lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

BAHASUL KARIJUL FIKHU 19 RABIUS SANI 1441 H, JERANTAWA TSAKANIN FATIHA DA SURA DA TSAKANKANIN KALMOMINSU DA HARUFFANSU 47

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami-tareda Ustaz Assayid Adil-Alawi (H) karfe 8 na safe.

Mas'ala 36: wajibi ne a kiyaye jerantawa tsakankanin ayoyin Fatiha da Sura da tsakankanin ayoyinta da haruffansu haka zalika kiyaye rashin jinkirtawa, da zai wofinta da wani abu daga haka da gangan to sallarsa ta baci.

Abubuwan da suka rataya kan (tartib da muwalat) jerantawa da rashin jinkiri:

Ina cewa: daga cikin mas'alolin da rassansu akwai karatun cikin sallah lallai wajibi cikinsa a kiyaye jerantawa cikin kira'a sannan wannan mas'ala tana da fuskoki: fuska ta farko: jerantawa tsakankanin ayoyin Fatiha da na sura.

Fuska ta biyu: jerantawa tsakankanin kalmomin Fatiha da sura, fuska ta uku: jeranta haruffan kalmomi cikin Fatiha da sura, fuska ta hudu: wajabcin kauracewa jinkiri tsakanin Fatiha da sura da tsakankanin kalmomi da haruffa.

Wannan shi ne abinda mwallafin Allah ya tsarkake sirrinsa ya tafi kansa kuma shi ne abinda ya fi shara shahra mai girma, amma jerantawa tsakanin ayoyi Fatiha da ayoyin sura, babu shakku wannan shi ne zahiri abinda ya bayyana cikinsa, kamar yanda jama'a daga malamai sun bayyana hakan karara ba tareda an sabani ko gangarar ishkali ba, a wannan lokaci da zai fara gabatar da karanta sura kan Fatiha tareda cewa ya san ana faraway ne da Fatiha yayi hakan ne cikin gangan to sallarsa ta baci, sun kafa hujja kan haka da wasu fuskoki, fuska ta farko: Siratu mutasharri'a Kahkara'iyya, bari dai Sirar dukkanin musulmi, bari dai Siratul Ma'asumin amincin Allah ya kara tabbata a garesu, sannanen lamari daga garesu tun zamanin farko har zuwa na baya shi ne kiyaye jerantawa tsakanin Fatiha da sura.

Sai dai kuma anyi nakadi da ishkali kansa: hakika aikin Ma'asumai ba daidai yake da zancensu ba da har zai zamana ya shiryar kan wajabci, kamar yanda Sira tana bayyana Asalin halasci bawai wajabci ba, na'am hakika rikonsu da dawwamarsu kan aiki yana shiryarwa zuwa ga fifikonsu da mustahabbanci a ba'arin wasu wurare bawai wajabci ba, sau da yawa zaka samu sun himmatu kan aikin mustahabbi kamar yanda suke himmatuwa kan wajibai, ka lura.

Fuska ta biyu: riko da gayya daga riwayoyi daga cikinsu: Sahihatu Hammad (Wasa'il: babi 1 daga babukan Af'alul salat hadisi na farko) da gabatar da Fatiha kan sura da farko bisa hadowar fadinsa amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin karshen hadisin: (ya Hammad haka zaka yi sallah) zahirin abinda za a iya fahimta daga wannan kalma shi ne wajabci, daga cikinsu akwai: Muwassakatu Samma'atu:

موثقة سماعة قال: (سألته عن الرّجل يقوم في الصلاة فينسى فاتحة الكتاب ـ إلى أن قال ـ فليقرأها ما دام لم يركع فإنّه لا قراءة حتى يبدأ بها في جهر أو إخفات .

Ya ce: na tambaye shi dangane da mutumin da ya manta Fatiha a cikin sallah –har zuwa wajen ya ce: ya karanta Fatiha matukar dai bai durkusa ruku'u ba, lallai yand alamarin yake babu karatu har sai ya fara da Fatiha cikin sallolin da ake bayyanar da karatu da boyewa.  Wasa'il babi 1 daga babukan kira'a cikin sallah hadisi na biyu.

