lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Manzon Allah (s.a.w) malami ne kuma mai ceto ne

 

Allah madaukaki yana cewa:

 (( ومبشرا برسول ياتي من بعدي اسمه احمد ))

Kuma mai bushara da wani manzo da zai zo daga bayansa sunansa Ahmad.

Mene ne yake iyakance mana girman da mutum yake da shi? Wannan wata tambaya da ya zama tilas a bijiro da ita lokacin da muke mu san rayuwar manyan mutane, musammam ma lokacin da muke kokarin kwankwada daga tafkin girmamar ubangijin wato shugaban annabawa da manzanni Muhammad (s.a.w).

Amasarmu sai mu ce: shi girmama wata daura ce ta ubangiji kuma kyauta daga gareshi zuwa ga mutum, kufai mai kyawu cikin matafiyar canjuwar samuwa ga rayuwa shine tubali na farko kuma na karshe kan daidaita, kuma kan haskensa ne ake iyakance alamomin girmamar mutum,girmama wani wajibi dake wuyan baki dayan mutane cikin iyakance matsaya mai kyawu daga soyayya da kauna da tsarkakuwa da karrama, da kuma tsayuwa cikin dukkanin girmama gaban dukkanin abinda ya danganta da wannan mutum, hatta manzon Allah (s.a.w) ya zo ne domin sauke mafi nauyin sakon sama, hakika yayi gwagwarmaya cikin sauke sakonsa da farko ya fara da rusa tarkacen tunanunnukan jahiliya  wanda al’umma suka tarbiyantu kansu gabanin zuwansa, bugu da kari ya ayyana sabuwar hanya ga mutane domin  domin su rayu karkashin inuwar dokoki da jagoranci, ya sauya musu miyagun akidun jahiliya da tsaftatattun akidoji ma’abota haskaka, ya kuma dora su kan mabayyaniyar hanya karkashin tsarin ubangiji wanda ya tattaro dukkanin kimomi da ma’anonin alheri, akon manzon Allah (s.a.w) bai takaita iya wata ayyananniya al’umma ba haka ma sakonsa bai iyakanta da wani bigire ko wani zamani ba, bai takaitu da iya yakar gaba a kiyayya daidaiku ba, bari dais shi ya zo ne domin tunbuke jijyoyin barna dag aba kasa da kuma yakar dukkanin azzalumai domin adalci da daidaito ya yadu da gamewar rahama ga dukkanin talikai

 ( وما ارسلناك الا كافة للناس )

Bamu aikoka face ga dukkanin mutane.

 (وما ارسناك الا رحمة للعالمين )

bamu aiko k aba face rahama ga dukkanin talikai.

Na’am manzon rahama ya kutsa fagen daga domin ya karya sasaran jahiliya, ya tarwatsa rundunarsu ya rusa gininsu ya karya karfinsu, cikin yardarm Allah hakan ya tabbatu gareshi ya samu nasara budi ya tabbatu a hannunsa ya tseratar da mutane daga wutar halaka.

 ( وكنتم على شفا حفرة من النار فانقذكم منها )

kuma kun kasance baki ramin wuta sai ceceku daga gareta.

Manzon Allah (s.a.w) ya samu ikon kafa daular muslunci kan Kalmar tauhid da iklasi da tsarkake kasa daga kumbar shirka da kafirci, kamar yanda ya tsarkake zukata da ilimi domin su daukaka cikin duniya zuwa tsarki da kamala, da bauta da iklasi ga Allah makadaici madaukaki.

Tsarki ya tabbata gareka ranar da Allah ya haskaka duniya da haihuwarka, aminci gareka ranar da Allah zai haskaka lahira da cetonka

Tura tambaya