Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Kin cigaba da kiran sallah da Bilal Habashi yayi
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kin cigaba da kiran sallah da Bilal Habashi yayi

 

Bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) Bilal Y daina kiran sallah, yace: ba zan yiwa kowa kiran sallah ba bayan Manzon Allah (s.a.w).

Wata rana Fatima (as) tace: ina sha'awar jin sautin wani mai kiran sallah da ya daina yi, yayin da labari ya isa kunnen Bilal sai ya tashi ya rangada kiran Sallah yace: Allahu Akbar, Allahu Akbar.

Sai Fatima(as)  ta tuna da lokacin mahaifinta Manzon Allah (s.a.w) sai ta kasa jurewa ta fashe da kuka yayinda Bilal ya kai ga fadin Ashhadu Anna Muhammadar Rasulillah.

Sai Fatima (as) ta fara shashshaka da kuka ta fadi kan fuskarta ta suma har ta kai ga wasu sun fara zaton cewa ta bar duniya sai suka cewa da Bilal: ya Bilal! Kada ka cigaba da yin kiran sallar hakikar `yar Manzon Allah da ti wafati

Sai Bilal ya yanke kiran sallar, yayin da ta farfado sai tace: ya Bilal kammala kiran sallar.

Sai ya amsa mata da fadin cewa ya shugabar matayen duk duniya! Ina tsoran miki halin da zaki samu kanki ciki idan kin jin sautin kiran sallar.

Sai Fatima (as) ta zobaitar da shi daga wannan rana bai kara yin kiran sallah ba..


Tura tambaya