Daga cikinsu: Kabaru Fadalu Ibn Shazan ya tattaro bayani karara kan faraway da Fatiha da dai wannan masadari da ya gabata a hadisi na uku, idan anyi ishkali da cewa isnadinsa yana da rauni sakamakon raunin da hanyar Saduk zuwa ga Fadalu, babu matsala cikin haka bayan rauninsa ya rigaya ya gyaru da aikin malamai, ko kuma ya kasance ya karfafa Sahihatu Hammad da Muwassakatu Samma'atu.

Fuska ta uku: mafhumin jerantawa cikin mafhumin kira'a da aka ambata yana daga abubuwa da ya doru kansu, faucewa da faduwarsa yana lazimta faucewarta da faduwarta, sai ya lazimta gurbata da bacin sallah sakamakon barin yanki daga yankunan sallah cikin halin sani da kuma ganganci.

Amma jerantawa tsakanin ayoyi da kalmomi haka haruffa, da farko wannan babu matsala cikinsa babu sabani sakamakon tsayuwar ijma'i da dukkanin kashe-kashensa, hali na biyu: abinda ake fa'idantuwa da shi aka ciro bari dai nassi daga nassoshin da hadisai na wannan babi, na uku: lallai mafhumin Fatiha da Sura kadai dai yana tsayuwa da wadancan ayoyi da kalmomi da haruffa kan kebantaccen tsari da jerantawa da aka ambata tsakankaninsu da abinda ake d ahsi daga yankunanta, da yanayin da da zai wofinta da su yana sane kuma bisa ganganci lallai zai haifar da rashin tabbatuwar Fatiha a ingantacciya, sai ya haifar da baci da gurbatar ta, kamar yanda hakan yake a bayyane.

Lallai hakan yana daga mudlakin wofinta cikin ayoyi da kalmomi ko kuma haruffa da sunan Fatiha ko Sura bai gasgatuwa tareda shi, sai ya zama abinda aka umarci a zo da shi bai tabbatu ba, sai ya haifar da gurbata da bacin sallah, idan ya maimaita sai ya maimaita ta tareda kiyaye jerantawa, lallai shi bai nesanta a kira shi da gurbata ba hakan ya faru sakamakon kari da ya haifar cikin sallah da gangan wanda yake jawo gurbatar sallahm sabida yana daga larura juzu'iyya na tabbatuwa da wannan karatu na farko da yayi gurbatcce, sai dai idan yayi niyyar karanta Kur'ani mudlakan bawai tareda nufin juzu'iyya, zahiri babu laifi cikin hakan sakamakon rashin kasancewarsa kari mai cutarwa.

Amma kiyaye muwalati (rashin jinkiri) tsakankanin surorin biyu da tsakankanin ayoyinsu da kalmominsu da haruffansu, wannan shi ne abinda Shaik Dusi yayi bayayanan shi karara haka zalika manya malamai biyu masau daraja Allama da Muhakkik da Shahid Awwal da Shahidus Sani, da Muhakkikul Karaki da wasunsu, barrio dai cikin littafin Jawahir( ni ban samu sabani cikinsa ba tsakankanin jiga-jigan malamai daga wadanda suka zo daga baya) sun kafa hujja kan haka da fuskoki: ta farko koyi da Annabi (s.a.w) da iyalansa (a.s), ta biyu: Sirar musulmai daga Sahabbai da Tabi'ai, ta uku: Sira mutasharri'a da ta hade da zamanin Ma'asumai (a.s) ta hudu: kasancewarsa ibada ba yarda ayi shi da wata sura in ba wacce shari'a ta bayyana ba, ta biyar: karkatar idlaki kira'a ya zuwa iya fuskokin muwalat.

Wadannan fuskoki zasu iya karbar munakasha da ishkali kamar yanda ya gabata, sai dia cewa kuma wasu daga manyan malamai na wannan zamani sun kafa hujja tsayuwar mafhumin kalma ko aya da nuwalati, hakan ya kasance daga fuskar la'akari wahdatul ittisaliya urfiya tsakaknanin juzu'ai, da yanayin da zai wofinta da ita ko yayi dogon shiru da makamancinsa daga abubuwa da suke rusa surar kira'a da karatu da hai'ar magana da kalma ko aya ta fito daga hakikaninta a al'adance, alal misali da zai ce (ma) sai bayan wani lokaci ya (li) daga can ya ce: (ki) to al'adance ba a kiransa da ya karanta (maliki)bari dai za kirga shi daga kuskure ya kuma fita daga larabci.

