musiba cikin fadin kasashen musulmi musammam ma Iraki da Hijaz ya haifar matsanancin tsoro da razani cikin zaurukan shi'a, domin sallamammen lamari ne cewa Yazidu ya shirya tsaf domin kashe `dan Manzon Allah (s.a.w) da yake da shahara da girma da tsarkaka wurin dukkanin musulmai, kuma shirye yake da kame matayen da `yayansa domin karfafa turakun hukumarsa kan wannan kazamin kuduri nasa shirye yake da ya aikata duk wani mugunyar laifi.

Wannan razani da matsanancin tsoro yayi tasiri matuka cikin Kufa da Madina, tareda faruwar waki'ar Harra da ta kasance a watan Zul hijja hijira nada shekara 63 wacce sojojin Yazidu suka afkawa mutanen Madina suka yi musu kisan gilla  na rashin tausayi, hakika wadannan waki'o'I sun haifar da tsanani da matsi a yankunan da Iyalan Annbata suke da fada aji  musamnmam ma Madina da Kufa, Yazidu ya samu iko da hukuma a wadannan garuruwa dama kan `yan shi'a wadanda ake kidaya su Makiyan Banu Umayya na sahun farko, `yan shi'a sun fada cikin sanyin jiki da rauni sun gaza dawo da hadin kansu da kungiyarsu komai ya raunana, Imam Sajjad (a.s) cikin ishara kan wannan yanayi mara dadi yana cewa: ciki da wajen garin Madina an gaza samun mutane ashirin da suke sonmu da kaunarmu.

Shahararren malamin Tarihi Mas'udi yayi bayani karara cewa Aliyu Ibn Husaini (a.s) yayi Imamancinsa a boye cikin takiyya a cikin matsanancin zamaninsa da ya rayu ciki.

Imam Sadik (a.s) cikin tsoro a wannan yanayi  mai daci da yake cike da bakin ciki yace: mutane bayan shahadar Husaini Ibn Ali (a.s) duk sun watse sun guji iyalan Annabi in banda mutum uku:sune: Abu Kalid Kabili, Yahaya Ibn Ummu Dawil, Jubairu Ibn Mad'am, daga baya wasu mutane suka shiga sawunsu adadinsu ya karu. 

Tura tambaya