Haka halin yake cikin wanda ya karanta (maliki) sai bayan dogon lokaci sai ya karanta (yaumi) can sai y ace( dini) wannan bai kasancewa misdakin aya mai albarka (maliki yaumi dini) lallai ya fita daga dokokin muhawara a harshen larabci, haka lamarin yake tsakankanin ayoyi ba'arinsu tareda ba'ari, lallai gasgatuwar sunan sura ko aya ya dogara kan kiyaye muwalati rashin jinkiri.

Sannnan daga cikin bayyananne lamari sananne abinda ake bukata cikin karatun sallah shi ne karatun kur'ani kan tsarin ingantaccen larabci, wannan lamari yana gudana cikin dukkanin hai'a ittilasiya urfiya kamar yanda yake cikin kulli da muwalati tsakanin cikin kullawa da tabbatarwa, ko kuma cikin kiran sallah da ikama kamar yanda ya gabata dogon shiru ko kuma shiga da bakon lafazi tsakanin ayoyi da kalmomi ko haruffa yana daga abinda yake rusa hai'ar zancen da take hade a al'adance da luggance, lallai yana daga abinda yake rusa ingancin sallah sannan wajibi a kiyaye muwalati urfiya, zahirin dalilan wajabcin karanta Kur'ani kan tsarin ingantaccen larabci

 (أنزلناه قرآنا عربياً)

Mun saukar da shi yana abin karantawa na harshen larabci.

Wajibi ne a kiyaye dukkanin abinda ya shafi kira'a ingnatacciya cikin Kur'ani mai girma hatta abinda ya shafi wasali da li'irabi da bina'I da sukuni da sauransu daga abubuwa da suke da alaka da ingantacciyar kira'ar larabci.

Sai dai kuma zahirin abinda ya zo daga manyan malamai daga cikinsu mawallafin Allah ya tsarkake sirrinsa hakika yayi idlakin wajabcin kiyaye muwalati cikin kir'a , amma zahiri kadai dai muwalati yana wajaba cikin halin da idan aka wofinta daga gareshi ingantacciyar kira'ar larabci zata rushe amma fiye da haka dalili bai tsayu kansa ba a zahiri, ka lura, abinda yake lazim daga muwalati shi ne iya abinda ake la'akari da shi cikin ingancin maganar larabci, kamar idan ya kasance kabar ko insha'I ba tareda yin dogo shiru ba kamar misalin wanda yake cewa: Zaidu sai bayan dogon lokaci ya ce yana tsaye, wannan yana da istimali na kuskure baya inganta a luggance da al'adance , ko kuma a furta wani lafazi bako tsakanin mubtada'u da kabar , ko tsakanin fi'ili da muta'allikatihi, ko tsakanin siffa da mausuf, ko shardu da ajza'ihi, ko mudaf da mudafun ilaihi da dai makamancin haka daga abubuwa da suke fita daga kasantuwarsu ingantacciar magana a larabci, bari dai ana kirga hakan daga kuskure cikin ilmul lugga.

Amma rata da ake samu daga abinda ya zo daga umarni da yin addu'a da rokon rahama da neman tsari daga azaba cikin ayoyinsu, ko kuma amsa sallama, ko kuma yin hamdala yayin yin atsihawa baye cin karo da muwalati, kamar yanda babu idlaki ga dalilinsu da har zai hado da wannan muhalli da wuri, kamar yand aya fita daga ciki da dalili.

Sannan ya doru kan sharadin muwalati da cewa da zai wofinta daga kiyaye muwalati yana sane cikin ganganci lallai hakan zai jawo bacin sallah, da farko dai lallai idan sharadi ya wofinta to abinda aka yi sharadi kansa shima zai wofinta, ta biyu: da zai wofinta da wani abu daga haka da gangan sallarsa y abaci kamar yanda ya zo daga littafin Annihayatul Ahkam da Zikra da Bayan da Alfiya da Jami'ul Makasid da Arraudu da wasunsu,

Zamu cigaba da yardar ubangiji.

 

 


Tura tambaya